SHEIKH ABDULJABBAR YA AIKAWA GANDUJE WASIQA BAYAN DA AKA KAWO MASA TAKARDAR GAYYATARb MUQABALA.
GA FASSARAR WASIQA:
Na rubuto (wannan wasika) domin na nuna farin cikina akan matakin da mai girma gwamna ya dauka game da damar daya bani (kamar yadda na nema) saboda yin hakan zai kawo fahimta da samun daidaito mai dorewa akan wannan lamari. Musamman duba da irin yadda dukkan bangarorin akayi adalci wajen basu dama iri daya yayin gudanar da wannan muqabala.
Inaso inyi amfani da wannan dama in sanar da mai girma gwamna cewa; Mummunan abu ne a gurina taba janabin Annabi s.a.w.a. da Sahabban sa managarta, inaso in sanar da mai girma gwamna ban taba kuma bazan taba raina janabin Annabi s.a.w.a. ko daya daga Sahabban sa managarta ba.
Duk wa'azina, hudubobina ko rubutuna ina yinsu ne da manufar kare kima da mutuncin Annabi s.a.w.a. da Iyalan gidanSa da Sahabban sa managarta. A yunkurina na aiwatar da hakan (a aikace) a shekarar 2015 na tafi har kasar Egypt domin yin muqabala da wani makiyin Musulunci (oriantelist) wanda yake amfani da wasu Hadisai da aka jinganawa Annabi s.a.w.a. da suka zo a mafiya yawan littattafan Hadisi, wajen kai hari ga janabin Annabi Muhammadu s.a.w.a. akan tashar Alhayat, a sakamakon haka mutane da dama musamman a kasashen larabawa sun fita daga musulunci (ridda). Saboda wasu dalilai da mutumin da na ambata ya sansu shi kadai yaki yarda yayi wannan zama dani.
Duba da wannan, na karbi wannan gayyata zan halarci wannan muqabala da budaddiyar kwakwalwa, suma ina fata daya bangaren (yan maja) zasu halarci wannan zama da budaddiyar kwakwalwa.
Yayin da nake godewa mai girma gwamna daya bani dama in taho da littattafaina don tabbatar da sahihanci, inganci da gaskiyar fahimta ta, ina roko da a amince na taho da mutanen da zasu kulamin da littattafai na, Video da Audio da za'a dauka yayin wannan zama.
ALLAH YA JA ZAMANIN JIHAR KANO
ALLAH YA JA ZAMANIN TARAYYAR NAJERIYA.
Muhammadul Hadi
28/02/21.