@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
MAGANA KAN AMBATON ZUWANSA (A. F)
Duniyar muslimci wacce ta tattara dukkan wata fahinta ta jama'ar musulmi sun yarda da cewa Annabi (S. A. W. W) yayi magana kan cewa kafin tashin alqiyama za a sami wani mutum mai suna Mahdi wanda zai cika duniya da adalci da daidaito.
Sabanin da aka samu kawai shine, shin, wannan Mahdin daga ina zai fito kuma daga wacce zuriyar ?
Sai kuma batun shin, an haife shi ne ko kuma ba a haife shi ba? Akan hakane kawai aka sami sabani . Amma cikin rubutunmu na yau munyi nufi ne kawai mu kawo magana kan tabbacin cewa Manzon Allah (S. A. W. W) yayi magana game da zuwansa (A. F).
Hafiz Abu Abdullah Muhammad Bn Majah Al-Qazawiniy ya fitar cikin wani hadisi mai tsaho cikin saukowar Isah Ibn Maryama (A. S), daga baban Umamata Al-Bahiliy (R. A) yace, " Manzon Allah (S. A. W. W) yayi mana Khudba sai ya ambato Dujal, ya fada a cikinsa;
" LALLE MADINAH ZA TA KORI RAGONTA (🐑) KAMAR YADDA MUTANEN MAKKAH SUKA KORI MAFI ALKHAIRIN RAGONTA. ZA A KIRA WANNAN RANA DA RANAR KHULAAS ."
Sai Ummus-Shuraik 'yar baban Askari tace, " To, ina larabawa suke a wannan lokaci ?" Yace;
" SU A WANNAN LOKACI 'YAN KADAN NE, SUN TARU A BAITUL-MAQDIS TARE DA LIMAMINSU MAHDI LOKACIN YA WUCE ZAI JA SU SALLAR ASUBAHI, A YAYIN ISAH 'DAN MARYAMA ZAI SAUKO. SAI LIMAMIN NASU (Mahdi) YA JAWO DA BAYA-BAYA YANA SUNKUYAR DA KAI (don girmamawa) GA ISAH DON YA YIWA MUTANE SALLAH. SAI ISAH (A. S) YA 'DORA HANNUNSA A TSAKANIN KAFADUNSA (Mahdi) YA CE MASA, " KA WUCE ."
(Nurul-Absar fee manaaqibul Ahlul-Bait, shafi na 276)
Wannan hadisi ya zo daidai da wannan hadisi na Bukhairi da ke cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
(3449)- حدثنا ابن بكير: حدثنا الليث، عن يونس، عن ابن شهاب، عن نافع مولى أبي قتادة الأنصاري: أن أبا هريرة قال:
قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: (كييف أنتم إذا نزل ابن مريم فيكم، وإمامكم منكم)
Ibn Bukhair ya bamu labari, Laithee ya bamu labari daga Yunus, daga Ibn Shihaab, daga Nafi'i 'yantaccen bawan baban Qatadata Al-Ansariy, cewa Abu Hurairata yace, Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" YA ZA KU KASANCE NE A YAYIN DA ISAH IBN MARYAMA YA SAUKO KUMA LIMAMINKU (Mahdi) NA CIKINKU ?"
(Bukhari, Kitabun Ahadithil-Anbiya'i, babin saukowar Isah Ib Maryama, hadisi mai lamba 3449).
Wannan na nuna mana ne cewa ashe wannan limami wanda Isah (A. S) zai riske shi yayin da ya sauko shine Mahdi.
Kuma ya zo cikin Tafsirin Suyudi (Durrul-Mansur) cewa,
وأخرج عبد بن حميد وابن جرير، عن الحسن رضي الله عنه {وإنه لعلم للساعة} قال: آية للساعة خروج عيسى ابن
Abdu Bn Humaid da Ibn Juraij sun fitar daga Hassan (R. A) " " LALLE SHI (bayyanarsa/dawowarsa) ALAMA CE TA TASHIN ALQIYAMA. " Yace:
" Alamar tashin alqiyama shine fitowar Isah. "
(Durrul-Mansur)
Sannan kuma cigaban wannan magana ce inda Annabi (S. A. W. W) ke cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
وعن أمِّ المؤمِنينَ أمِّ عبدِ اللهِ عائشةَ رضي الله عنها قالت:
قالَ رسول الله صلى الله عليه وسلم: (يغْزُو جَيْشٌ الْكَعْبَةَ فإِذَا كَانُوا بِبَيْدَاءَ مِنَ الأَرضِ يُخْسَفُ بِأَوَّلِهِمْ وآخِرِهِمْ). قَالَتْ: قلتُ: يَا رَسُولَ اللهِ، كَيْفَ يُخْسَفُ بأوَّلِهِمْ وَآخِرِهِمْ وَفِيهمْ أسْوَاقُهُمْ(1)، وَمَنْ لَيْسَ مِنْهُمْ ؟! قَالَ: (يُخْسَفُ بِأَوَّلِهِمْ وَآخِرِهِمْ ثُمَّ يُبْعَثُونَ عَلَى نِيّاتِهمْ) مُتَّفَقٌ عَلَيهِ. هذَا لَفْظُ الْبُخَارِيِّ .
Daga uwar muminai uwar Abdullahi A'ishata (R. A) tace;
Manzon Allah (S. A. W. W) yace,
" WATA RUNDUNA ZA TA YAQI KA'ABA, AMMA IDAN SUKA KASANCE A WANI GURI (da ake kira) BAIDA'A ZA A SHAFE TUN DAGA NA FARKONSU ZUWA NA QARSHENSU. " Tace, sai nace;
" Yaa Ma'aikin Allah ! Ta yaya za a shafe tun daga na farkonsu har na qarshensu alhali cikinsu akwai 'yan kasuwarsu dama wanda ba ya daga cikinsu (harya ce kawai ta hada su) ? Yace;
" ZA A SHAFE TUN DAGA NA FARKONSU HAR ZUWA NA QARSHENSU, SANNAN A TASHE SU (kowa) BISA NIYYARSA ."
1 - باب الإخلاص وإحضار النية
حديث رقم :2
(Riyadus-Saliheen, Kitabul-Ma'amurat Babun Ikhlaas wa ihdhaarun-Niyyati, hadisi mai 2)
Tarihi ya tabbatar da cewa wannan al'amari bai auku ba, sai lokacin da Imam Mahdi (A. F) ya bayyana wasu za su fito da niyyar yaqarsa, sai wannan waqi'a ta auku a kansu.
ZA MU CIGABA INSHA ALLAH.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
20th March, 2021/ 7th Sha'aban, 1442.