QALUBALEN DA SHEIKH TIJJANI BAUCHI KE YIWA 'YAN SHI'AH
Gaskiya wannan magana ta Sheikh Tijjani Bauchi abin dubawa ce kuma abin nazari ga wanda ke ganin abinda 'yan Shi'ah keyi da sunan juyayin kisan Imam Hussaini (A. S).
Da gaske Umar Bn Khaddab kashe shi akayi kuma kisa na zalunci, domin wani Bamaguje ne ya same shi yana kan jan sallah ya kafa masa Mashi wanda yayi sanadin kisansa.
Ba ma Umar Bn Khaddabi kadai ba, har Imam Ali (A. S) ma irin wannan kisa akayi masa, domin Ibn Muljam (L. A) ne ya same shi yana jan sallar asuba ya sare shi da Takobi mai guba a tsakar kansa.
To, ganin irin wannan kisan ta'addanci da aka yiwa Umar da Imam Ali (A. S) yasa wannan Shehin ke gani su suka fi cancanta a fito ana juyayin kisan da akayi musu matuqar abinda 'yan Shi'ah keyi addini ne kuma don Allah suke yi, har yake cewa su a aqidarsu ta Ahlus-Sunnah Umar yafi Hussaini daraja.
Ko da shike Imam Ali (A. S) ana juyayin wannan kisan gilla da akayi masa, amma dai juyayin bai kai kamar yadda ake yin na Imam Hussaini (A. S) ba.
'Yar qanqanuwar hujjar da za mu bawa wannan Shehin dama wadanda ke ganin maganarsa hujja ce ta qalubantar Shi'ah za mu iya kawo masa hujja cikin nassosi kamar haka :-
Cikin Alqur'ani Allah (T) na cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
Yayin da Allah (T) ke bawa Annabi (S. A. W. W) labarin halakarwar da ya yiwa Fir'auna da jama'arsa, sai yace masa,
" فَمَا بَكَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلسَّمَآءُ وَٱلۡأَرۡضُ وَمَا كَانُواْ مُنظَرِينَ ."( ٩٢)
" (Amma duk da haka) SAMA DA QASA BA SUYI KUKA A KANSU BA, KUMA BASU KASANCE WADANDA AKE JINKIRTAWA BA ."
(SURATUL-DUKKAN :29)
To, idan muka duba qarqashin Tafsirin wannan aya za muga wata magana kamar haka;
وأخرج ابن أبي حاتم عن عبيد المكتب، عن إبراهيم رضي الله عنه قال: ما بكت السماء منذ كانت الدنيا، إلا على اثنين.
قيل لعبيد: أليس السماء والأرض تبكي على المؤمن؟ قال: ذاك مقامه وحيث يصعد عمله.
قال: وتدري ما بكاء السماء؟ قال: لا.
قال: تحمر وتصير وردة كالدهان إن يحيى بن زكريا لما قتل، احمرت السماء وقطرت دماً.
وإن حسين بن علي يوم قتل احمرت السماء.
وأخرج ابن أبي حاتم عن زيد بن زياد رضي الله عنه قال: لما قتل الحسين، احمرت آفاق السماء أربعة أشهر.
Ibn Abiy Haateem ya fitar daga Ubaidul-Muktabi, daga Ibrahim (R. A) yace : " SAMA BATA TABA YIN KUKA BA TUN LOKACIN DATA KASANCE, SAI DAI AKAN MUTUM BIYU.
Sai aka cewa Ubaid, Ashe sama ba ta yin kuka akan mumini ? Yace, " WANCAN MUQAMINSA NE GWARGWADON YADDA AIKINSA KE HAWA. " Yace,
" KO KA SAN KUKAN SAMA ?" Yace, "A'a. " Yace,
" TANA YIN JA (red) NE, SAI JAN NATA YA SHUDE KAMAR GARURA (abinda ake yiwa Fata rini). LALLE YAYIN DA AKA KASHE YAHYA BN ZAKARIYYAH SAMA TAYI JA KUMA TA ZUBAR DA JINI . SANNAN KUMA HUSSAINI BN ALIYU YAYIN DA AKA KASHE SHI SAMA TAYI JA ! "
Ibn Abiy Haateem ya fitar daga Zaid Bn Ziyaad (R. A) yace, " YAYIN DA AKA KASHE HUSSAINI SAI DA SARARIN SAMANIYA TAYI JAA TSAHON WATANNI HUDU (4) ."
(TAFSIRU DURRUL-MANSUR NA SUYUDI)
Sannan kuma yazo cikin Tafsiri na 'Dabari kamar haka,
24072- حدثني محمد بن إسماعيل الأحمسي، قال: ثنا عبد الرحمن بن أبي حماد، عن الحكم بن ظهير، عن السدي قال: لما قتل الحسين بن علي رضوان الله عليهما بكت السماء عليه، وبكاؤها حمرتها.
Muhammad Bn Isma'il Al-Ahmasiy ya bamu labari yace, Abdurrahman Bn Abiy Hammad ya bashi labari daga Hakam Bn Zuhair, daga Saddiy yace :
" YAYIN DA AKA KASHE HUSSAINI BN ALIYU (R. A) SAMA TA YI KUKA A KANSA, KUKAN NATA KUWA SHINE YIN JANTA (redness) !"
(TAFSIRUL-'DABARIY)
Sannan kuma ya zo cikin Nurul-Absaar, daga Ummul-Fadl Bn Abbas (R. A) tace,
" Manzon Allah (S. A. W. W) ya shigo gare ni sai nace, yaa Ma'aikin Allah ! Cikin daren jiya nayi wani mummunan mafarki. Yace, " MENENE SHI ?" Nace,
" Na gani ne kamar wata tsoka daga jikinka ta yanko ta fado cikin dakina. " Sai Manzon Allah (S. A. W. W) yace,
" ALKHAIRI KIKA GANI, FADIMATU ZA A HAIFI YARO NE A 'DAKINKI. "
Sai kuwa Fadimatu ta haifi Hussaini . Tace, " Ya kasance a dakina kamar yadda Manzon Allah (S. A. W. W) ya fada, sai na shiga dashi gare shi, sai ya dora shi akan cinyarsa, sa'an nan ya miqa masa Tufa (apple) daga gare ni, sai ga idanuwan Manzon Allah (S. A. W. W) na zubar da hawaye. Sai nace, " Fansar mahaifina da mahaifiyata gare ka yaa Ma'aikin Allah, kukan me kake yi ?" Yace,
" JIBRIL (A. S) NE YAZO YA BANI LABARI CEWA, LALLE AL'UMMATA ZA TA KASHE WANNAN 'DAN NAWA ! SAI YAZO MIN DA QASA DAGA WATA JAR QASA ."
(NURUL-ABSAAR NA SHIBALANJI, SH:204)
Idan muka kalli wadannan riwayoyi uku za muga akwai kuka wanda sama tayi, kuma Manzon Allah (S. A. W. W) yayi sakamakon labarin da aka ba shi cewa za a kashe dansa Hussaini (A. S).
Saboda haka muke yin kuka na koyi dasu a kansa, kuma hakan ya zama Sunnah ga muminai masu dabbaqa aikin da Manzon Allah (S. A. W. W) ya aikata shi a aikace ba wai bada umarni ba.
TAMBAYA
Yaa Sheikh Tijjani, ko akwai wata riwaya komai rauninta (weak) wacce ke magana cewa wani abu ya faru sakamakon kashe Umar ?
Ko kuma za ka iya kawo nassi wanda ya soke wadannan riwayoyi hudu (4) ?
Na san cikin karatukanka kana cewa koda an sami aya dole sai an bi fassarar magabata wajen Fassarata ba wai wani ya fassarata da ra'ayinsa ba. To, kai kana da wata fassarar magabata wacce ta irin abinda ya auku sakamakon kisan Imam Hussaini (A. S) ya auku a kisan Umar ?
Idan kuwa babu, to, ta yaya kake danganta kisan makashin 'yar Manzon Allah (S. A. W. W) da kisan da aka yiwa dan Manzon Allah (S. A. W. W) ?
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(0813792504)
28th March, 2021/ 15th Sha'aban, 1442.