MENENE TARIHIN HIJABI KAFIN ZUWAN MUSULUNCI, SHIN SAURAN ADDINAI SUNA SANYA SHI KO A'A?
AMSA: Tabbas akwai kayan da Yahudawa, Masihawa, Larabawa, ke sanya shi domin rufe jikkunan su a matsayin HIJABI ko sitirta jikinsu da shi tun kafin zuwan MUSULUNCI, nasan wasu da yawan mutane za suyi tsammani da mata ba sa rufe jikinsu, wasu kuma za su dauka MUSULUNCI ne kawai ya zo da sanya kayan da mata suke rufe jikkunan su babu shi a sauran addinai, to lallai sauran addinai ma suna sanya kayan da yake rufe musu jikkunan su, tarihi ya tabbatar da cewa suma sauran addinai sun mahimmantar da rufe jikkunan matayensu.
*MISALI:*
1. Addinin Yahudanci matan su suna rufe jikinsu gaba daya har da fuskar su da duk wani kwalliya da zata bayyana ga wani wanda bai dace ya ga jikin su ba, in banda mijinsu ta yadda basa fitowa waje ba tare da sun rufe jikin su ba, kai wani lokaci ma idan mace ta daga muryarta ta yadda makwabcin su zaiji to mijinta zai iya sakinta, kuma ba tare da ya bata sadaki ba, saboda mahimmancin rufe jikkunan matayensu, da kuma sitirta jikin matansu.
2. Sannan idan muka koma addinin Masihanci shi ma za muga matayen su ba sa fitowa waje sai sun rufe dukkannin jikin su, wasu ma suna hana kwalliya a fuskar su ko tace kan matayen na su ko kitso ko kunshi ko sanya a warwaron hannu da duk wani kyale-kyale suna rufe shi in dai ba mazajen su ba to ba mai ganin sa, saboda mahimmatar da rufe jikin matayensu.
3. Idan kuma muka dawo IRAN shi ma za muga a wancan lokacin na baya yadda suke mahimmantar da rufe jikin matayen su kai su harma sun tsananta sosai ta yadda idan aka Aurar da mace ta daina fitowa kenan sannan dan uwanta ko Babanta ba zai zo wajantaba, bata da alaka da waje ballema wani ya ganta, Sarakunan su kuma na wancan lokacin suma idan suka Auri mace to, ta daina fita kenan sai dai iya gidan Sarki kawai ko farfajiyan gidan Sarki za ta iya fitowa, saboda suma yadda suke ba da mahimmaci akan rufe jikin matayen su, to, idan mukalura za muga yadda Hijabi yake a sauran addinai ba wani abu bane boyayye, musulunci ya sami addinai da yawa da Larabawa suna sa shi, sai dai musulunci ya nuna yadda ake sanya shi ne da kuma yadda Allah Subhanahu wata Allah yake nufi da shi, da kuma yadda za a sanya shi da kammala shi, da kuma ka'idojinsa da matsayinsa da kuma ma'anarsa ta hannun Annabin Rahama (s).
Idan mukalura za muga yadda MUSULUNCI ya zo da maganar sanya HIJABI shi na shi sauki yazo da shi ba kamar yadda sauran addinan suka tsananta da kuma ta kura matayensu wajan rufe jikinsu ba, ko ina da ina FUSKA, HANNU, KULLE A GIDA, HANA DAN UWANTA GANINTA KO BABANTA NE mutukar tai Aure,wannan ga wasu addinai kenan, amma shi MUSULUNCI yaba mace damar barin fuskarta da wuyan hannunta matukar babu wani kwalliya ko ado a su, idan da su abin da musulunci yace shi ne a rufe su kawai, ka ga kenan shi musulunci sauki ne yazo da shi ga matayen muminai, idan mukai la'akari da sauran addinan nasu yayi tsanani sosai, kamar yadda muka kawosu a baya.
*Binya Shi'a Kauran-Wali, Kudan*