NA FARKO; HIJABI a Luggan Larabci yana da ma'ana kamar guda uku.
1. LABULE
2. KATANGA
3. BANGO
NA BIYU;
Amma a ISDILAHI na Shari'a ana kiran sa da SITIR, yawanci haka litattafai na musulunci suke kiran sa, duk da yake yanzu amfi kiran sa da Hijabi, kuma shi ne ya fi shahara wajan mutanen wannan zamani daka an ce Hijabi to mutanen yanzu za su fahimci wanda muke amfani da shi ne yanzu, kuma muke kiransa da suna Hijabi.
To masha Allah, abin da ake nufi da Hijabi shi ne wani kaya wanda matan muminai suke amfani domin rufe jikkunan su da shi.
SABODA ME?
1. Domin bin ummarnin Allah Subhanahu wata Allah, da yai Ummarni da sanya Hijabi.
2. Domin rufe ado ga mace ga wanda bai dace su gani ba.
3. Domin gane Alamomin mata muminai.
4. Domin kariya ko katanga daga masu cutar da muminai mata mutane da Al-jannun su.
5. Domin kiyaye mutuncin mata muminai a takaicen takaicewa wannan shi ne kadan daka cikin abubuwan da Shari'a ta sanya wajabta sanya Hijabi.
Musammanma ga wanda ba Muharrami ba ya ga mace babu shi ba, wanda kuma wajabi ne ga mace musulma mumina ta sanya shi, domin dukkanin jikin mace al'aura ne in banda fuskanta da wuyan hannunta zuwa ya tsunta na karshen sama, shi ma da sharadin babu wani ado ko zane kai wuce nanma wajabi ne ma da duk wani abu da zai janyo hankalin namijin da ba Muharraminta ba wajibi ta kauda shi ko da kuwa fuska ne da wuyan hannunta wanda Shari'a ta ce yanzu ba matsala don an gani, amma daka lokacin da tai ado akansu yanzu ya dole ta rufe su balle kuma sassan jikinta.
Don haka ya kamata mata su kula sosai wajan ba da mahimmaci ga sanyi Hijabi, da kuma bin ka'idojin sanya shi masamman 'yan uwa Almajiran Malam Zakzaky (H) idan muka kula da yadda Malam Zakzaky yake yawan magana akansa tare da maidakin sa Malam Zeena wajan muhimmantar da sanya shi.
Sannan idan muka duba tarihin musulunci za muga yadda Sayyida Fatima (as) take muhimmantar da Hijabi a rayuwata har ta koma zuwa ga Allah!
Saboda mahimmancin da take ba Hijabi da bin ummarnin Allah Subhanahu wata Allah za mugani cikin tarihi cewa, akwai lokacin da Sayyida Fatima (as) suna tare da Annabin Rahama (s) da Ali (as) a gidanta wani Makaho ya nemi izinin shigowa gidanta, amma Sayyida Zahra (as) sai da ta sanya Hijabi FULL ta rufe dukkannin jikinta, Sai Manzon Allah yake cewa Sayyida Fatima (as) ai Makaho zài shigo me ya sa kika sanya Hijabi?
Sai Sayyida Fatima take cema Manzon Allah ai duk da yake Makaho ne ai ni ina ganin sa ko da ko shi ba ya ganina, sannan zai iya jin kamshin jikina, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ji dadi kuma yai farin cikin yake cewa lallai ke Sayyida Fatima (as) tsokace daka jikina.
In ko haka ne me zai hana mi koyi da su Sayyida Fatima (as) wajan sanya Hijabi da koyi da Sayyida Fatima ta kowane irin yanayi?
*Binya Shi'a Kauran-Wali*