@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
MALAMAN MAJA ZA SU TAYAR DA HARGITSI
Babu wata alaqa da sanin Ghaibu ko kuma wahayi wanda za ace da ita na dogara wajen kawo wannan magana ko rubutu, sai dai kawai sanin al'ada ko dabi'a irin ta kangararru masu qin gaskiya.
Duk wanda ke bibiyar tarihin kangararru mutane wadanda tarihi ya kawo mana su zai san cewa haka dabi'arsu take, duk lokacin da suka ga gaskiya sai su kangare mata ta hanyar yin bore ko kuma juya wata fassara ga wanda ke qoqarin tabbatar da gaskiya.
Idan kasan dabi'ar mutane dole ne ka yi musu hasashen cikin rayuwarsu ko kuma qarshensu. Wannan dalili yasa Annabi Nuhu (A. S) yayi addu'ar Allah ya halakar da mutanensa gaba daya wadanda suka qi karbar gaskiya. Yake cewa Allah;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
وَقَالَ نُوحٞ رَّبِّ لَا تَذَرۡ عَلَى ٱلۡأَرۡضِ مِنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ دَيَّارًا ٦٢ إِنَّكَ إِن تَذَرۡهُمۡ يُضِلُّواْ عِبَادَكَ وَلَا يَلِدُوٓاْ إِلَّا فَاجِرٗا كَفَّارٗا ٧٢
" KUMA NUHU YACE, " YAA UBANGIJI KADA KA BAR WANI DAGA CIKIN KAFIRAI A DORON QASA (wanda zai rayu ba tare da ka halakar dashi ba). DOMIN IDAN KA BARSU ZA SU BATAR DA BAYINKA, KUMA BA ZA SU HAIFA BA FACE FAJIRAI KAFIRAI ."
(SURATUL-NUHU, AYA TA 26-27)
Kunga wannan sanin halayyar mutanen ne yasa Annabi Nuhu ke fadar haka tare da irin wannan addu'ah, kuma Allah ya amsa masa.
KU LATSA HOTON NAN DAKE DOMIN KARANTA LABARAI SAHIHAI CIKIN HARSHEN HAUSA>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
To, muma mun san dabi'un wadannan mutane domin muna ji kuma muna karanta tarihin magabatansu masu dabi'u irin nasu.
Duk mai ilimi da hankali ya san cewa wadannan mutane sun san cewa duk abinda wannan Shehin malamin ke fada gaskiya ne, domin yana fito da karatukan ne daga cikin littafan da suka sani, suka yarda dasu kuma suke karantawa. Sai dai kuma duk da wannan sani nasu bai hana su rufe ido daga wannan gaskiya ba, sannan bai hana su yin sharri gare shi ba.
Shi kuma Shehin malamin bisa fikira tasa da sanin abinda yake yi zai dake ne kan abinda yake karantawa cikin littafan da buqatar su fito su qaryata abinda yake fada bisa hujja ko kuma kawo hadisai masu qaryata wadanda yake karantawa, sai dai kuma ba za su iya kawo ba kuma ba za su iya cewa abinda yake fada qarya ne ba, domin zai nuna musu a zahirance (reality).
Sakamakon ganin cewa matuqar in sun bi ko sun yarda da abinda Shehin malamin ke kawowa za su dau qasqanci a fahintarsu, wannan dalili zai sa suyi qoqarin canzawa zaman wata fuska ba ta fuskarsa da suka soma tuhumarsa ba, shi kuma ba zai yarda da canza fuskar da za suyi ba, domin buqatarsa ita su fito su qaryata zancensa bisa hujja wanda yasan ba za su iya ba.
Saboda gudun daukar qasqanci da jin kunya tare da zubewar darajarsu a idon masu ganinsu da daraja zai sa su kawo hayaniya da rudu don kada a gano cewa shi ya fi su hujja.
Wannan dai hasashe ne, amma haqiqanin abinda zai faru saninsa sai Allah, sai kuma wadanda Allah ya nuna musu lokacin za su gani.
ALLAH BAI TABA 'DAUKAKA QARYA AKAN GASKIYA BA.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
4th March 2021/ 21st Rajab, 1442.
KU LATSA HOTON NAN DAKE DOMIN KARANTA LABARAI SAHIHAI CIKIN HARSHEN HAUSA>>>>>>>>>>>>>>>>>>>