.
.
ISHAQ MUHAMMAD ISHAQ.
.
17 ga Watan Rajab.
.
A irin wannan rana ce a Shekara ta 1389 bayan hijirah, wanda ya yi daidai da 25 ga Watan Satumbar 1969 miladiyya, aka haifi Babban Gwarzo As-Sheikh As-Shahid Malam Qasim Umar Sakkwato (R.A).
An haifi Shahid ne a Unguwan Rinin Tawaye da ke cikin birnin Sakkwato. Maihaifin Shahid Shi ne Alh Ummaru Sanda gudu, Wanda yake hamshaqin Dan Kasuwa ne sananne a Garin Sakkwato a wancan lokacin, kuma ya shahara wajen taimaka wa Al'umma da Dukiyar da Allah Swt ya ba Shi, kuma Allah ya yi masa rasuwa ne ta hanyar hadarin Jirgin Sama!.
.
Mahaifiyar Shahid kuwa ita ce Hajiya Hauwa'u, amma an fi Sanin ta da Hajiya Kulu, kamar yadda Mutanen Sakkwato ke kiran Mace mai Suna Hauwa'u da laqabin 'Kulu'.
.
Ana yi wa Shahid (R.A) Alkunya ne da Baban Khadijah, wacce ita Khadija ita ce Babbar Yarsa, kuma Allah ya yi mata cikawa ne tun a Shekarar 2007 miladiyya, a lokacin tana matakin Karatun Secondary!.
.
.
Sahahid Malam Kasim Umar Mutum ne mai yawan kawaici, da hakuri, da tsantseni, da kau da Kai, da dogaro ga Allah, da Yafiya, da Tawadu'u, da yawan Ibada, da gudun Duniya tun yana Yaro Karami, kamar yanda Mahaifiyarsa ta tabbatar da hakan a wata hira da Dan Uwa Bilal Sakkwato ya yi da ita bayan Shadar Shi!, Tana cewa:
"Sam bai damu da abin duniya ba tun yana karami".
.
.
Shahid ya Fahimci kiran Jagora As-Sayyid Zakzakiy (H) ne tun a Shekarar 1984, wato tun Shahid na da kimanin Shekaru 15 a rayuwarsa kenan. Haka ma Shahid ya taba aikin Harisanci a Harka, sannan kuma ya taba rike wakilin Halka, kafin daga baya kuma ya zama Wakilin Yan uwa na Garin Sakkwato.
.
Shahid dai ya fuskanci tsangwama da takura da muzgunawa iri-iri ta wajen Azzalumai a tafarkin Gwagawarmayar tabbatar da Addinin Allah Swt, ya sha tsarewa a Kurkukuku a lokuta daban daban, dun daga Waki'o'in Abacha, in da a lokacin ya zauna gidan Yari a Kurkukun da ke garin Argungu ta Jahar Kebbi. Haka dai ya yi rayuwa Jarabawa bayan Jarabawa har zuwa Waki'ar Gwamna Wamakko barawon Akuya, inda Shahid da sauran Yan uwa fiye da 100 suka kwashe wajen Shekaru 6 a Kurkuku daban-daban, ba laifin tsaye ba na zaune!, inda aka fara tsare Su Shahid tare da sauran Yan uwa a Kurkukun Sakkwato, sannan kuma daga baya aka shirya Makircin rarraba Su a kurkukun Kudancin Kasar nan daban daban, yayin da shi Shahid ya zauna tsawon Shekaru a Kurkukun Awka da ke Jahar Anambra. Daga baya kuma Kotu ta wanke Su daga kowacce irin tuhuma, ta kuma bayar da umarnin a sake Su. Shahid da sauran 'Yan uwa sun fito ne daga Kurkuku a Shekara 2013 Miladiyya bayan kwashe Shekaru 6 cur a Kurkuku!.
.
WAKI'AR GYALLESU DA SHAHID KASIM UMAR SAKKWATO.
.
A ranar 12 ga watan 12 ne na Shekara ta 2015, Sojojin Gwamnatin Buhari suka aukawa Husainiyyar Baqiyatullahi da kuma Gidan Jagora Sheikh Zakzaky (H) a gidansa da ke Gyallesu, inda suka yi kisan Kiyashi, suka hallaka fiye da Mutum Dubu tsakanin Maza, Mata, Matasa, Yara, Tsofaffi da ma Jarirai na goye!, suka kashe suka qona suka binne a rami ba Sallah ba Sutura!.
.
A wannan Waki'ar ta Zariya Shahid Sheikh Kasim Umar yana a gidan Jagora tare da sauran Yan uwa, kuma shi Shahid ma a ranar ne ya dawo daga Kasar Lebanon tare da As-Shahid Hammad Da a wajen Jagora (H).
Ba zan manta ba ma mun gaisa da Shahid din bayan Isha yana sanye da Jallabiyya baqa. Shahid yana daga cikin Kadan daga Yan uwan da suka kubuta a wannan Waki'ar.
.
Shahid ya jima yana cikin bakin ciki da damuwa na kai wa da aka yi ga Jagora (H) alhali shi kuwa bai rabauta da samun Shahada ba a lokacin! .
Ka ji karfin Imani da cikakkiyar Sallamawa irin ta Manya-Manyan Bayin Allah fa!.
.
.
A ranar Talata 9/1/2018 ne 'Yan sanda bisa umurnin Shugabansu na wannan lokacin IGP Ibrahim Kpotun-Idris, suka bude wuta a kan yan uwa Musulmi, a lokacin da suke Muzaharar nuna kin jinin ci gaba da tsare Jagora (H) duk da kuwa irin matsananciyar Rashin lafiyar da yake fama da ita. Kuma a wannan ranar ce aka harbi Shahid Shaikh Qasim Umar. Harbin da ya yi sanadin shahadar sa a ranar Litini 5/2/2018. Bayan jinyar harbin da ya yi na tsawon Sati uku a Garin Kano!.
.
Shahid ya yi Shahada ne yana da Shekaru kusan 50 a Rayuwarsa, kuma ya bar Mahaifiyarsa a Raye, sannan ya bar 'Ya'Ya 4 a raye. 'Ya'Yan nasa Su ne: Muhammad, Ahmad, Hamid da kuma Fadima. Muhammad da Ahmad da Hamid dukan su sun yi Haddar Alkur'ani mai girma a Makarantar Fudiyya R/lemo Kano
.
Biyu daga cikin 'Ya'Yan nasa kuwa sun rasu ne tun yana raye, wato Khadija, wacce ita ce Babbar Yarsa, sai Kuma Amina wacce aka haife ta a lokacin da yake tsare a Kurkuku a lokacin Waki'ar Wamakko, kuma Allah ya yi mata Rasuwa tun kafin fitowar Su a Kurkukun, an kuma binne ta ne a Makabartar Dantata da ke Kofar Ruwa a cikin Garin Kano!.
.
Amincin Allah ya tabbata a gare Ka ya Aba Khadijah, As-Sheih Shahid Qasim Umar!.
.