Ha ha ha, Wallahi Abu Huraira da Abin Dariya Kake !!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


KO DAMA A WAJENKA SU 'DAN IBRO SUKA KOYI BARKWANCE NE  ?


Hausawa na cewa wai tafiya mabodin ilimi ce, duk wanda zaiyi tafiya dole ya riqa cin karo da wasu abubuwa na ilimi, idan ma kana karatu za ka riqa ganin wasu abubuwa wadanda na ban dariya 😂🤣 ko na al'ajabi 😱.


Na ci karo ne da wani hadisi cikin Bukhari wanda Abu Huraira ya bada labarinsa, nima naga ya kamata na kawo muku don nishadantarwa, domin wannan shafi namu ya qunshi abubuwa ne masu yawa. 


Ga nassin hadisin nan kamar haka 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



وجوب النفقة على الأهل والعيال



(5355) - حدثنا عمر بن حفص: حدثنا أبي: حدثنا الأعمش: حدثنا أبو صالح قال: حدثني أبو هريرة رضي الله عنه قال: 

قال النبي صلى الله عليه وسلم: (أفضل الصدقة ما ترك غنى، واليد العليا خير من اليد السفلى، وابدأ بمن تعول)


Bukhari yace, Amruu Bn Hafsin ya bamu labari, babana ya bamu labari , A'amashu ya bamu labari, baban Salihu ya bamu labari yace, Abu Hurairata ya bani labari yace :


Annabi (S. A. W. W) yace; 


" MAFIFICIYAR SADAQA ITA CE WACCE ( aka bawa talakawa) AKA BAR MAWADATA, KUMA HANNUN SAMA (na bayarwa) YA FI HANNUN QASA (na me karba), KU FARA DA WANDA KE SAMA. "


Abu Hurairata yace, 


Mata (wife) tana cewa, " KO DAI KA CIYAR DANI KO KUMA KA SAKE NI. "


Bawa (slave) kuma na cewa, " KA CIYAR DANI KUMA KA BANI AIKI. "


Shi kuma da (son) na cewa, " KA CIYAR DANI ZUWA GA WANDA KE KIRANA (Allah)  ."


Sai suka ce: " Yaa baban Hurairata  ! Daga Manzon Allah (S. A. W. W) ka ji wannan magana kuwa  ?" 


Sai yace,  " A'A,  WANNAN NA DAGA CIKIN KISISIYYAR (Barkwancen ) ABU HURAIRATA NE  ."


(SAHIHUL-BUKHARI, KITABUN-NAFAQAATI, BABUN WUJUBIN-NAFAQATI ALAL AHLI WAL IYAAL, HADISI MAI LAMBA 5355)


NB:- Za kuga ba dukkan wannan fassarar ne yazo cikin Arabic text din ba, domin application ne, amma idan kuka duba littafi cikin wannan Babi insha Allahu za kuga dukkan abinda na kawo din nan. 


                  DARASI 


Cikin wannan hadisi za mu koyi abubuwa da dama kamar haka :-



(1)- Idan kana son ladar sadaqa mafi girma, to, ka riqa bayar da ita ga talakawa mabuqata ba mawadata don neman suna ba. 


(2)- Ka zama mar bayarwa, ba wai ka zama kullum sai dai a baka ka (maroqi).


(3)- Za ka iya zama abin zargi matuqar kullum sai dai a baka ba tare da kai ma kana bayarwa ba. 


-------------------------------------------


DARASSUN DAKE CIKIN BARKWANCEN ABU HURAIRATA 


(4)- Ita mace 'yar tawaye ce, domin abinda take cewa Mijinta shine in dai ba zai ciyar da ita ba, to, ya saketa kawai. 


(5)- Shi kuwa bawa mai biyayya ne, idan za ka bashi abinci yaci ya qoshi, to, ko wanne aiki ne ma ka ba shi ba shi da matsala. 


(6)- 'Da kuwa ya kasance mai neman haqqinsa ne wajen ubansa don ya dora shi zuwa ga mahaliccinsa. 


ASHE DAI SU 'DAN IBRO SUN 'DOSANO BARKWARCANSU NE DAGA ABU HURAIRATA. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


         (08137925034)


22nd March, 2021/  9th Sha'aban, 1442.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post