@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DA MUZAHARA KADAI CE MAFITA DA ANNABI YUSUF (A. S) YA DAWWAMA A GIDAN KURKUKU
Duk wata koyarwa matuqar ta muslimci ce za kaga ta doru ne kan hankali da ilimi, domin tare suke tafiya kafada-da-kafada. Idan har kaga ko kaji wani furuci na fitowa daga bakin mutum da sunan da'awa, to, ka auna wannan aiki nasa da hankali da kuma ilimi, idan kaga sunyi hannun riqa sunan wannan aiki nasa shine taimakon Shaidan.
A koyarwar wannan harka islamiyyah za muga cewa Muzahara na daya daga cikin hanyoyi mafi girma wacce ake amfani da ita wajen nuna wani abu na farin ciki ko kuma baqin ciki, kuma tana daka rawa sosai wajen isar da dukkan abinda ake son isarwa. Duk wanda kaji ya soki yin Muzahara a wannan Harka, to, ka kira shi mai adawa da harka matuqar dai Muzaharar ta doru kan koyarwar Harkar ce.
Amma da za a wayi gari sai kaga ana aikata wani abu da sunan Harka kuma ta wata hanya wacce ta kaucewa koyarwar harka, to, yin gyara a kanta ko adawa da ita shine taimakon wannan Harka wacce Sayyid Zakzaky (H) ke jagoranta. Sannan kuma idan kaji wani na cewa babu mafita cikin addu'ah to, ka kira shi wanda ya jahilci Allah.
Sai dai har yanzu abinda wasu suka jahilta shine, komai na kasantuwa ne bisa qudirar Allah, abinda yaso shi ke kasantuwa. Duk wani Fadi-tashi da wata addu'a da mutum zai yi matuqar Allah bai kawo lokacin samun biyan buqatar ba mutum ba zaiga ijaba ba, kuma Shi Allah ba a yi masa dole.
Idan muka koma tarihi za muga cewa kama bayin Allah a tsare su ba wani baqon abu bane, sannan kuma hanyar da aka bi don ganin wadannan bayin Allah sun kubuta ba baquwa bace.
A lokacin da 'yan'uwan Annabi Yusuf suka yi sanadin raba shi da mahaifinsa da kuma riqe Biliyaminu sai mahaifin nasu Ya'aqub (A. S) ya cigaba da addu'ah yana kai kukansa zuwa ga Allah don ya share masa hawayensa.
.... فَصَبۡرٞ جَمِيلٌۖ عَسَى ٱللَّهُ أَن يَأۡتِيَنِي بِهِمۡ جَمِيعًاۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡحَكِيمُ ٣٨
" ...HAQURI MAI KYAU. AKWAI TSAMMANIN ALLAH YAZO MIN DASU GABA 'DAYANSU (Yusuf da Biliyaminu) , LALLE SHI MASANI NE KUMA MAI HIKIMA (cikin duk abinda ya aikata). "
(SURATUL-YUSUF:38)
A wani guri kuma yake cewa;
قَالَ إِنَّمَآ أَشۡكُواْ بَثِّي وَحُزۡنِيٓ إِلَى ٱللَّهِ وَأَعۡلَمُ مِنَ ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ ٦٨
" YACE, " ABIN SANI NI DAI INA KAI KUKANA DA BAQIN CIKINA ZUWA GA ALLAH , KUMA INA SANIN ABINDA BA KU SANI BA DAGA ALLAH. "
(SURATUL-YUSUF:68)
Tahiri bai kawo inda aka ce Annabi Ya'aqub (A. S) yayi ta Wani Abu ba ne har Allah ya tseratar masa da 'ya'yansa biyu ba, idan abin alfahari ne ma sai muce addu'o'insa ne suka zama hanyar samun biyan buqatarsa.
Manzon Allah (S. A. W. W) shi yafi kowa tausayi kuma shine babban abin misali kuma abin koyi ga dukka wani mumini, amma a lokacin da ya fara da'awarsa aka soma amsa masa sai mabiyansa suka riqa samun cutuwa daga Mushirikai, kuma yana gani amma ba shi da wani iko na hanawa ko qwato su, sai dai ya riqa basu haquri da kuma qarfafarsu cewa su qara juriya.
A cikin wannan yanayi suka zauna har sai da Allah yayi musu umarni da cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَٰتَلُونَ بِأَنَّهُمۡ ظُلِمُواْۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ نَصۡرِهِمۡ لَقَدِيرٌ ٩٣
" ANYI IZNI GA WADANDA AKE YAQARSU CEWA AN ZALUNCE SU, KUMA ALLAH MAI IKO NE AKAN TAIMAKONSU ."
(SURATUL-HAJJ:39)
Ma'ana su tashi suyi yaqi don kare kansu.
Duk da wannan umarni na Allah bai sa Sahabbai sun dau malami ba har sai da Annabi (S. A. W. W) ya furta musu cewa su dau makamin su tafi yaqi don kare kansu da daukaka addinin Allah.
Sayyid Zakzaky (H) na sane da wannan aya amma ko sau daya (1) bai taba bude baki yace a tanadi makami ko a dauke shi da nufin yaqar azzalumai ba.
Duk da cewa ba ma tare da shi (H) yanzu haka a waje, amma ana samun masu ganawa dashi lokaci bayan lokaci kuma suna zuwa mana da bayanin cewa mu qara dakewa da haquri dai, domin jarrabawa ce kuma za ta wuce.
Har zuwa yanzu da nake rubutun nan ba a sami wani furuci wanda ya fito daga bakin Sayyid (H) kan cewa a dauki makami ko a tanade shi ba. To, yanzu idan kaji wani na da'awar daukar makami wanne matsayi za ka ba shi ? Ya zama shine Jagora mai bada umarni kenan ko ?
Idan kuwa ya zama haka, to, ina matsayin wanda ake da'awa da sunan shi ake yiwa biyayya ?
KUYI NAZARI YAA KU MASU HANKALI.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
26th March, 2021/ 13th Sha'aban, 1442.