'
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
RADDI ZUWA GA SHEIKH TIJJANI BAUCHI
Yana daga cikin abinda jahilai ke tattara jahilai a gabansu suna karantar dasu cewa Shi'ah ba muslimci bace kuma 'yan Shi'ah ba musulmai bane. Duk da cewa masu irin wannan magana da wadanda ake fadawa maganar suna ganin 'yan Shi'ah na yin sallah, azumi da Hajji, sannan suna fitowa suna murna na zagayowar watan da aka haifi fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S. A. W. W).
Daga cikin qa'idojin dake maida mutum musulmi shine :-
Tauhidi, sallah, azumi zakkah da kuma Hajji, kuma kai kanka baka isa ka rantse kan cewa 'yan Shi'ah ba sa aikata wadannan abubuwa biyar dana lissafo ba.
Cikin karatun naka ka ce, " SHI'AH CE MAFI SHARRI DAGA CIKIN MASU NASABTA KANSU GA MUSLIMCI , KUMA GURBATACCIYAR AQIDA MAFI HADARI (very risk) ."
To, wannan dai maganarka ce wacce ka fada ba tare da kawo nassi cikin Qur'ani ko Hadisi dake tabbatar da wannan magana taka ba. Saboda haka mu za mu kawo maka abinda Annabi (S. A. W. W) ya fada game da 'yan Shi'ah, kuma cikin littafinku na Sunnah wacce kake da'awarta.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
وأخرج ابن عساكر عن جابر بن عبد الله قال: «كنا عند النبي صلى الله عليه وسلم فأقبل عليّ فقال النبي صلى الله عليه وسلم: والذي نفسي بيده إن هذا وشيعته لهم الفائزون يوم القيامة، ونزلت {إن الذين آمنوا وعملوا الصالحات أولئك هم خير البرية}» فكان أصحاب النبي صلى الله عليه وسلم إذا أقبل عليّ قالوا: جاء خير البرية.
Ibn Asakiri ya fitar daga Jabir Bn Abdullahi (R. A) yace : " Mun kasance a wajen Annabi (S. A. W. W) sai Aliyu ya fuskanto, sai Annabi (S. A. W. W) yace;
" NA RANTSE DA WANDA RAINA KE HANNUNSA, LALLE WANNAN DA 'YAN SHI'ARSA SUNE MASU RABAUTA RANAR ALQIYAMA ." Sai aka saukar;
" LALLE WADANDA SUKA YI IMANI KUMA SUKA AIKATA KYAKKYAWA WADANNAN NE MAFI ALKHAIRIN AL'UMMA ." Sai ya kasance Sahabban Annabi (S. A. W. W) idan suka ga Aliyu ya fuskanto (yana zuwa gare su) sai suce, " MAFI ALKHAIRIN HALITTA YA ZO !"
وأخرج ابن عدي عن ابن عباس قال: «لما نزلت {إن الذين آمنوا وعملوا الصالحات أولئك هم خير البرية} قال رسول الله صلى الله عليه وسلم لعلي: هو أنت وشيعتك يوم القيامة راضين مرضيين».
Ibn Abiy Adiy ya fitar daga Ibn Abbas (R. A) yace; " Yayin da aka saukar, " LALLE WADANDA SUKA YI IMANI KUMA SUKA AIKATA KYAKKYAWA WADANNAN SUNE MAFI ALKHAIRIN AL'UMMA. " Sai Manzon Allah (S. A. W. W) ya cewa Aliyu;
" KAINE DA 'YAN SHI'ARKA RANAR ALQIYAMA KUNA YARDADDU ABABAN YARDARSA. "
وأخرج ابن مردويه عن عليّ قال: قال لي رسول الله صلى الله عليه وسلم: «ألم تسمع قول الله: {إن الذين آمنوا وعملوا الصالحات أولئك هم خير البرية} أنت وشيعتك وموعدي وموعدكم الحوض إذا جئت الأمم للحساب تدعون غرّاً محجلين».
Ibn Mardawaihi ya fitar daga Aliyu yace; "Manzon Allah (S. A. W. W) yace min;
" ASHE BAKA JI FADIN ALLAH (T) BA; " LALLE WADANDA SUKA YI IMANI KUMA SUKA AIKATA KYAKKYAWA WADANNAN SUNA MAFI ALKHAIRIN AL'UMMA. "
TO, KAINE DA 'YAN SHI'ARKA, ALQAWARINA DA ALQAWARINKU SHINE TAFKINA (pool) IDAN AL'UMMU SUKA ZO DOMIN HISABI ZA A KIRAYE SU TA HANYAR JAJAYEN SOFANE (guraban sujjadarsu). "
(TAFSIRUL-DURRUL MANSUR NA SIYUDI)
Wannan ita ce shaidar da Annabi (S. A. W. W) yayi kan 'yan Shi'ah wadanda ka kira su da mafiya sharri.
Sannan kuma kace wai babu wani abinda 'yan Shi'ah ke yi idan watan Al-Muharram ya kama sai dai zagin Sahabbai da tsinewa matan Annabi (S. A. W. W). Har ka qara da cewa kuma ba zai taba yiwuwa mutum ya zama 'Dan Shi'ah ba har yana da wannan aqida.
To, ka sani cewa Sahabban Annabi (S. A. W. W) basu da alaqa da abinda ya faru cikin watan Muharram, domin shi kansa Yazidu (L. A) ma ana cewa ba Sahabi bane. Sannan kuma menene alaqar matan Manzon Allah (S. A. W. W) da waqi'ar Karbala ballantana a zage su?
Kuma ka sani cewa, abubuwan da suka faru basu daga cikin wata aqida tamu rubutacciya ballantana ta zama wani sharadi na shiga Shi'ah .
Sannan kuma ka qara da bada wani misali cewa duk wani mutum idan ya tashi yin auren yakan duba gida mai mutunci don ya sami matar kirki amma Annabi (S. A. W. W) ne bai san gidan mutunci ba kuma ba shi da matan kirki kamar yadda 'yan Shi'ah ke cewa.
To, idan batun matansa (S. A. W. W) a ina kaji muka ce su matan banza ne? Idan kuma Annabawa (A. S) ba sa haduwa da mata masu saba musu ne sai nace me yasa Annabi Lud da Annabi Nuhu (A. S) suka hadu da mata wadanda ba na kirki ba kamar yadda Qur'ani ya ambato ?
" ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱمۡرَأَتَ نُوحٖ وَٱمۡرَأَتَ لُوطٖۖ كَانَتَا تَحۡتَ عَبۡدَيۡنِ مِنۡ عِبَادِنَا صَٰلِحَيۡنِ فَخَانَتَاهُمَا فَلَمۡ يُغۡنِيَا عَنۡهُمَا مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـٔٗا وَقِيلَ ٱدۡخُلَا ٱلنَّارَ مَعَ ٱلدَّٰخِلِينَ ."(٠١)
" ALLAH YA BUGA MISALI DA WADANDA SUKA KAFIRTA, MATAR NUHU DA MATAR LUD, SUN KASANCE QARQASHIN BAYINMU SALIHAI SAI SUKA HA'INCE SU, SAI YA KASANCE ZAMANTAKEWAR DASU BAI AMFANAR DASU DA WANI ABU BA, KUMA AKA CE; " KU SHIGA WUTA TARE DA MASU SHIGA ."
(SURATUL-TAHRIM:10)
Barin kuma mu qara sanar da kai abinda baka sani ba daga bakin Umar Bn Khaddab.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
330- حَدَّثَنَا سُفْيَانُ ، عَنْ يَحْيَى يَعْنِي ابْنَ سَعِيدٍ ، عَنْ عُبَيْدِ بْنِ حُنَيْنٍ ، عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ ، قَالَ : أَرَدْتُ أَنْ أَسْأَلَ عُمَرَ فَمَا رَأَيْتُ مَوْضِعًا ، فَمَكَثْتُ سَنَتَيْنِ ، فَلَمَّا كُنَّا بِمَرِّ الظَّهْرَانِ ، وَذَهَبَ لِيَقْضِيَ حَاجَتَهُ ، فَجَاءَ وَقَدْ قَضَى حَاجَتَهُ ، فَذَهَبْتُ أَصُبُّ عَلَيْهِ مِنَ الْمَاءِ ، قُلْتُ : " يَا أَمِيرَ الْمُؤْمِنِينَ ، مَنْ الْمَرْأَتَانِ اللَّتَانِ تَظَاهَرَتَا عَلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ، قَالَ : عَائِشَةُ ، وَحَفْصَةُ " .
Sufyan ya bamu labari daga Yahya, yana nufi Ibn Sa'eed, daga Ubaidu Bn Hunain, daga Ibn Abbas (R. A) yace,
" Na so na tambayi Umar amma ban ban sami guri (wanda ya dace nayi masa tambayar ba), sai na zauna har shekaru biyu (ina riqe da wannan buqata tawa). A yayin da muka je Marra Zahrani sai ya tafi don biyan buqatarsa, sai yazo bayan ya biya buqatar tasa, sai na bi shi ina zuba masa ruwa, sai nace, " Yaa shugaban muminai ! Wadanne mata biyu ne suka hada kansu (don cutar da Annabi (S. A. W. W) ne) ? Yace;
" A'ISHATU DA HAFSA NE ."
( MUSNAD-AHMAD, MUSNAD KHULAFA'AR-RASHIDEEN, BABUN FADHA'ILU UMAR BN KHADDAB, HADISI MAI LAMBA 330)
Ka koma cikin Tafsirin wannan aya za kaga abinda aka ce kan wannan al'amari.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
29th March, 2021/ 16th Sha'aban, 1442.