@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ITA AYA BA A TABA SOKETA DA HADISI
Auren Mutu'ah ba shi daga cikin wata aqida cikin aqidun Shi'ah wanda za ace aikata shi wajibi ne ko kuma rashin yinsa sabawa Allah ne. Sai dai shi yana daga cikin abubuwa ne na halas wanda ake yinsa yayin lalura.
Shi wannan aure ana yinsa ne da wasu qa'idoji na shari'a ba ta yadda kowa yaga dama ba, domin tun zamanin Annabi (S. A. W. W) ake yinsa har bayan ransa. Sannan kuma ba a fara yinsa ba har sai da aya ta sauko kan wannan al'amari mai girma don samarwa al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W) mafita ko sauqi.
Ga ayar nan kamar haka;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
.....فَمَا ٱسۡتَمۡتَعۡتُم بِهِۦ مِنۡهُنَّ فَـَٔاتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ فَرِيضَةٗۚ......
" KUMA WADANDA KUKA JI DADI DASU DAGA CIKINSU KU BASU LADARSU FARILLA..."
(NISA'I, AYA TA 24)
An kira wannan ne da lada ba sadaqi ba, domin wani aiki ne na qanqanin lokaci wanda akayi yarjejeniya wajen aikata shi, kuma haqqi ne ka bawa mutum ladan wani aiki da zai yi maka don biyan buqatarka.
An sami riwayoyi da suka yi nuni kan cewa wannan ayar ta sauka ne kan al'amarin auren Mutu'ah. Ga riwayoyin nan kamar haka;
وقد روى عن ابن عباس وطائفة من الصحابة القول بإباحتها للضرورة وهو رواية عن الإمام وكان ابن عباس وأبي بن كعب وسعيد بن جبير والسدي يقرؤن « فما استمتعتم به منهن إلى أجل مسمى فآتوهن أجورهن فريضة » وقال مجاهد نزلت في نكاح المتعة
Haqiqa an riwaito daga Ibn Abbas da wasu jama'ah daga Sahabbai fadinsu cewa an halarta ne bisa lalura, ita riwaya daga Imamu. Ibn Abbas da Ubaiyu Bn Ka'ab da Sa'eed Bn Jubair da Saddiy suna karantawa,
" WADANDA KUKA JI DADI DASU DAGA CIKINSU ZUWA WANI AJALI AMBATACCE KU BASU LADANSU FARILLA. "
Mujaheed yace, " Ta sauka ne kan auren Mutu'ah. "
Ya cigaba da cewa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
وقوله تعالى « ولا جناح عليكم فيما تراضيتم به من بعد الفريضة » من حمل هذه الآية على نكاح المتعة إلى أجلمسمى قال لا جناح عليكم إذا إنقضى الأجل أن تتراضوا على زيادة به وزيادة للجعل قال السدي إن شاء أرضاها من بعد الفريضة الأولى يعني الأجر الذي أعطاها على تمتعه بها قبل إنقضاء الأجل بينهما فقال أتمتع منك أيضا بكذا وكذا فإن زاد قبل أن يستبرئ رحمها يوم تنقضي المدة وهو قوله تعالى « ولا جناح عليكم فيما تراضيتم به من بعد الفريضة »
Kuma fadinSa (T),
" KUMA BABU LAIFI A KANKU CIKIN ABINDA KU KAYI YARJEJENIYA DASHI BAYAN FARILLA (ladan da kuka ba su). "
Wanda ya dauki wannan aya akan auren Mutu'ah zuwa ajali ambatacce. Yace, " Babu laifi a kanku idan kuka qare wannan lokaci da kuyi (wani) yarjejeniya akan yin qari dashi, shi qarin kuwa zuwa wani lokaci ."
Saddiy yace, " Idan yaso zai nemi yardarta bayan farillar daya ba ta a farko, abin nufi ladan da ya ba ta akan jin dadi (Mutu'ah) da ita kafin wannan ajali dake tsakaninsu ya qare. Sai yace, " ZAN QARA YIN MUTU'AH DAKE KAWAI DA KAZA DA KAZA. "
Idan yayi qari kafin tayi istibra'in mahaifarta (tsarkin farji) a ranar da ta qare adadinta .Wannan shine fadinSa Madaukaki;
" KUMA BABU LAIFI A KANKU CIKIN ABINDA KU KAYI YARJEJENIYA DASHI BAYAN FARILLA (na farko) ."
(IBN KATHEER)
Sannan kuma ya zo cikin Durrul-Mansur na Suyudi cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
وأخرج الطبراني والبيهقي في سننه عن ابن عباس قال: كانت المتعة في أول الإسلام، وكانوا يقرأون هذه الآية {فما استمتعتم به منهنَّ إلى أجل مسمى} الآية.
'Dabarani da Baihaqi sun fitar cikin Sunan nasa, daga Ibn Abbas (R. A) yace;
" Mutu'ah ta kasance a farkon muslimci, sun kasance suna karanta wannan ayar, " KUMA ABINDA KUKA JI DADI DASHI DAGA GARE SU ZUWA WANI AJALI ."
(DURRUL-MANSUR NA SUYUDI)
Kunga shima anan yana tabbatar da cewa aya ce ta sauka kafin fara jin wannan aure.
Mu qara duba wannan riwaya ta qasa kawai,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" .7185 - حدثنا محمد بن المثنى، قال: ثنا محمد بن جعفر، قال: ثنا شعبة، عن الحكم، قال: سألته عن هذه الآية: {والمحصنات من النساء إلا ما ملكت أيمانكم} إلى هذا الموضع: {فما استمتعتم به منهن} أمنسوخة هي؟ قال: لا. قال الحكم: قال علي رضي الله عنه: لولا أن عمر رضي الله عنه نهى عن المتعة ما زنى إلا شقي
Muhammad Bn Musannah ya bamu labari yace, Muhammad Bn Ja'afar ya bamu labari yace, Shu'ubatu ya bamu labari daga Hakam yace, an tambaye shi game da wannan aya :
" DA KUMA KATANGAGGU DAGA MATA, FACE ABINDA HANNAYENKU SUKA MALLAKA. " Har zuwa wannan guri, "KUMA ABINDA KUKA JI DADI DASHI DAGA GARE SU ."
Shin, sokakkiya ce? Yace, " A'A, (ba a soke ta ba) "
Hakeem yace; Aliyu (R. A) yace, " DA BA DON UMAR YA HARAMTA MUTU'AH BA DA BABU MAI YIN ZINA IN BA SHAQIYYI BA !"
(TAFSIRUL-'DABARI)
Kunga anan ana nuna mana ne cewa Umar ne ya haramta auren Mutu'ah ba Annabi (S. A. W. W) ba, sai dai an qirqiro hadisai na qarya wadanda aka jingina su gare shi (S. A. W. W) don a kare wannan aiki na Umar. Kun san su sunfi gamsuwa su yiwa Annabi qarya don bawa Sahabbai kariya.
To, bisa riwayoyin da muka kawo a sama sun tabbatar mana cewa aya ce ta sauko sannan aka fara yin auren Mutu'ah. Sai dai kuma cikin Bukhari da Muslim sunce wai Annabi (A. A. W. W) ya haramta shi a yaqin Khaibar.
Mu kuma abinda Allah (T) ya tabbatar mana cikin Qur'ani shine,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
۞مَا نَنسَخۡ مِنۡ ءَايَةٍ أَوۡ نُنسِهَا نَأۡتِ بِخَيۡرٖ مِّنۡهَآ أَوۡ مِثۡلِهَآۗ أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ ٦٠١
" BA MA SOKE WATA AYA KO MU JINKIRTAR DA HUKUNCINTA FACE MUN ZO DA MAFI ALKHAIRINTA KO KUMA MISALINTA . BA KU SAN CEWA ALLAH MAI IKO NE KAN KOMAI BA ?"
(SURATUL-BAQARATI, AYA:106)
Sannan idan kuka koma cikin NAASIKH wal MANSUKH za kuga ba a kawo wannan ayar data sauka kan auren Mutu'ah cikin sokakku ba, sannan babu wata ayar da aka kawo aka ce ta soke wancan ayar.
Tambaya, shin, a ina aka ce hadisi na soke aya ? Ko kuma inda Annabi (S. A. W. W) yace haka ?
SAI MUN JI DAGA GARE KU
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08126385470)
16th March, 2021/ 3rd Sha'aban, 1442.