TARIHIN SHAIKH IBRAHIM ZAKZAKY (H) A TAQAICE
'Yan Uwansa :
Mahaifin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wato Malam Yaqubu Aliyu, ya rasu ya bar ‘ya’ya goma sha shida ne cif a duniya, takwas maza, takwas mata, su Shaikh Zakzaky (H) su bakwai ya bari ta wajan mahaifiyarsu Hajiya Salaha, wato wanda suka haxa uwa xaya uba xaya, maza huxu, mata uku, ga su a bisa jerinsu; Abdulqadir Yaqub, Maryam Yaqub, Fatimah Yaqub (Goggon Qaura), Ibrahim Yaqub (Sheikh Zakzaky), Badamasi Yaqub, Yahya Yaqub, sai ‘yar autarsu Maimunatu Yaqub.
Ta vangaren sauran ‘yan uwan Shaikh Zakzaky guda 9 kuwa, sun haxa mahaifi ne kawai da su, wato mahaifinsu xaya, amma mahaifiyarsu ita ce Hajiya Aminah wacce ake qira (Iya mai Manja), su tara ne, maza huxu, mata biyar, ga su a bisa jerinsu; Muhammad Sani Yaqub, Ramatu Yaqub, Karimatu Yaqub, Usman Yaqub (Sarkin Malaman Fadar Zazzau), Maryam Yaqub, Abubakar Yaqub, Salihu Yaqub, Zaliha Yaqub, sai ‘yar autarsu Hajara Yaqub.
A jumlace, waxannan sune ‘yan uwan Shaikh Zakzaky (H) na jini, kuma Shaikh (H) ne xa na shida a wajan mahaifinsu, amma na biyar a wajan mahaifiyarsa, (bisa lissafawa da wansa Zubairu Yaqub, wanda ya rasu yana qarami).
Haihuwarsa :
An haifi Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne gab da hudowar Alfijir na ranar Talata 15 ga watan Sha’aban 1372 Hijiriyya, wanda ya yi daidai da Talata 5 ga watan Mayu shekara ta 1953 Miladiyya. An haife shi ne a bayan Fada da ke unguwar Kwarbai cikin birnin Zariya jahar Kadunan Nijeriya.
Zamu cigaba...
Daga Wakilinmu:
Auwal M Tukur
09072712469
Daga littafin da Cibiyar Wallafa Jawaban Sheikh Zakzaky (H) ta buga Mai suna "SHEIKH ZAKZAKY IKON ALLAH".