CIGABA... SHIN KUNKO SAN WANENE SHAIKH IBRAHIM ZAKZAKY??? Na 2

          BABI NA FARKO 


TARIHIN SHAIKH IBRAHIM ZAKZAKY (H) A TAQAICE


Kontagora Media Forum

 KMF/4321/SC/002


Mahaifinsa :


Sunan mahaifin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Malam Yaqubu Aliyu, ana masa laqabi da Malam Magaji, tarihi bai ambaci takameme shekarar da aka haifi Malam Yaqubu Aliyu ba, amma ana kyautata zaton an haife shi ne a shekarar 1902. Ya taso a gidan malanta da ilimi, dan haka ya taso ne da karatu da riqo da addini, tun tasowarsa mutum ne mai haquri da sanin ya kamata, an shaide shi da kyawawan xabi’u da aiki da abin da ya karanta. Sana’arsa ita ce koyarwa da kuma Noma da Kiwo. Ana kyautata zaton ya rayu a duniya ne tsawon shekaru 70 daidai (1902 – 1972), ko shekaru 72 a qidayar Hijiriyyah.


Allah ya yi wa mahaifin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Malam Yaqubu Aliyu rasuwa ne a watan Fabarairu na shekarar 1972, ya rasu ne a wani kududdufi da ke bayan unguwar Qwarbai cikin birnin Zariya, a lokacin da ya je ceto wata Akuya da ta faxa cikin kududdufin lokacin da ta je shan ruwa, kuma an yi masa jana’iza aka binne shi a maqabartar da ke kusa da kududdufin, yanzu haka qabarinsa yana wurin. Ya rasu ya bar ‘ya’ya 16, maza takwas, mata takwas.


Mahaifiyarsa :


Malama Salaha Muhammad Gixaxo, wacce aka fi sani da Hajiya Hari Jamo ita ce mahaifiyar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Bafulatanar usuli ce daga qabilar Fulani Toronkawa, kakanta Malam Abdulqadir ya taho ne daga qasar Mali ya yaxa zango a Zariya. Laqabinta na “Hari” a harshen Fulatanci yana nufin “Wacce aka haifa a Damina”. An haifi Hajiya Salaha ne a shekarar 1924 a cikin birnin Zariya. Ta haifi ‘ya’ya 12 da mijinta Malam Yaqubu, amma 5 daga ciki sun rasu tun suna qanana, kuma Shaikh Zakzaky (H) shi ne xa na biyar a wurinta.


Mahaifiyar Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) Hajiya Salaha (Hari Jamo) malama ce mai ilimin addini, ta kasance tana karantar da mata maqwabta da matan unguwa da kuma qananan yara a cikin gida. An shaideta da yawan ibada, musamman karatun Alqur’ani da yawan addu’a. Ta rasu ranar 17 ga watan Nuwamba na qarshen shekarar 2014 (25-Muharram-1436), sakamakon jinyar da ta yi fama da ita, kuma ta rasu tana da shekaru 90 daidai a qidayar Bature (1924-2014), ko shekaru 93 a qidayar Hijira. Ta bar ‘ya’ya 6 da jikoki masu yawa, qabarinta yana Hubbarenta da ke unguwar Jushi a cikin birnin Zariya.

Zamu cigaba...


Daga Wakilinmu:

 Auwal M Tukur

09072712469

Daga littafin da Cibiyar wallafa jawaban Sheikh Zakzaky (H) ta wallafa Mai suna "SHEIKH ZAKZAKY IKON ALLAH".

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post