TARIHIN RAYUWAR SHAIKH IBRAHIM ZAKZAKY A TAQAICE
Karatuttukansa :
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ma’abucin ilimi ne da ya yi karatu mai zurfi a fannonin ilimi guda biyu, wato karatun addini da kuma na zamani (Boko), kuma a lokacin yin waxannan karatuttuka ya bi ta hanyoyi biyu ne da aka saba bi bisa al’ada, wato tsarin karatun gida (karatun Zaure), da kuma tsarin karatun Nizamiyya na makarantun zamani.
Karatunsa na Zamani :
A fannin karatun zamani na Boko, ko mu ce karatun Nizamiyya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara karatun ne yana da shekaru 17 a duniya, dan haka bai yi karatun Primary kai tsaye ba. Ya fara shiga makarantar horar da malaman Larabci da ake qira “Fada Provincial Arabic School, Zaria” ne a shekarar 1969 zuwa 1971. A shekara huxu ake gama wannan makarantar, amma saboda basirar Shaikh da hazaqarsa ya kammala ta ne cikin shekaru biyu kacal. A lokacin da yake karatu a wannan makaranta ta FPAS yana koyarwa a makarantun Islamiyyah har guda huxu, xaya a unguwar Kwarbai, xaya a unguwar Kakaki, xaya a unguwar Lemu, xaya kuma a Rimin Tsiwa duk dai a cikin garin Zariya.
A tsakiyar Shekarar 1971 ya tafi makarantar koyon harshen larabci “School for Arabic Studies” da ke birnin Kano don zurfafa karatun harshen Larabci, amma bayan an yi masa gwaji (Interview) an ji ya iya turanci, sai shugaban makarantar ya canza masa ra’ayi daga karatun harshen Larabci zuwa karanta darussan Turanci. Ya kammala wannan makaranta ne a shekarar 1975.
A lokacin da yake karatu a S.A.S Kano ya gwama karatun “Grade Two” xinsa ne da karatun darussa huxu na “Advance Level”, darussan kuwa sune; Economics, Government, Islamic Studies, da kuma Hausa, dan haka bayan ya kammala jarabawar “Grade Two” sai kuma ya zarce da ta “Advance Level” a lokaci guda. Da jarabawowin guda biyu suka fito, sai ya zamo duk ya ci su, takardunsa duk sun yi kyau, wannan ne ya ba shi damar samun karatun digiri kai tsaye a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Ya kasance yana halartar karatuttukan addini a zaurukan manyan malamai da dama na birnin Kano a lokacin da yake xalibta a can.
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU Zariya) ne a shekarar 1976, inda ya karancin fannin tattalin arziqi (Economics). Ya kammala digirinsa a shekarar 1979, amma a lokacin da yake jarabawarsa ta qarshe ta kammala karatun, sai jami’an tsaro suka kama shi suka tsare bisa tuhumar hana wasu mashaya giya yin taronsu na fasadi a harabar makarantar, wannan ya sa bai samu damar yin wasu takardu (Papers) na jarabawarsa ba, har sai da aka sako shi daga kurkukun Inugu a 1984, sai hukumar makarantar ta ba shi damar qarasa jarabawar tasa, amma bayan ya rubuta jarabawar suka ga ya yi nasara, sai suka riqe sakamakon suka hana shi, wato har zuwa yau hukumar jami’ar ba su ba Shaikh Zakzaky (H) digirinsa ba. Amma rahotanni sun tabbatar da cewa shi ne xalibi mafi hazaqa a wannan shekarar, wato ya fita da “First Class” ne.
A jumlace, za mu iya cewa, karatun Boko daga fara shi zuwa kammala digiri, ana yinsa ne a tsawon shekaru goma sha tara (19), amma Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya kammala karatun zuwa digiri ne a tsawon shekaru Goma (10) kacal! Domin karatun shekaru bakwai na Firamare, ya yi shi ne a shekaru biyu kacal a FPAS Zariya. Karatun shekaru shida na Sakandire kuma, ya yi shi ne a shekaru huxu kacal a S.A.S Kano. Sa’annan ya yi digirinsa a ABU Zariya cikin shekaru 4. Wannan zai nuna baiwa da hazaqa ta musamman da Allah Ta’ala ya yi wa Shaikh Zakzaky (H) ne.
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a lokacin xalibta ya riqe muqamai a qungiyoyin xalibai na cikin makarantun da ya yi, amma mafi fice shi ne muqaman da ya riqe a Jami’a. A shekarar 1978 ya zama babban sakataren qungiyar xalibai musulmi “Muslim Students Society” (wato MSS a taqaice) a jami’ar Ahmadu Bello, sannan daga baya ya zama mataimakin shugaban qungiyar ta MSS na qasa baki xaya mai kula da harkokin qasashen waje a 1979.
Zamu cigaba...
Daga wakilinmu
Auwal M Tukur
09072712469
Daga littafin da cibiyar wallafa jawaban Sheikh Zakzaky ta wallafa Mai Suna "SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH".