Cigaba... SHIN KOKUN SAN WANENE SHAIKH ZAKZAKY??? Kashi na 5

      BABI NA FARKO

TARIHIN RAYUWAR SHAIKH ZAKZAKY A TAQAICE

Yarintarsa :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya taso a gida na addini da tarbiyya, dan haka tun yana yaro qarami ya gudanar da yarinta ce mai tsabta, sam ba a san shi da qin jin magana, ko faxa da yara, ko mugunta da qeta, ko nuna fin qarfi ga wanda ya fi ba. An san shi ne a matsayin yaro mai dattaku, mai tarbiyya, mai girmama na gaba, mai ladabi ga iyaye, mai tausayin qanne, mai taimakon tsofaffi, mai son karatu, kuma mai qwazo da rashin kasala.


Iyaye da ‘yan uwan Shaikh Zakzaky (H) sun tabbatar da cewa tun yana qaramin yaro bai tava zuwa neman qarin miya ba, wato in an zuba masa abinci komai qarancin miya ba zai ce a qara ba, kuma in yana cin abinci miya ta qare, to ko bai qoshi ba haka zai haqura, amma ba zai je ya ce a qara masa miya ba. Wannan yana nuna halin dattaku da Makarimul-Akhlaq xin Shaikh (H) ne tun yana qaraminsa.


Wanda suka san tasowa da yarintar Shaikh Zakzaky (H) sun tabbatar da kyawawan halayensa na yarinta. Dattijo kuma xan Sarkin Zazzau Aliyu Xan Sidi, wanda aka fi sani da Alhaji Basiru Aliyu Xan Sidi ya faxi cewa; “A wancan lokaci (na yarinta), sanin da na yi wa Malam Ibraheem Zakzaky yaro ne mai hankali da biyayya ga na gaba da shi, tare da dattako, ban kuma tava jin wani abu na laifi ko kuma aibu akansa ba!” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 84).


Shi ma Magayaqin Zazzau Alhaji Abubakar Jibrin ya faxi cewa; “Ni dai na san shi (Ibraheem Zakzaky) yaro ne mai kawaici, sannan bai cika maganganu haka barkatai ba… A makarantun da ya yi yana da ladabi da biyayya ga duk na gaba da shi a yawan shekaru, domin mu nan ba mu samu wani abu da za mu soka game da shi ba” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 82).


Wata dattijuwa ‘yar kimanin shekara 100 daga zuriyar gidan su Shaikh Zakzaky (H), wacce ake kira Goggo Fatimah, ta bada kyakkyawar shaida akan yarintar Shaikh xin, ta ce; “Shi dai lokacin da aka haife shi mun ga abin mamaki… tun farko mun ga alamar zai zama wani abu. Yana da biyayya qwarai da gaske. Mutum ne mai zumunci, ya san nasa, duk inda suke zai sa qafa ya bi su da alheri, dama (tun asali) da alherinsa ya taso, ba yanzu ne ya fara ba, tuntuni haka yake… Tun yana yaro bai san faxace-faxacen nan na yara ba, ba ruwansa, shi ya taso kamar Dattijo ne, tun yana yaro kamar dattijo yake, irin sakarcin nan ma na yara shi ba ya yi, sai ma idan yara sun yi abun da bai dace ba, sai ka ga ya tsawatar musu” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 68).


Wani abokin Shaikh da suka taso tare, mai suna Malam Wadan Mai Raqumi yana cewa; “Ibraheem mutum ne wanda tun yana yaro ba ya son wasa ko wulaqanta addini, (sannan) shi ba ya irin mugun wasannin nan da yara kan yi, ko a unguwa ko a makaranta, idan mun zo muna yin (mugun wasa) sai ka ga ya koma gefe guda abinsa” (Mujallar Gwagwarmaya, fitowa ta 3, shafi na 24).


A taqaice, Shaikh Zakzaky (H) rinin Allah ne, tun tasowarsa ya taso ne a matsayin kamili mai halin dattaku, duk wani shexanci na yara bai yi shi ba, da kamala da kyawawan halaye ya taso. Kenan halaye da xabi’un Shaikh Zakzaky (H) rinin Allah ne, tun ran gini ran zane !

Zamu cigaba...

Daga Wakilinmu

Auwal M Tukur

09072712469

Daga littafin da cibiyar wallafa jawaban Sheikh Zakzaky ta wallafa mai suna "SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH".

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post