BABI NA FARKO
Suna da Laqabinsa :
Sunan jagora shi ne Ibraheem, laqabinsa kuma Al-Zakzaky, wanda fassararsa ke nufin mutumin Zariya, wato mutumin qasar Zazzau, ko Bazazzagi a taqaice. Laqabin Al-Zakzaky ya samo asali ne a lokacin yana makaranta, sai ya zamo su biyu sunansu ya zama iri xaya (Ibrahim Yaqubu), sai aka ce kowa ya qara suna xaya a jikin nasa, sai Shaikh ya qara Zakzaky a jikin sunansa, daga nan ake qiransa Al-Zakzaky.
Wani laqabinsa da ya shahara shi ne laqabin da Shaikh Usman bin Fodiye ya laqaba masa tun sama da shekaru 200 kafin haihuwarsa, wato laqabin Sharafuddeen, wanda fassararsa ke nufin “Mai Xaukaka Addini”. Sai kuma laqabin Ibraheemul-Magriby, wanda ke nufin “Mutumin Yamma” wanda shi ma laqabi ne da ya samo asali daga zantukan waliyai magabata. Sannan akwai laqabin “Khaleel” wanda iyalinsa Malama Zeenatuddeen ce kaxai take kiransa da wannan laqabi. A taqaice Shaikh (H) yana da laqubba guda uku, wato Zakzaky, da Sharafuddeen, da Al-Magriby, sai kuma na khass da iyalinsa ke kiransa da shi, wato Khaleel.
Siffofinsa :
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) baqin fata ne mutumin Nijeriya a Afirka ta yamma. Matsakaici ne a tsawo amma ya fi kusa da gajarta. Yana da matsakaiciyar qiba. Kyakkyawa ne mai kyan sifa da kyan diri. Yana da manyan idanu matsakaita girma. Yana da faffaxan goshi, da faffaxan qirji, da karan hanci. Yana da hasken fata da madaidaitan kunnuwa. Yana da mayalwacin gemu amma bai da qasumba. Yana da tsaga bibiyu a kwivin idanuwansa biyu, wanda hakan ke alamta cewa shi Bamalle ne a qabilar Fulani. Ta ko ina bai da naqasa a halitta. Yana da cikar kwarjini da Haiba. Yana da izza a cikin tafiya da zamansa. Haziqi ne mai fikira da hangen nesa. Fasihi ne mai fasahar magana. Xan baiwa ne a ilimi, Fikira da sanin fannoni.
Daga Wakilinmu:
Auwal M Tukur
09072712469
Daga littafin da cibiyar wallafa jawaban Sheikh Zakzaky ta wallafa Mai suna "SHAIKH IBRAHIM ZAKZAKY IKON ALLAH".