Cigaba SHIN KOKUN SAN WANENE SHAIKH??? Na 8

 


BABI NA FARKO

TARIHIN RAYUWAR SHAIKH IBRAHIM ZAKZAKY A TAQAICE.

Istibsarinsa :


Duk da cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tsatson Manzon Allah (S) ne, to amma yanayi na Biy’a (Inviroment) ya sa an haife shi a cikin Sunni, kuma hatta karatuttukan addini da ya taso da su na Mazhabar Malikiyya ne ta Ahlis-Sunnah.


Babu tabbataccen batu game da takameme lokacin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi riqo da Mazhabar Ahlul-Bait (AS), to amma ta bayyana ga mutane cewa Shaikh yana bin tafarkin Ahlul-Bait (AS) ne a shekarar 1980, a lokacin yana da shekaru 27 da haihuwa. Almajiransa (wanda kusan baki xayansu Ahlis-Sunnah ne) sun soma gunaguni game da yadda suka ga Shaikh xin ya soma yin wasu abubuwa sabbi da ba su sani ba a cikin Alwala da Sallarsa a wancan lokacin.


Shaikh Zakzaky (H) da kansa ya tava bada labarin wannan rashin fahimta da sashen almajiransa suka nuna a wancan lokaci, wanda hakan ke tabbatar da cewa ya fara fitowa fili yana aikata koyarwar Ja’afariyya a ibadarsa ne tun a 1980, ya ce; “Na san tun 1980 lokacin da aka yi “Funtua Declaration” akwai waxanda suka zo suka same ni, cewa sun ga na yi Alwala amma na shafa qafa ne, sai na qyale, sai wani ya ce musu; ai shi Shi’a ne, shi ya sa yake shafa a qafa, amma ni ban ce musu komai ba, (sai) wani ya ce ya ga ina Qunuti ina xaga hannu, shi ma na qyale ban ce masa komai ba, wani kuma ya ce ya ji ni ina Tasbihi a Ruku’u a bayyane, shi ma sai na qyale, duk dai na qi in amsa masu.


“Wani lokaci kuma mun tafi Sakkwato a dai cikin shekarar 1980, sai nai Sallar Azuhur da La’asar, sai na karanta “Bismillahir-Rahmanir-Raheem” a bayyane, wani sai ya tambaye ni, ya ji a cikin Sallah na yi Bisimilla a bayyane, sai na ce masa e, Manzon Allah (S) ya kasance yana yin haka, saboda su mutane akan wannan, sai su yi faxa, ko kuma su ce addininka daban ne, saboda haka ni ban so tun farko mu fitinar da mutane (ba)” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 154).


A wani zama na Khass da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi da wakilan ‘yan uwa na manyan Da’irori a wancan lokaci, ya bayyana musu cewa; “Ana jira in ce ni Shi’a ne domin a tarwatse, to, ni Shi’a ne! Tun da can ni Shi’a nike akai, a Shi’ar ka sanni, in ba ka sanni a haka ba to ba ka da basira! Saboda haka a Shi’a nike, kuma Insha Allah a Shi’a zan mutu, kuma ina fata Allah ya tasheni da Shi’a a ranar Qiyama, ya kai ni mokomar Shi’a!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 155).


Kenan, a bisa wannan jawabi, duk wanda ya fahimci Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), to ya shigo ne ya samu Shaikh (H) a bisa aqidar Shi’a da Wila’a ga Ahlul-Bait (AS) da kuma biyayya ga koyarwarsu, amma saboda maslaha ta Biy’ar da yake rayuwa a ciki, da kuma tausayin kar mutane su fitinu su nesanci tafarkin tsiransu, ya sa Shaikh (H) bai bayyana wannan aqida da Mazhaba ta Ahlul-Bait (AS) a fili ba, ya bar abin ga kansa kawai, sai da yanayi ya kyautata sannan ya shelanta tare da ayyana tafarkin da yake riqo da shi a fili, wanda sakamakon hakan ya sa miliyoyin almajiransa suka rungumi aqidar ba tare da qyama ba. Wannan ya sa Shaikh Zakzaky (H) ya zama mutumin da ya fi kowa nasarar canza akalar aqidar miliyoyin mutane daga Sunnah zuwa Shi’a a tarihin Musulunci baki xaya!


Uwargidansa :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana da mace xaya, wannan kuwa ita ce Malama Zeenatuddin Ibraheem, ita ce mahaifiyar duk ‘ya’yansa, wato daga gareta zuriyarsa ta samu. An haifi Malama Zeenatuddin ne ranar 14 ga watan Ogusta na shekarar 1961, a unguwar Sabon Gari da ke cikin garin Zariya. Sunan mahaifinta Malam Ibrahim, sunan mahaifiyarta Malama Maryam, su huxu ne a wajan mahaifiyarsu kuma dukkaninsu mata, Nafisa Ibraheem, Maryam Ibraheem, Zeenatuddeen Ibraheem da Khadija Ibraheem.


Malama Zeenatu ta fara karatun firamare ne a wata firamare ta Mishon da ke Sabon Gari Zariya, daga baya ta koma Firamaren Jafaru, wato St, George Primary School Zaria, daga 1967 zuwa 1973. Daga nan ta tafi “Commercial College, Zaria” a shekarar 1977, ta kammala a 1979, sai ta tafi CAST Katsina, ta shekara biyu a can, daga nan sai ta shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1981 inda take karanta fannin aikin Banki, amma ba ta samu damar qarasawa ba sakamakon korarsu da makarantar ta yi saboda harkokin addini a sekarar 1982.


Daga nan Malama Zeenatu ta tafi karatu a wata “Hauza Ilmiyyah” da ke qasar Iran, daga shekarar 1982 zuwa 1984. Malama Zeenatu baiwar Allah ce ma’abuciyar hidima ga addini da tsayuwa akan hadafi, mace ce haziqa mai tsananin riqo ga karantarwar addini da fikirar Harka Islamiyya. An shaideta da yawan ibada da kishin addini da tsananin tausayawa mata.

Zamu cigaba...


Daga Wakilinmu

Auwal M Tukur

09072712469

Daga littafin da cibiyar wallafa jawaban Sheikh Zakzaky ta wallafa mai suna  "SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH".

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post