@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KHUDUBOBIN SALLAH AN CANZA MUSU MATSAYI
Ba tare da doron bayani ba an san cewa zamanin Manzon Allah (S. A. W. W) a kanyi Khudubar sallar juma'ah ce bayan idar da sallah, domin lokacin ne kowa ya halatta yadda za a isar musu saqo fiye da yadda za ayi ta kafin sallah. Wannan canji kuwa ya auku ne a lokacin daular miyagun shuwagabanni na Umayyawa yayin da suka soma tsinewa Imam Ali (A. S) akan Mimbari. Ganin mutane na tashi su tafi don ba sa son jin wannan tsinewa sai aka dawo da yin Khudubar kafin sallah, domin duk wanda ke son samun jam'i sai ya saurari wannan tsinewa ba bisa son rai ba.
Haka zalika Khudubar Sallar Idodi ma ana yinsu ne kafin sallah, amma sai aka canza aka kaita bayan sallah. Bamu san menene hujjarsu anan ba, sai dai bisa tunani za mu iya cewa su dai kawai so suke suka sun canza dukkan wasu abubuwan da Annabi (S. A. W. W) yayi a halin rayuwarsa.
KU LATSA HOTON NAN DAKE DOMIN KARANTA LABARAI SAHIHAI CIKIN HARSHEN HAUSA>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
Ga misali nan kamar haka,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
10848- حَدَّثَنَا قُتَيْبَةُ بْنُ سَعِيدٍ ، حَدَّثَنَا لَيْثٌ ، عَنْ خَالِدِ بْنِ يَزِيدَ ، عَنْ سَعِيدِ بْنِ أَبِي هِلَالٍ ، عَن أَبِي يَعْقُوبَ الْخَيَّاطِ ، قَالَ : شَهِدْتُ مَعَ مُصْعَبِ بْنِ الزُّبَيْرِ الْفِطْرَ بِالْمَدِينَةِ ، فَأَرْسَلَ إِلَى أَبِي سَعِيدٍ ، فَسَأَلَهُ كَيْفَ كَانَ يَصْنَعُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ؟ فَأَخْبَرَهُ أَبُو سَعِيدٍ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم : " كَانَ يُصَلِّي قَبْلَ أَنْ يَخْطُبَ ، فَصَلَّى يَوْمَئِذٍ قَبْلَ الْخُطْبَةِ " .
۞۞۞۞۞۞
Qutaibatu Bn Sa'eed ya bamu labari, Laithee ya bamu labari daga Khaleed Bn Yazeed, daga Sa'eed Bn Abiy Hilaal, daga baban Ya'aquba Al-Khayyadi, yace;
" NA HALARCI SALLAH FIDRI (qaramar sallah) TARE DA MUS'AB BN ZUBAIR A GARIN MADINAH, SAI NA AIKA ZUWA GA BABAN SA'EED A TAMBAYE SHI CEWA YAYA MANZON ALLAH (S. A. W. W) YA KASANCE YANA AIKATAWA (kafin yanzu) ? SAI BABAN SA'EED YA BA SHI LABARI CEWA, " AI SHI (S. A. W. W) YA KASANCE YANA YIN SALLAH CE KAFIN KHUDUBAH, AMMA A YANZU SALLAH AKE YI KAFIN KHUDUBAH. "
(MUSNAD-AHMAD)
To, gaskiya dole ne qwaqwale su buga har ma su riqa tambayar kansu da kansu cewa me yasa ne aka cancanza ayyukan Manzon Allah (S. A. W. W) daga haqiqanin yadda yake yinsu kuma ya koyar dasu ?
Wannan kuma na daga cikin hujjojin da za ace an canza ayyukan addinin muslimci daga haqiqanin yadda aka koyar da shi kuma aka bar al'umma a kansa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
4th March, 2021/ 21st Rajab, 1442.
KU LATSA HOTON NAN DAKE DOMIN KARANTA LABARAI SAHIHAI CIKIN HARSHEN HAUSA>>>>>>>>>>>>>>>>>>
Gaskiyane
ReplyDeleteOkay
ReplyDelete