Babban Abin Kunya Ne da Ba'a Tabayi A Kasar Nan ba!!



 *“MAJAR/GAMAYYAR MALAMAI AKAN DR. ABDULJABBAR KABARA ABIN KUNYA NE DA BA’A TABA YI BA A TARIHIN KASAR NAN”*


Ina mai farawa da sunan Allah mai rusa gayyar azzalumai da munafukai, mahaliccin sammai da kassai Wanda ya kagemu da dukkan halittu baki-daya.


Tsira da aminci su kara tabbatar ga shugabanmu, maicetonmu, gatanmu a duniya da kiyama Annabi Muhammad (SAWA) da iyalan gidansa tsarkakakku.


Bayan haka, ba said na taxi da nisa ba na tabbata tun daga matashiyar wannan rubutu mai karatu zai gane inda na nufa wato “Maja/Gamayya ta malaman kano masu akidu mabanbanta akan Dr. Abduljabbar Kabara” harma da wasu malaman da bana kano ba sai na ce ‘abin kunya ne a garesu’.


Eh, tabbas! Wannan ba karamin abin kunya bane wadanda ake kira malamai suka aikata akan wannan bawan Allah. Dalili kuwa shine dukkansu basu yarda da musuluncin junansu ba suna kafirta da shirkanta junansu a masallatan da suke gabatar da karatuttuka ko ibadunsu.


Sashen Izala kowa ya sani a kasar nan su suka fara bijiro da rashin girmama manya a wa’azozinsu, tun daga Shehu Tijjani (RTA), Shehu Ibrahim Inyass (RTA), Shehu Dahiru Bauchi (H) da sauran malamai da shehunnai na Darika babu Wanda basu kafirta ba, sun yi rashin kunya wa su, sun kirasu da sunaye iri-iri ciki har da mushirikai sannan a gurinsu duk Wanda yake Darika to bautar shehunnai ko farin kyalle yake yi ma’ana dai mushiriki ne.


A tarihi bamu taba ji wani Dan Izala yayi kira akan a fito a hada kai da ‘Yan Darika ba sai dai kullum yana babatun ana raba kan al-umma, kuma shi(dan izala) shine yake da kaso mafi tsoka a cikin raba kan al-umma da yake ikirarin ana yi, domin kuwa yazo mutane suna zaune lafiya, masallici daya, makabarta daya, al-umma daya amma ya ce sai an raba , kuma ya kira duk sauran ayyuka da ibadu na addini da shirka wasu kuma ya kirasu da bidi’a. (Ga mai Neman Karin bayani akan hakan ya nemi karatun Marigayi Malam Albani Zaria Wanda ya yi akan kungiyar Izala).


Kowa ya sani a kasar nan duk Dan Darika yana yiwa Dan Izala kallon makiyin Annabi (SAWA) saboda baya yin maulidi da wasu nau’ikan na sufanci wanda a gurisa(Dan Izala) hakan bidi’a ne ko kuma shirka.


Ni a nawa tunanin ban ga dalilin da zai sa musulmi kuma mumini ya hada kai da kafiri ko mushiriki akan wani dalili ko wane iri ne, abin da yasa nace haka shine: kowane sashe kafirta dayan sashen yake amma kwatsam duk da wannan kwamacalar akan su sai muka ji wai sun hada kai sun yi mama/gamayya domin yaki da da’awar Dr Abduljabbar Kabara, sun manta da cewa ko sallah basa bin junansu, to kun ga babu aminci kenan a gayyar tasu kamar yadda naji a wani rahoto Sheikh Tijjani B. Kalarawi yana fada.


Wani shawara da tuni da zan yi ga ‘Yan mama a nan gurin shine: *Ku fara tabbatar da musuluncin junanku, ko wane sashe ya tabbatarwa dayan sashen musuluncinsa, to idan kun yi hakan kuma kowa ya gamsu sannan sai kuyi maja da hujja* ta yanda zamu samu damar karanta dala’ilu da yin salatil fatihi a masallacin Gadon Kaya.


*Abin lura*


Idan ba don akwai wata kulalliya a kasa ba me zai sa


me zaisa malaman nan su dunkule su hade kai guri guda? Kuma abin takaicin ma ko shugaba basu da shi domin babu Wanda zai yarda wani mushiriki/makiyin Annabi (SAWA) ya shugabanceshi kamar yadda suke alakantawa kawunansu.

Akwai malamin da aka yi a cikinsu Wanda ya ce “ko mafarki nayi ahlussunnah sun hada kai da ‘Yan Darika (‘Yan bidi’a) to idan na farka sai nayi astigfari” a cewarsa babu ranar da za’a samu hadin kai a tsakaninsu.

Abin da yasa wadannan malamai suka yi gungun maja kamar yadda suke fada shine: wai sun hadu su kare martabar Shugaba (SAWA), sahabbansa da kuma iyalan gidansa, sai dai kash! Karya suke gungun makaryata ne akwai akwai wani abu a kasa dalili kuwa shine: ta yaya zaku kalubalanci mutum akan maganganunshi sai Ku daddatse/yayyanke ko gutsure wasu bangarori/wurare a ciki Wanda basu wuce na ‘yan sakonni ba bayan yayi awa/sa’a ukku yanna karatu? Wannan rashin adalci ne a bayyane.

Inda suka yanke/datse wa Malam Abduljabbar gurin da yake kokarin korewa shugaba (SAWA) miyagun hadisai Wanda a cika littattafan addini da su aka jinginawa Shugaba (SAWA) Wanda a yau wasu keyin amfani dasu domin cin mutunci SHI dama ribatar wasu su bar addinin wasu kuma su fada Ilhadi(Atheism).

Gashi nan muna gani live yana faruwa a Egypt sakamakon programs da Rachit ya gabatarwa da kuma zanen batanci da Mujallar Charlie Hebdo ta kasar faransa take yi.

Malam Abduljabbar ya tashi tsaye ne matuka ainun domin ganin an cire wadannan miyagun hadisai da kazamen ruwayoyi da makiya addini suke farmana dasu, su kuma taron ‘yan maja kokarin tabbatar da wadancan miyagun hadisai suke yi da kuma jinginasu ga Annabi (SAWA), kamar yadda Dr. Ahmad Gumi da Malam Abdulwahab Dan Togo suka tabbatar da wasu daga cikin kuma suke ganin ba laifi bane. Malaman nan sun fadi abubuwa da dama masu muni ga janibin Shugaba (SAWA) kuma suna zaune lafiya saboda suna amsa sunan ahlussunnah, sannan kuma a gurinsu maruwaitan da suka ruwaito wadancan miyagun hadisai basu yi kuskure ba amma duk malamin da ya tashi tsaye yana korewa Annabi (SAWA) wadancan kazamen hadisai da ruwayoyi sai su saka shi gaba suna kafirta shi suna kiransa da sunaye iri-iri ciki har da Zindiki wai suna cewa yana taba manya/magabata, su kuma magabatan basu yi laifi ba kenan da suka ruwaito wadancan miyagun hadisai?


*Mu Auna da Hankali*


Sun ce Malam Abduljabbar ba daidai yake fassarawa ba, wasu kuma suka ce a’a kirkirowa yake yi domin cin mutunci ga Shugaba (SAWA) sun manta cewa yanzu kan mage ya waye muna karni na ashirin da daya(21st Century) lokacin da komai yake bukatar hujja gamsashshiya kafin aiwatar dashi.


Sai suka yi amfani da damar da suke da ita suka kai karansa ga gwamna sannan suka bawa gwamna guntayen/datsatstsun lakcocinsa Wanda suka yayyanke ya ji, suka yi masa sharri da kage kala-kala, sai shi kuma gwamna ya dauki matakin rufe masallacinsa da sauran wuraren da yake gudanar da harkokinsa na addini.

Daga baya sai gwamna ya saka lokaci da wuri domin yin MUKABALA tsakanin Dr. Abduljabbar da sauran malamai da suka kai kararsa wajen gwamna, kamar yadda shi malam ya bukata da a hadasu su ganar dashi domin a yi adalci ga kowane bangare.


Abin da zai Baku mamaki anan shine: tun farkon saka wannan Mukabala, Malamai ‘yan maja suka fara bijiro/fito da wasu abubuwa da alamomi na gujewa wannan zama, wani daga cikinsu ma cewa yayi bai yarda da hankali Malam Abduljabbar ba, shi a gurinsa hauka malam Abduljabbar kawai yake yi, amma ya manta lokacin da ya ce wai ‘Allah ma da kansa yana Kuna-bakin-wake’ don Allah jama’a mai gurbataccen tunani irin wannan har zai ce bai yarda da hankalin wani ba? Duk wata suffa ta hauka ta kare a gurin Wanda ya jinginawa Allah ta’addanci(Kuna-bakin-wake). Abin tambayar ma shine, shi ta yaya Allah zai yi hakan? Muna jiran amsa.

Malamai sun ta yin maganganu da kira ga gwamna domin dakile wannan zama na Mukabala amma gwamna yaki ji, hatta kungiyar Jama’atu Nasril Islam(JNI) wacce yakamata da zamewa kowane mutum da yake Nigeria Inuwa, ta soki wancan zama da gwamna ya shirya domin bawa Dr. Abduljabbar dama ya kare kansa daga Sharrin da ‘yan maja suka yi masa, hallo dai gwamna ya kauda kai yayi watsi da shawarar sarkin musulmi(JNI).


Karyar Kare Sahabbai suke, kawai suna amfani da sunan ne domin cimma wani kudiri nasu:


Da suka tabbatar babu sarki sai Allah sai suka garzaya kotu domin dakatar da Mukabala sannan suka fara yada jita-jitar cewa Dr. Abduljabbar ne ya garzaya kotu ya roki a dakatar da wannan zama, ko kunya basa ji.


Yanzu dai ta tabbata ba zasu iya zama da Malam Abduljabbar ba, kuma kowa ya gane sharri suka yi masa,domin idan har sun taki gaskiya me ya hanasu zama da shi?


A karshe zan rufe da roko zuwa ga gwamnatin jihar kano dama ta tarayyar Nigeria, tun da sun fahimci malaman nan karya suke yi to suyi masa Adalci ta hanyar bude masa santocinsa da masallatansa domin cigaba da harkokinsa na yau-da-kullum.

Ga mai hankali da tunani babu wani Abu a cikin wannan dambarwar ta malaman maja face hassada, kiyayya, da kuma tsagwaron gaba da suke nunawa a fili karara ga Malam Abduljabbar.

Kada Ku manta kasarmu Nigeria secular nation ce kuma akwai fundamental human rights, constitutional rights, da kuma Islamic rights da aka tauyewa Malam Abduljabbar Wanda zan yi bayaninsu a rubutuna na gaba.


© *A A WISDOM DAURA*

AKAFSAN(Katsina)


https://myrealaawisdomdaura.wordpress.com/2021/03/10/majar-gamayyar-malamai-akan-dr-abduljabbar-kabara-abin-kunya-ne-da-baa-taba-yi-ba-a-tarihin-kasar-nan/

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post