KAMA BASHIR DAN DAGO ZALINCINE
Da wanne dalili aka kama bashir dan dago?
Kamar yadda sukace sun kamashine sabo da ya soki wasu malamai, A Cikin Wata Wakar da Yayi Sabuwa Domin Kare Shaksiyyar Sherk Abdul-jabbar...
haba, haba haba.Shin malama izala da wasu daga darika basu taru sunci mutuncin malam Abdul-Jabbar ba shin wanne mataki hukuma ta dauka? Abin da zai kara baka mamaki shine anga wani saban salo na yadda aka rinka rera waka tacin mutunci a wannan masallaci na usman bin affan gadan kaya, bayan sun samu tabbacin cewar gwamnatin jahar kano ta amince da dakatar da mukabala, wanda tun lokacin da aka sa rana bakajin duriyarsu, wani karin ban takaici kai tsaye aka rinka yadasu, idan dan wakar da mlm bashir dan dago yayine, to suma sun rere waka tacin mutunci da zagi ga malam Abdul-Jabbar wanda ba a tabajin yayan izala da iyawa annabi yaboba amman sai gashi yan wayi gari suna rere waka ga Sahabbai a kuma masallaci, kasantuwar da ace sahabban akayiwa waka da sauki a'a cin mutuncin da ke cikin ta ya baci ga malam Abdul-Jabbar, shin me yasa hukumar jahar kano bata dauki matakiba akan su?
Na tabbata da almajiran mlm Abdul-Jabbar bane sukayi wannan taran a lokacin da sai ance yayi maganganun tunxura al'umma. Amman da ya ke su yayan mowane sunyi abin da sukaga dama, abin da masu hankali ke tambaya shine, shin anya kuwa akwai wata sauran doka akasar nan kuwa? Shin idan akwaita shin tana aiki akan kowa da kowa ko kuwa se wani bangare, gaskiyar magana hatta yan jirada bakwayiwa malam Abdul-Jabbar adalci da almajiransa wanne mataki kuka dauka lokacin da gamayar malamai sukayi cin mutunci ga malam Abdul-Jabbar? Amman yau daya daga almajiransa yayi raddi an kamashi wai ya ci anfake da cin mutuncin malamai, tooo shi dai dauri baisa araba mutumi da hikimar da allah yayimasa. Muna rokan allah yasa shigarsa kurkuku yasa hanyace ta kara haskaka kwakwalwarsa, da harshensa darajar Manzan Rahama (sawa).
©Habibu Rabiu Nasrallah