Abun Mamaki Ga 'Yan Nigeria:- Shaikh Zakzaky (h) Yayi Wannan Jawabin Da Kwana 10 Sojojin Nigeria Suka Kai Masa Hari!!



MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE

A Cikin Jawabin Shaikh Zakzaky Yake Cewa:


"Sojojin Amerika da na Isra'ila Suna nan a Kasar nan, kuma suna nan suna tattaunawa da wai Jami'an tsoron Kasar nan, wai suna kawo tsaro daga wata tsiya wai ita Boko Haram, wanda babu ita sam, su ne Boko Haram ba wani ba. 


"Maganar kwara daya ce, kisan mutane. Kisan kuma na rashin hankali. Ba kan gado, a samu dandazon mutane kawai a kashe."

 

Malam Zakzaky yace: "in kun ce Boko Haram ne me yasa kuka je kuka kashe mutane a masallacin Juma'a na Birnin Kano? Sallah Haram ne? Me yasa kuka je kasuwar sayar da wayar salula (Handset) kuka ta da bom? Shima yin waya din Haram ne? Yanzu kisa ne ake yi ko ta ko ina. A kasuwa ne, a office ne, a kanti ne, a tashan mota ne, a gida ne, a titi ne, duk kisa ake yi. Saboda haka tunda labarin kenan kisa, to gara ma kasan a kan me aka kasheka."


Shaikh Zakzaky bayyana a cikin wannan jawabin cewa: "Za a kai hari Masallaci da Cocina, Ku gaya min to ana fada da wane kenan? Da duk Addinai ko mene? Kuma za a kai hari kasuwar 'mobile' ana fada da wane? Kowa da kowa yana kasuwar mobile, kasuwar mobile na Addini ne? Kowane mai addini yana amfani da mobile anje kasuwar mobile an ta da bom. Tashan mota na wane Addini ne? Wanene za a maishe shi wawa cewa ana hare-hare ana kashe mutane kace Mana wai wani Addini ne ake yi? Wane addini? Addini sai ya zama kowa da kowa ake kashewa? Wa yace maka kuma in kana da wani ra'ayi na addini kana kashe wanda bashi da shi ne?"


Shaikh yace: "Na'am. Na san akwai wadansu mutane da ra'ayinsu yana karkata izuwa ga irin wannan. Muna musu nasiha da su shiga hankulansu, su gane cewa duk wani mutumin da yake maka da'awa na cewa dan'uwanka (mutum) koma meye addininsa kasheshi za ka yi to ba addini yake koya maka ba, don addini ba kisan kai bane. Da Annabi da yazo da addinin nan ya kashe duk mushirikan Larabawa ne da ina addinin yake? Ba yazo ya same su suna bautar Gumaka ba? To sai ya kashe su? Sai ya kira su har suka Musulunta, suka bi addini."


Dangane da Harin Bom da aka kai ma masu tattakin yankin Kano, Shaikh Zakzaky yace: "Daga bayanan da suka yi wanda yake ba mu za su ruda ba, wai Boko Haram sun ce su suka yi. Dama mun san ba wani Boko Haram. Labarin da farko ya fito daga Isra'ila ne daga nan sai Amerika, in ka duba Internet jaridun Isra'ila da Amerika da India su suke ba da labarin. Ta ina suka ji Boko Haram din yake? Ina ofishinsu a Kano? Waye Boko Haram? Ina ne head-quater sa? Ina lambar wayar Shugabansu? A ina yake? Kawai Bom muke ji. 


Ya cigaba da tambaya: "Ya aka yi kuma da zaran wata magana sai a samu Video daga Amerika in ba su suke wannan aikin ba? Duk videyoyin nan da ake yi (na Boko Haram) duk daga Amerika ake yinsu a kawo su. To, ta Allah ba tasu ba." 


Malam yace: "Ba wani dan kunan bakin wake, mutum ne suke kamawa, 'innocent' bai san hawa ba bai san sauka ba su daura mishi bom su ingizashi. To kunga ta Allah ba taku ba sai ya zama sanadiyyar wannan ne ma mutane suka bumbunto, sai ga Taron da muke gani (Na Arbaeen), Kuma Insha Allahul Azeem kun dunga ganin wannan Taron kenan." 


Malam Zakzaky yace: "To sai suka dawo suna cewa to za su kai (mana wani) harin, suna hankoron ranar karshe ne, in ana shigowa (Zaria) za su aiko da masu Boma-bomai, jiya na ba da labarin yadda suka ce za su yi har da za su samu jarka sai su saka bom a ciki sai su aje a gefen hanya alhali Bom ne, sai su matsa 'remote' in ana wucewa. To kuma jiya naji wani labarin da suka ce, in har Taron ma an yi shi 'succesfully' to in za a koma za su sakama wadanda suke komawa gida bom. Kuma wannan wanda ya gaya mana Soja ne mai 'Uniform', dan a wajensu aka yi 'meeting' din aka ce za a yi hakan. 'Which means' mun san waye yake saka bom din. Don a hanyar Kano ma an gansu da uniform dinsu suna haka rami. To bara ma sun daddasa a hanyar Kaduna, sai aka kakkauce ma wuraren da suka daddasa din, har aka iso."


__________


Maganganun da Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yi a wannan ranar suna da yawa. Inda ya bayyana duk kullin Jami'an tsoron Kasar nan na shekar da jini bisa Umarnin Amurka da Isra'ila. Wanda kuma bayan wannan jawabin da kwana 10 daidai ne Sojojin Nigeria suka zabi su Afkama Shaikh Zakzaky da almajiransa tunda sun ga Bom din da suke saka Mana da sunan Boko Haram mun san ba wani Boko Haram sai su.

.

FREE SAYYID ZAKZAKY.H.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post