Abinda Yafi Tayar Mun Da Hankali a Kurkuku!_ Inji Falalu Hassan Shinkafi


Mlm Falalu Yana Daya Daga Cikin Mutanen da Akakama a Garin Shinkafi akan Tuhumar su da Jagorantar zanga-Zangar Kwatar yancin Kai, game da Dauki Dai-Dai da Yan Kidnapped keyi Mana a Garin Shinkafi,


Mlm Falalu ya Rubuta a kafar Sada Zumunta ta Facebook yau 25-mar Yake Cewa"


 Duk da Zamana a kurkuku gajeren lokaci ne,amma nayi karatu wanda kimarsa to gaskiya karatun shekaru ne! Naga abubuwa da daman gaske.Tabbas gidan yari gida ne na karatu kuma makaranta ce mai cin gashin kanta wanda mutum ka shiga yayi abinda zai kaishi ko bai yi ba.


Nasan wadanda ke biye da ni sun zaqu su ji miye yafi tayar mun da hankali a Kurkuku? 


Abinda yafi tayar mun da hankali a Kurkuku daya ne,wanda a halin yanzu da nake a waje bisa umurnin Ubangijin da yayi mun wannan jarabawa a lokacin da ya tsara kuma ya kawo karshenta a lokacin da ya tsara,idan na tuna abun wallahi sai naji rayuwata tayi kunci!


Abinda yafi tayar mun da hankali shi ne; irin yanda naga gurguzun yara matasa daure a gidan yari! Yaran da kowace al'umma ke hankoron samu domin dogaro da su wajen ci gabanta! Yaran da ya dace su kasance abin alfaharim al'umma! Domin babu wata al'umma a tarihi wadda ta ci gaba ba tare da matasa ba! Matasa sune ginshikin ci gaban kowace al'umma.


Abu mafi muni mafi tashin hankali shi ne,idan kayi magana da goma daga cikinsu zaka taras takwas ko tara duk basuyi nadamar abinda suka aikata ba! Kurkuku ta kasance tamkar gida a wajensu.Wani zakaji yazo kurkuku sau hudu,biyar,shidda kai wani ma har tara! Kai akwai wanda ma na taras ban jima ba ya samu mafita,amma abin ban takaici kafin na samu mafita sai da ya sake aikata wani laifin da ya maido shi a kurkuku.


Nayi nazari iya nazari akan wadanda laifuka ne ke kawo su a kurkuku? Bisa gaskiyar magana abubuwa hudu ne suka fi kai matasa kurkuku a yau!


( 1)  Sata

( 2 )  Luwadi

( 3 ) Fyade

( 4 ) Shaye-Shaye


Wannan ne ya tilasta mun yin rubuce-rubuce akan wadannan matsaloli. A rubutuna nayi kokarin tattaunawa kai tsaye da matasan wadanda wadannan laifuka uku suka Kai a kurkuku. Nayi kokarin zaqulo babban makasudin aikata wadannan laifuka!


Bayan sanin makasudin aikata wadannan laifuka,sai na karkata alqalamina wajen rawar da iyaye ya dace su taka wajen tarbiyar 'yayansu wanda akwai sakacinsu sosai wajen lalacewar 'yayansu,rawar da gwamnati ya dace ta taka wajen daqile wannan munanan ayukku wanda itama gwamnati tana da sakaci fiye da sakacin iyaye kamar yanda bincikena ya tabbatar! Daga karshe kuma wace rawa ita al'umma ya dace ta taka wajen diqile wadannan laifuka domin a wani janibi akwai rawar al'umma kanta  wajen aikata wadannan laifuka.


Ina gab da kammala wannan rubutu sai Ubangiji ya kawo mafita bisa ganin damarsa! Amma Alhamdulillah duk abinda nake son na samu akan wannan bincike na same shi,kuma ina kan kammala rubutun yanzu haka Insha Allah.


Da zarar na kammala Insha Allah zanci gaba da wallafa shi a shafi na lokaci bayan lokaci domin amfanuwar al'umma da kuma daukar matakan da suka dace wajen ganin mun samu matasa na gari wadanda zasu zamo abin alfaharinmu.


SAI KUN JI DAGA GARENI!

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post