​Zarif: Amurka Na Fuskantar Manyan Matsaloli Na Cikin Gida Wadanda Trump Ya Haifar Musu


 

2021-02-06


Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, gwamnatin Joe Biden tana fuskantar mayan matsaloli a cikin gida wadanda Donald Trump ya haifar musu.

Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, ba su adawa da komawar Amurka a cikin yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, amma kuma a lokaci guda yanzu Amurka tana fuskantar manyan matsaloli a cikin gida wadanda Trump ya haifar musu.


Ya ce, idan Amurka ta dawo cikin yarjejeniyar abu ne mai kyau gare ta, kuma wannan shi ne abin da ya kamata ta fara yi, kafin neman Iran ta yi watsi da matakan da ta dauka, na jingine yin aiki da wasu bangarorin yarjejeniyar, saboda ficewar Amurka da kuma saba alkwulla daga bangaren kasashen tarayyar turai.


Dangane da alaka tsakanin Iran da Saudiyya kuwa, Zarif ya bayyana cewa a kowane lokaci Iran tana maraba da duk wani mataki na kyautata alaka tsakaninta da Saudiyya, domin hakan abu ne da zai amfanar da al’ummomin yankin da ma musulmi na duniya baki daya.


Zarif ya ce a lokuta daban-daban Iran din ta sha mika goron gayyata ga Saudiyya domin tattaunawa, ta yadda za a iya warware matsaloli da dama ta hanyar fahimtar juna, amma hakan bai yiwuwa cikin sauki ba, kasantuwar gwamnatin Saudiyya tana karbar umarni ne daga Washington kafin aiwatar da duk wani lamari da ya shafi siyasar gabas ta tsakiya.


HAUSA TV

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post