Yadda auren Sayyidah Fatima Zahra (A.S) ya kasance !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


ALLAH NE WALIYYINTA, JIBRILU KUMA MAI MAGANA 


Dole ya kasance masu neman auren Sayyidah Zahra (S. A. W. W) a doron qasa su rasa ta, domin aurenta an dauro shi ne a sama bisa Waliccin Allah (T) .


Manya daga cikin Sahabbai sun nemi aurenta amma basu samu ba sakamakon ita (S. A) ba abokiyar hadin kowa bace, ita Siddiqa ce kuma babu mai aurenta sai Siddiqi. 


An kawo yadda aka yi aurenta (S. A) kamar haka;


Daga Jabir Bn Samrata yace, Manzon Allah (S. A. W. W) yace, 


" YAA KU MUTANE, WANNAN SHINE ALIYU BN ABIY 'DALIB, KU KUMA KUNA RIYAWA CEWA NI NA AURAR MASA DA 'YATA FADIMATU. HAQIQA MADAUKAKAN QURAISHAWA (a shekaru da dukiya) SUN NEMI AURENTA A WAJENA AMMA BAN AMSAWA KOWANNENSU INA SAURARON LABARI DAGA SAMA (kan wannan buqatu naku), HAR SAI DA JABRA'ILU YAZO MIN A DAREN 24 NA WATAN RAMADANA YACE; 


" YAA MUHAMMAD ! MADAUKAKIN DA YAFI KOWA 'DAUKAKA YANA MIQA MAKA GAISUWA. HAQIQA YA TARA RUHANAI DA KUMA MANYAN MALA'IKU CIKIN WANI TAFKI WANDA AKE KIRANSA AFYAHU A QARQASHIN WATA BUSHIYAR 🌲'DUBA (wacce aka tsinko 'ya'yata aka bawa Manzon Allah yayin Mi'irajinsa wanda ya zama nudufa na samuwar Sayyidah Zahra ) YA AURARWA ALIYU FADIMATU, KUMA YA UMARCE NI. 


NA KASANCE (nine) MAI MAGANA (yayin qulla auren) ALLAH KUMA WALIYYI. KUMA YA UMARCI BISHIYAR 🌲 'DUBA DA TA 'DAUKU ADO (to be very ornament ) SAI KUWA TA 'DAU ADO (it became ornamented) DA DURR DA KUMA YAQUTU, SA'AN NAN YA WATSA SHI. KUMA YA UMARCI HURUL-EEN (matan Aljannah) SUKA TARU SUKA YI BIKI, KUMA SUNE ZA SUYI TA SHIRYAR DASHI (bikin) HAR ZUWA RANAR ALQIYAMA, KUMA SUCE, " WANNAN SHINE GARAR FADIMATU ."


عَنْ جَابِرِ بْنِ سَمُرَةَ قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏ أَيُّهَا النَّاسُ هَذَا عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبٍ وَ أَنْتُمْ تَزْعُمُونَ أَنِّي أَنَا زَوَّجْتُهُ ابْنَتِي فَاطِمَةَ وَ لَقَدْ خَطَبَهَا إِلَيَّ أَشْرَافُ قُرَيْشٍ فَلَمْ أُجِبْ كُلَّ ذَلِكَ أَتَوَقَّعُ الْخَبَرَ مِنَ السَّمَاءِ حَتَّى جَاءَنِي جَبْرَئِيلُ لَيْلَةَ أَرْبَعٍ وَ عِشْرِينَ مِنْ شَهْرِ رَمَضَانَ فَقَالَ يَا مُحَمَّدُ الْعَلِيُّ الْأَعْلَى يَقْرَأُ عَلَيْكَ السَّلَامَ وَ قَدْ جَمَعَ الرُّوحَانِيِّينَ وَ الْكَرُوبِيِّينَ فِي وَادٍ يُقَالُ لَهُ الْأَفْيَحُ تَحْتَ شَجَرَةِ طُوبَى وَ زَوَّجَ فَاطِمَةَ عَلِيّاً وَ أَمَرَنِي فَكُنْتُ الْخَاطِبَ وَ اللَّهُ تَعَالَى الْوَلِيَّ وَ أَمَرَ شَجَرَةَ طُوبَى فَحَمَلَتِ الْحُلِيَّ وَ الْحُلَلَ وَ الدُّرَّ وَ الْيَاقُوتَ ثُمَّ نَثَرَتْهُ وَ أَمَرَ الْحُورَ الْعِينَ فَاجْتَمَعْنَ فَلَقَطْنَ فَهُنَّ يَتَهَادَيْنَهُ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ وَ يَقُلْنَ هَذَا نُثَارُ فَاطِمَةَ.


Daga Ja'afar Bn Muhammad (A. S) yace; 


" ALIYU YA AURI FADIMATU NE A WATAN RAMADAN, KUMA YA TARE DA ITA A WATAN ZUL-HIJJAH A SHEKARA TA BIYU BAYAN HIJRA ."


عَنْ جَعْفَرِ بْنِ مُحَمَّدٍ ع قَالَ: تَزَوَّجَ عَلِيٌّ فَاطِمَةَ فِي شَهْرِ رَمَضَانَ وَ بَنَى بِهَا فِي ذِي الْحِجَّةِ مِنَ السَّنَةِ الثَّانِيَةِ مِنَ الْهِجْرَةِ.



Sai dai a wata riwayar ance ya tare da ita na ranar alamis 21 ga Muharram shekara ta 3 bayan Hijra. 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


، عيون أخبار الرضا عليه السلام بِالْأَسَانِيدِ الثَّلَاثَةِ عَنِ الرِّضَا عَنْ آبَائِهِ ع قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏ أَتَانِي مَلَكٌ فَقَالَ يَا مُحَمَّدُ إِنَّ اللَّهَ يَقْرَأُ عَلَيْكَ السَّلَامَ وَ يَقُولُ لَكَ قَد زَوَّجْتُ فَاطِمَةَ مِنْ عَلِيٍّ فَزَوِّجْهَا مِنْهُ وَ قَدْ أَمَرْتُ شَجَرَةَ طُوبَى أَنْ تَحْمِلَ الدُّرَّ وَ الْيَاقُوتَ وَ الْمَرْجَانَ وَ إِنَّ أَهْلَ السَّمَاءِ قَدْ فَرِحُوا لِذَلِكَ وَ سَيُولَدُ مِنْهَا وَلَدَانِ سَيِّدَا شَبَابِ أَهْلِ الْجَنَّةِ وَ بِهِمَا يُزَيَّنُ أَهْلُ الْجَنَّةِ فَأَبْشِرْ يَا مُحَمَّدُ فَإِنَّكَ خَيْرُ الْأَوَّلِينَ وَ الْآخِرِينَ.


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏43، ص: 106



Yazo cikin Uyunil-Akbaar na Ridha da isnadai guda uku, daga Imam Ridha daga iyayensa (A. S) yace, Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" MALA'IKA YA ZO MIN YACE, " YAA MUHAMMAD! LALLE ALLAH NA MIQA MAKA GAISUWA KUMA YANA CE MAKA LALLE FA YA AURARWA ALIYU FADIMATU, KAIMA KA AURAR MAR (a doron qasa), KUMA LALLE YA UMARCI BISHIYAR 'DUBA DA TA 'DAU ADO NA YAQUTU DA MURJANI, KUMA HAQIQA HALITTUN SAMA SUNYI FARIN CIKI DA HAKA. SANNAN KUMA ZAI HAIFI 'YA'YA BIYU DAGA GARE TA SHUGABANNIN SAMARIN ALJANNAH, KUMA DA SU NE ZAI QAWATA 'YAN ALJANNAH. KAYI BUSHARA YAA MUHAMMAD, DOMIN KAINE MAFI ALKHAIRIN NA FARKO DANA QARSHE. "



 عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ سَمِعْتُهُ يَقُولُ‏ لَوْ لَا أَنَّ اللَّهَ خَلَقَ أَمِيرَ الْمُؤْمِنِينَ لِفَاطِمَةَ مَا كَانَ لَهَا كُفْوٌ عَلَى الْأَرْضِ.


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏43، ص: 98


Daga Abu Abdullahi (A. S) yace, " Na ji shi yana cewa, " DA BA DON ALLAH YA HALICCI SHUGABAN MUMINAI (ALI) GA FADIMA BA, TO, DA KUWA BATA DA ABOKIN HADI A DORON QASA ."


MADALLA DA WANNAN AURE MAI ALBARKA 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


       (08137925034)


7th February, 2021/ 25th Jimada-Saaniy, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post