@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
MAI HANKALI BA YA BADA LABARI GA WANDA YAKE JIN TSORON ZAI QARYATA SHI
A ko da yaushe shi mai hankali ya kanyi aiki da hankalinsa cikin komai nasa, domin ba ya furuci ko aiki ba tare da yayi nazarin abinda zai iya biyowa baya ba.
Ita magana ana yinta ne a inda za tayi amfani ga wanda ya ji ta ko kuma ta amfanar da mai yinta. Domin akwai maganar da kan iya zama sharri, wata kuma kan iya zama khairi ga mai yinta da ma al'umma baki daya.
Babu laifi ko kuma ba za ace rashin hankali bane ka bada labari ga wanda kasan yana qaryata ka ko zai iya qaryata ka in dai har shine ya tambaye ka, domin za ka iya tunani wataqila ko halinsa ya canza zuwa karbar gaskiya.
Ya zo cikin wasiyyar tasa (A. S) yana cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
يَا هِشَامُ إِنَّ الْعَاقِلَ لَا يُحَدِّثُ مَنْ يَخَافُ تَكْذِيبَهُ وَ لَا يَسْأَلُ مَنْ يَخَافُ مَنْعَهُ وَ لَا يَعِدُ مَا لَا يَقْدِرُ عَلَيْهِ وَ لَا يَرْجُو مَا يُعَنَّفُ بِرَجَائِهِ وَ لَا يَتَقَدَّمُ عَلَى مَا يَخَافُ الْعَجْزَ عَنْهُ وَ كَانَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ع يُوصِي أَصْحَابَهُ يَقُولُ أُوصِيكُمْ بِالْخَشْيَةِ مِنَ اللَّهِ فِي السِّرِّ وَ الْعَلَانِيَةِ وَ الْعَدْلِ فِي الرِّضَا وَ الْغَضَبِ وَ الِاكْتِسَابِ فِي الْفَقْرِ وَ الْغِنَى وَ أَنْ تَصِلُوا مَنْ قَطَعَكُمْ وَ تَعْفُوا عَمَّنْ ظَلَمَكُمْ وَ تَعْطِفُوا عَلَى مَنْ حَرَمَكُمْ وَ لْيَكُنْ نَظَرُكُمْ عَبَراً وَ صَمْتُكُمْ فِكْراً وَ قَوْلُكُمْ ذِكْراً وَ إِيَّاكُمْ وَ الْبُخْلَ وَ عَلَيْكُمْ بِالسَّخَاءِ فَإِنَّهُ لَا يَدْخُلُ الْجَنَّةَ بَخِيلٌ وَ لَا يَدْخُلُ النَّارَ سَخِيٌّ.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج1، ص: 142
" YAA HISHAAM ! LALLE MAI HANKALI BA YA BADA LABARI GA WANDA YAKE JIN TSORON ZAI IYA QARYATA SHI , KUMA BA YA ROQON WANDA YAKE JIN TSORON ZAI IYA HANA SHI, SANNAN BA YA ALQAWARI KAN ABINDA YASAN BA YA DA IKO A KANSA, ..........KUMA BA YA GABATA AKAN ABINDA YAKE JIN TSORON GAZAWA A KANSA.
SHUGABAN MUMINAI (A. S) YA KASANCE YANA YIWA SAHABBANSA WASIYYA YANA CEWA, " INA YI MUKU WASIYYA DA TSORON ALLAH A BOYE DA BAYYANE, DA KUMA YIN ADALCI CIKIN YARDA (halin walwala) DA KUMA (halin) FUSHI, DA YIN AIKI (neman halal) CIKIN HALIN TALAUCI DA WADATA, DA KUMA SADAR DA (zumuncin) WANDA YA YANKE MUKU, KUMA KU YAFEWA WANDA YA ZALUNCE KU, KUMA KU TAUSAYAWA WANDA YA HARAMTA MUKU, KALLONKU KUMA YA ZAMA HANGE (mai kyau), SHIRINKU (your silence) KUMA YA ZAMA TUNANI, KUMA MAGANARKU TA ZAMA AMBATO (Allah's remembrance) .
SANNAN KUMA NA HANE KU DA YIN ROWA, KUMA NA HORE KU DA YIN KYAUTA, DOMIN SHI MAROWACI BA ZAI SHIGA ALJANNAH BA, KUMA MAI KYAUTA BA ZAI SHIGA WUTA BA. "
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(13th February, 2021/ 2nd Rajab, 1442.
#FREE OUR LEADER SAYYID ZAKZAKY (H) !!!