Wasiyyar Imam Musa Bn Ja'afar (A.S) ga Hishaam Bn Hakaam cikin ayoyin Alqur'ani (2)


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


MALAMAN WANNAN ZAMANI KOYI SUKE DA KAFIRAN FARKO


'Dabi'a ce ta kafiran farko ko da sun ji gaskiya ko sun ganta ba za su bita ba sai dai subi irin abinda kakanninsu suka doru a kansa na kafirci, karbar gaskiya kuma ta zama wani sabon al'amari. 


To, mafi yawan malaman wannan zamani na yanzu da almajiransu sunfi gamsuwa da bin abinda Yahudawa ko Wahabiyawa suka tsara musu, idan wani yazo musu da gaskiya ba za su karbeta daga gare shi ba domin gaskiyar bata zo daga inda suke so ba.


Sun fi gamsuwa da bin qarya wacce aka gina su a kanta, da kuma yin fada da masu qoqarin bayyanar da gaskiyar. 


Ya zo cikin wasiyyar Imam Musa Bn Ja'afar (A. S) ga Hishaam Bn Hakaam yake ce masa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" Yaa Hishaam ! Sa'an nan (Allah) yayi wa'azi ga ma'abota hankali kuma ya kwadaitarsu game da lahira yace; 


" KUMA ITA RAYUWAR DUNIYA BATA KASANCE BA FACE (wani dan) WASA DA WARGI (wanda ke qarewa), KUMA GIDAN LAHIRA SHINE MAFI ALKHAIRI GA WADANDA SUKA YI TAQAWA, YANZU BA ZA KU HANKALTA BA ?"


Kuma yace; " KUMA ABINDA AKA ZO MUKU (da shi) DAGA WANI ABU (na arziqi ko qyalqyali ) 'DAN JIN DADI NE NA RAYUWAR DUNIYA DA KUMA ADONTA, KUMA ABINDA KE WAJEN ALLAH (wanda ya tanadar muku) YAFI ALKHAIRI (gare ku) DA KUMA WANZUWA, ASHE BA ZA KU HANKALTA (daga irin wadannan bayanan) BA? 


7 يَا هِشَامُ ثُمَّ وَعَظَ أَهْلَ الْعَقْلِ وَ رَغَّبَهُمْ فِي الْآخِرَةِ فَقَالَ‏ وَ مَا الْحَياةُ الدُّنْيا إِلَّا لَعِبٌ وَ لَهْوٌ وَ لَلدَّارُ الْآخِرَةُ خَيْرٌ لِلَّذِينَ يَتَّقُونَ أَ فَلا تَعْقِلُونَ‏[64] 


وَ قَالَ‏ وَ ما أُوتِيتُمْ مِنْ شَيْ‏ءٍ فَمَتاعُ الْحَياةِ الدُّنْيا وَ زِينَتُها وَ ما عِنْدَ اللَّهِ خَيْرٌ وَ أَبْقى‏ أَ فَلا تَعْقِلُونَ‏[65]


" Yaa Hishaam ! Sa'an nan (Allah) ya tsoratar da wadanda ba sa hankaltuwa (daga dukkan wasu misalai ko ayoyin da ake nuna musu) daga azaba, yace; 


" SA'AN NAN MUKA DARKAKE (halakar) DA WASU (mutane) NA DABAM (sakamakon kafircewarsu). KUMA LALLE KU (ai) KUNA SHUDEWA A KANSU (cikin halin tafiye-tafiyenku) KUNA MASU ASUBANCI. DA KUMA DARE, (amma duk da irin wadannan ayoyi da kuke gani) BA ZA KU HANKALTA BA ?"


7 يَا هِشَامُ ثُمَّ خَوَّفَ الَّذِينَ لَا يَعْقِلُونَ عَذَابَهُ فَقَالَ‏ ثُمَّ دَمَّرْنَا الْآخَرِينَ وَ إِنَّكُمْ لَتَمُرُّونَ عَلَيْهِمْ مُصْبِحِينَ وَ بِاللَّيْلِ أَ فَلا تَعْقِلُونَ‏[66


" Yaa Hishaam ! Sa'an nan (Allah) ya bayyana cewa lalle shi hankali tare da ilimi yake. Yace; 


" WADANCAN MISALAI NE MUKE BUGA SU GA MUTANE, AMMA BABU MAI HANKALTARSU SAI MASU ILIMI. "


(shi yasa kuke ganin mutane da yawa basa gane gaskiya komai bayyanarta sakamakon rashin ilimi na haqiqa da suka rasa ).


Yaa Hishaam! Sa'an nan (Allah) ya zargi wadanda basu da hankalin (sauraren magana da bin mafi kyawu daga gare ta) yace; 


" KUMA IDAN AKACE MUSU, " KUBI ABINDA ALLAH YA SAUKAR (na gaskiya) SAI SUCE, " A'A, MU DAI ZA MUBI ABINDA MUKA TARAR DA IYAYENMU A KANSA NE (na bata da bin son zuciya). (Allah yake tambayarsu da cewa ), " ASHE KO DA ACE IYAYEN NASU BASA FAHINTAR KOMAI (na gaskiya) KUMA BA SA SHIRIYA ?"


(Kamar dai yadda wasu ke cewa duk abinda Sahabbai suka yi daidai ne don sun rayu da Manzon Allah, kenan ko da sunci amanar Manzon Allah)? 


Allah (T) ya qara cewa, 


" LALLE MAFI SHARRIN DABBOBI A WAJEN ALLAH SUNE KURAME (daga jin gaskiya) BEBAYEN DA BASA FAHINTA (mahaukata).


(Irin wadannan malaman kenan masu fifita wasu kan Annabi (S. A. W. W)). 


 Kuma yace, 


" KUMA DA ZA KA TAMBAYE SU (cewa) WANENE YA HALICCI SAMMAI DA QASA ZA SUCE MAKA ALLAH NE, TO, KACE GODIYA TA TABBATA GA ALLAH. A'A, MAFI YAWANSU BA SA HANKALTA (daga irin wadannan misalai da ake basu ). "


Sa'an nan kuma ya zargi yawa (daga taron mutane) yace; 


" KUMA LALLE IDAN KABI MAFI YAWA DAGA WADANDA KE CIKIN QASA ZA SU BATAR DA KAI DAGA TAFARKIN ALLAH. "


(ma'ana yawan JAMA'ARTA kan abu ba shine ma'auni na gane shiriya ba). 


Kuma yace, 


" MAFI YAWAN MUTANE BASA SANIN (gaskiya sai dai shirme) KUMA MAFI YAWANSU BA SA SAKANKANCEWA. 


7 يَا هِشَامُ ثُمَّ بَيَّنَ أَنَّ الْعَقْلَ مَعَ الْعِلْمِ فَقَالَ‏ وَ تِلْكَ الْأَمْثالُ نَضْرِبُها لِلنَّاسِ وَ ما يَعْقِلُها إِلَّا الْعالِمُونَ‏[68] 


يَا هِشَامُ ثُمَّ ذَمَّ الَّذِينَ لَا يَعْقِلُونَ فَقَالَ‏ وَ إِذا قِيلَ لَهُمُ اتَّبِعُوا ما أَنْزَلَ اللَّهُ قالُوا بَلْ نَتَّبِعُ ما أَلْفَيْنا عَلَيْهِ آباءَنا أَ وَ لَوْ كانَ آباؤُهُمْ لا يَعْقِلُونَ شَيْئاً وَ لا يَهْتَدُونَ‏[69]


 وَ قَالَ تَعَالَى‏ إِنَّ شَرَّ الدَّوَابِّ عِنْدَ اللَّهِ الصُّمُّ الْبُكْمُ الَّذِينَ لا يَعْقِلُونَ‏[70] 


وَ قَالَ‏ وَ لَئِنْ سَأَلْتَهُمْ مَنْ خَلَقَ السَّماواتِ وَ الْأَرْضَ لَيَقُولُنَّ اللَّهُ قُلِ الْحَمْدُ لِلَّهِ بَلْ أَكْثَرُهُمْ‏ لَا يَعْقِلُونَ‏[71]


 ثُمَّ ذَمَّ الْكَثْرَةَ فَقَالَ‏ وَ إِنْ تُطِعْ أَكْثَرَ مَنْ فِي الْأَرْضِ يُضِلُّوكَ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ‏[72] 


وَ قَالَ‏ أَكْثَرَ النَّاسِ لا يَعْلَمُونَ‏ وَ أَكْثَرُهُمْ لَا يَشْعُرُونَ.


(1) الأنعام: 32.


(2) القصص: 60.


(3) الصافّات: 136، 137، 138.


(4) بفتح السين المهملة: قرية قوم لوط.


(5) العنكبوت: 42.


(6) البقرة: 170.


 


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏1، ص: 135



YAA ALLAH KA QARA MANA SHIRIYA DA KUMA BIN TA. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


       (08137925034)


12th February, 2021/ 30th Jimada-Saaniy, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post