WANENE ZAID BN AMRUU BN NUFAIL ???

 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


SAHABIN DA YAFI ANNAFI (S. A. W. W)  IMANI IN JI BUKHARI 


Tabbas, idan ka kira malaman MAJA da suna KAFIRAI kayi daidai kuma babu wani laifi a kanka na cewa ka kafirta musulmai, domin musulmin kirki shine ke ganin fifikon Annabi (S. A. W. W) akan kowa. 


Ko kadan wadannan malamai basu ma san Annabi (S. A. W. W) ba ballantana ace sun san darajarsa, shi yasa suke gani tare da yin imani cewa akwai wani wanda ya fi shi imani (S. A. W. W). 


Ba tare da bata lokaci ba za mu kawo wasu riwayoyi cikin SAHIHUL-BUKHARI masu nuna cewa akwai wanda yafi Manzon Allah (S. A. W. W) imani daga cikin Sahabbansa. Ga riwayar nan kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


66-فضائل أصحاب النبي - صلى الله عليه وسلم



حديث زيد بن عمرو بن نفيل



(3826)- حدثني محمد بن أبي بكر: حدثنا فضيل بن سليمان: حدثنا موسى بن عقبة: حدثنا سالم بن عبد الله، عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما: 

أن النبي صلى الله عليه وسلم لقي زيد بن عمرو بن نفيل بأسفل بلدح، قبل أن ينزل على النبي صلى الله عليه وسلم الوحي، فقدمت إلى النبي صلى الله عليه وسلم سفرة، فأبى أن يأكل منها، ثم قال زيد: إني لست آكل مما تذبحون على أنصابكم، ولاآكل إلا ما ذكر اسم الله عليه وأن زيد بن عمرو كان يعيب على قريش ذبائحهم، ويقول: الشاة خلقها الله، وأنزل لها من السماء الماء، وأنبت لها من الأرض، ثم تذبحونها على غير اسم الله إنكارا لذلك وإعظاما له .


Muhammad Bn Abubakar ya bamu labari, Fudhail Bn Sulaiman ya bamu labari, Musa Bn Uqbata ya bamu labari, Saleem Bn Abdullahi ya bamu labari daga Abdullahi Bn Amruu, Lalle Annabi (S. A.W.W) ya hadu da Zaid Bn Amruu Bn Nufail a ASFALU BALDAHA kafin a saukarwa Annabi (S.A.W.W) wahayi, sai Annabi ya miqa masa wani qunshi (da aka nannade wani abu), sai (Zaid) ya qi yaci daga gare shi, sa'an nan Zaid yace; 


" NI BANA CI DAGA ABINDA KUKA YANKA AKAN GUMAKANKU, KUMA BANA CI FACE ABINDA AKA AMBACI SUNAN ALLAH A KANSA  ."


Zaid Bn Amruu Bn Nufail ya kasance yana zargi akan yakan Quraishawa yana cewa; 


" ITA AKUYA ALLAH NE YA HALICCETA KUMA YA SAUKAR MATA DA RUWANTA DAGA SAMA, SANNAN YA TSIRAR MATA (da abinci) DAGA QASA SANNAN SU (Quraishawa) SUKE YANKA TA DA SUNAN WANIN ALLAH  ." Yana inkarin hakan da kuma girmamawa gare Shi.


(BUKHARI, HADISI MAI LAMBA 3826)


Wannan hadisi na nuna mana ne cewa Zaid Bn Amruu Bn Nufail ya fi Annabi (S. A. W. W) imani  tunda har zai qi karbar Nama daga hannunsa bisa zargin wai ba sa yankawa da sunan Allah. 


           NUSARWA 


Idan kuka koma cikin (Arabic text) na hadisi za kuga sun so juya ma'anar hadisin yadda suka so nuna kamar Annabi (S. A. W. W) ne ya miqawa Zaid Naman, amma kuma bayanin da ke gaba sai ya tabbatar mana da cewa Annabi (S. A. W. W) ne ya miqawa Zaid. 


Idan kun kasa fahinta ku qara biyo mu cikin hadisin da ke biye, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


16- ما ذبح على النصب والأصنام


5499 - حدثنا معلَّى بن أسد: حدثنا عبد العزيز يعني ابن المختار: أخبرنا موسى بن عقبة قال: أخبرني سالم: أنه سمع عبد الله يحدث، عن رسول الله صلى الله عليه وسلم: 

أنه لقي زيد بن عمرو بن نُفَيل بأسفل بَلْدَحَ، وذاك قبل أن يُنزل على رسول الله صلى الله عليه وسلم الوحي، فقُدِّم إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم سفرة فيها لحم، فأبى أن يأكل منها، ثم قال: إني لا آكل مما تذبحون على أنصابكم، ولا آكل إلا مما ذُكر اسم الله عليه .


Mu'allah Bn Asad ya bamu labari, Abdul-Azeez ya bamu labari, yana nufin Ibn Mukhtar, Musa Bn Uqbata ya bamu labari yace, Saleem ya bani labari cewa ya ji Abdullahi yana bada labari daga Manzon Allah (S. A. W. W) cewa Shi ya hadu da Zaid Bn Amruu Bn Nufail a ASFALI BALDAHA, hakan kuwa kafin a saukar da Wahayi ne akan Manzon Allah (S. A. W. W) , sai Manzon Allah (S. A. W.W) ya miqa masa wani qunshi dake da Nama a cikinsa, sai ya qi yaci. Sa'an nan yace;


" NI BANA CI DAGA ABINDA KUKA YANKA KAN GUMAKANKU, BANA CI FACE DAGA ABINDA AKA AMBACI SUNAN ALLAH A KANSA  ."


Shi ma wannan hadisi an juya maganar, domin cikinsa za kuga an ce " FAQUDDIMA ILAH RASULUL-LAHI SAFRATAN FEEHA LAHMAN " wanda ke nufin, " sai ya miqawa Annabi wani qunshi da Nama a ciki. "


In da hakane sai ace ba Annabi (S.A.W.W) ne ya miqawa Zaid ba,  Zaidu ne ya miqawa Annabi (S. A. W. W). Tabbas canzawa akayi, amma dan Allah duk wanda ke da SAHIHUL-BUKHARI ya dauka ya duba hadisi mai lamba 5499 zai ga cikin hadisin an rubuta  " FAQADDAMA ILAIHI RASULULLAHI SAFRATAN FEEHA LAHMAN  " Sai Annabi (S. A. W.W) ya miqa masa..... 



Idan ma kanku ya rude kuyi nazari mana, ai maganar an kawota ne kan Falalar Sahabbai wanda ake son nuna falalar Zaid. In da Annabi (S.A.W.W) ya qi cin naman da ba za a kawo cikin falalar Zaid Bn Amruu Bn Nufail ba. 


Ku qara biyo mu cikin hadisi dake qasa za ku qara gamsuwa insha Allah. 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼




[3828- وقال الليث: كتب إلي هشام، عن أبيه، عن أسماء بنت أبي بكر رضي الله عنهما قالت: رأيت زيد بن عمرو بن نفيل قائما، مسندا ظهره إلى الكعبة، يقول: يا معاشر قريش، والله ما منكم على دين إبراهيم غيري وكان يحيي الموءودة، يقول للرجل إذا أراد أن يقتل ابنته: لا تقتلها، أنا أكفيكها مؤونتها، فيأخذها، فإذا ترعرعت، قال لأبيها: إن شئت دفعتها إليك، وإن شئت كفيتك مؤونتها


Laithee yace, Hishaam ya rubuto zuwa gare ni, daga babansa, daga Asma'u Bnt Abubakar tace, " Na ga  Zaid Bn Amruu Bn Nufail a tsaye ya jingina gadon bayansa a jikin Ka'abah yana cewa; 


" YAA KU TARON QURAISHAWA  !  WALLAHI KAF CIKINKU BABU WANDA KE KAN ADDININ IBRAHIM IN BA NI BA   !"


(Tace), ya kasance yana rayar da wadanda ake bisne su da ransu , yana fadawa mutum idan yayi nufin bisne 'yarsa; 


" KADA KA KASHE TA, NI ZAN 'DAUKE MAKA 'DAWAINIYARTA. "


Sai ya karbe ta (in ji Asma'u), yayin da ta sami nutsuwa a wajensa sai ya cewa babanta; 


" IDAN KANA SO SAI NA MAYAR MAKA DA 'YARKA GARE KA, IDAN KUMA KASO SAI NA 'DAUKE MAKA 'DAWAINIYARTA. "


Kunga wannan furuci da aka ce ya fada cewa kaf cikin Quraishawa babu wanda ke kan addinin Ibrahim in ba shi ba na nuna cewa har da Annabi (S. A. W. W) kenan, domin bai ware kowa ba, kuma Annabin na daga cikin Quraishawa kuma yana raye cikinsu. 


Kun san addinin Ibrahim shine muslimci, shi kuma Zaid yace shi kadai ne ke kan addinin Ibrahim (A. S) daga cikin Quraishawa. 


" SUBHANAL-LAHI AMMA TASIFUUN  ."


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


      (08137925034)


21st February, 2021/  9th Rajab, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post