SHINE ZAI BN ABDUL-MANAF BN AMEER BN AMRUU
Kamar yadda aka sani ne cewa laqabi kan rinjayi suna ta yadda sai kaga wani lokaci an tara mutane masu yawa amma basu san haqiqanin sunan wani ba.
Imam (A. S) ya nasabta kansa-da-kansa da asalin sunan nasabarsa ga wadanda basu sani ba. Ga shi dai daga bakinsa (A. S) ;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
الأمالي للصدوق مع، معاني الأخبار عَلِيُّ بْنُ عِيسَى الْمُجَاوِرُ فِي مَسْجِدِ الْكُوفَةِ عَنْ عَلِيِّ بْنِ مُحَمَّدِ بْنِ بُنْدَارَ عَنْ أَبِيهِ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ عَلِيٍّ الْمُقْرِي عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ سِنَانٍ عَنْ مَالِكِ بْنِ عَطِيَّةَ عَنْ ثُوَيْرِ بْنِ سَعِيدٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ سَعِيدِ بْنِ عِلَاقَةَ عَنِ الْحَسَنِ الْبَصْرِيِّ قَالَ: صَعِدَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ع مِنْبَرَ الْبَصْرَةِ[39] فَقَالَ أَيُّهَا النَّاسُ انْسُبُونِي فَمَنْ عَرَفَنِي فَلْيَنْسُبْنِي وَ إِلَّا فَأَنَا أَنْسُبُ نَفْسِي أَنَا زَيْدُ بْنُ عَبْدِ مَنَافِ بْنِ عَامِرِ بْنِ عَمْرِو بْنِ الْمُغِيرَةِ بْنِ زَيْدِ بْنِ كِلَابٍ فَقَامَ إِلَيْهِ ابْنُ الْكَوَّاءِ فَقَالَ لَهُ يَا هَذَا مَا نَعْرِفُ لَكَ نَسَباً غَيْرَ أَنَّكَ- عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبِ بْنِ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ بْنِ هَاشِمِ بْنِ عَبْدِ مَنَافِ بْنِ قُصَيِّ بْنِ كِلَابٍ فَقَالَ لَهُ يَا لُكَعُ إِنَّ أَبِي سَمَّانِي زَيْداً بِاسْمِ جَدِّهِ قُصَيٍّ وَ إِنَّ اسْمَ أَبِي عَبْدُ مَنَافٍ فَغَلَبَتِ الْكُنْيَةُ عَلَى الِاسْمِ وَ إِنَّ اسْمَ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ عَامِرٌ فَغَلَبَ اللَّقَبُ عَلَى الِاسْمِ وَ اسْمُ هَاشِمٍ عَمْرٌو فَغَلَبَ اللَّقَبُ عَلَى الِاسْمِ وَ اسْمُ عَبْدِ مَنَافٍ الْمُغِيرَةُ فَغَلَبَ اللَّقَبُ عَلَى الِاسْمِ وَ إِنَّ اسْمَ قُصَيٍّ زَيْدٌ فَسَمَّتْهُ الْعَرَبُ مُجَمِّعاً لِجَمْعِهِ إِيَّاهَا مِنَ الْبَلَدِ الْأَقْصَى إِلَى مَكَّةَ فَغَلَبَ اللَّقَبُ عَلَى الِاسْمِ."
أمالي الصدوق: 359. معاني الأخبار: 120 و 121
Ya zo cikin Amali Lis-Sudduq tare da Ma'anil-Akbar, daga Aliyu Bn Isah Al-Mujawiru cikin masallacin Kufah daga Aliyu Bn Muhammad Bn Bundaar, daga babansa Muhammad Bn Aliyu Al-Qummiy, daga Muhammad Bn Sinaan, daga Malik Bn Adiyyata, daga Suwair Bn Sa'eed, daga babansa daga Sa'eed Bn Alaaqata, daga Hassan Al-Basariy yace; " Amirul-muminina (A. S) ya hau Mimbarin Basrah, sai yace;
" YAA KU MUTANE, KU NASABTA NI ! WANDA YA SANNI YA NASABTA NI, IDAN KUMA BA HAKA BA ZAN NASABTA KAINA !
NINE ZAID BN ABDUL-MANAF BN AMEER BN AMRUU BN MUGEERATA BN ZAID BN KILAAB !"
Sai Ibn Kawwa'a ya miqe zuwa gare shi yace masa, " Yaa kai wannan ! Bamu san wata nasaba taka ba face kaine Aliyu Bn Abiy 'Dalib Bn Abdul-Mudallib Bn Haashim Bn Abdul-Manaf Bn Qusaiyi Bn Kilab. " Sai yace masa;
" YAA KAI LUKA'U ! LALLE BABANA YA KIRAYE NI DA ZAID DA SUNAN KAKANSA QUSAIY, KUMA SUNAN BABANA SHINE ABDUL-MANAAF, SAI ALKUNYA TA RINJAYI SUNA, KUMA SUNAN ABDUL-MUDALLIB SHINE AAMEER, SAI LAQABI YA RINJAYI SUNA, KUMA SUNAN HAASHIM SHINE AMRUU, SAI LAQABI YA RINJAYI SUNA, KUMA SUNAN ABDUL-MANAAF SHINE MUGEERATA, SAI LAQABI YA RINJAYI SUNA, KUMA SUNAN QUSAIY SHINE ZAID, SAI LARABAWA SUKA KIRAYE SHI GABADAYA SABODA TATTARASU DA YAKE YI DAGA BIRNIN AQSAA ZUWA MAKKAH, SAI LAQABI YA RINJAYI SUNA ."
Wannan ita ce nasabarsa (A. S) cikin sunayen yanka (na asali) cikin sunayen iyaye da kakanninsa (A. S).
A wata riwaya kuma daga Ibn Abbas (R. A) yake cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
عَنِ ابْنِ زَكَرِيَّا الْقَطَّانِ عَنِ ابْنِ حَبِيبٍ عَنِ ابْنِ بُهْلُولٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ أَبِي الْحَسَنِ الْعَبْدِيِّ عَنْ سُلَيْمَانَ بْنِ مِهْرَانَ عَنْ عَبَايَةَ بْنِ رِبْعِيٍّ قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى ابْنِ عَبَّاسٍ فَقَالَ لَهُ أَخْبِرْنِي عَنِ الْأَنْزَعِ الْبَطِينِ عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ فَقَدِ اخْتَلَفَ النَّاسُ فِيهِ فَقَالَ لَهُ ابْنُ عَبَّاسٍ أَيُّهَا الرَّجُلُ وَ اللَّهِ لَقَدْ سَأَلْتَ عَنْ رَجُلٍ مَا وَطِئَ الْحَصَى[48] بَعْدَ رَسُولِ اللَّهِ ص أَفْضَلُ مِنْهُ وَ إِنَّهُ لَأَخُو رَسُولِ اللَّهِ وَ ابْنُ عَمِّهِ وَ وَصِيُّهُ وَ خَلِيفَتُهُ عَلَى أُمَّتِهِ وَ إِنَّهُ لَأَنْزَعُ مِنَ الشِّرْكِ بَطِينٌ[49] مِنَ الْعِلْمِ وَ لَقَدْ سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ ص يَقُولُ مَنْ أَرَادَ النَّجَاةَ غَداً فَلْيَأْخُذْ بِحُجْزَةِ هَذَا الْأَنْزَعِ يَعْنِي عَلِيّاً."
علل الشرائع: 64. معاني الأخبار: 43.
Daga Ibn Zakariyyah Al-Qaddani, daga Ibn Habeeb daga Ibn Buhuluu, daga babansa daga baban Hassan Al-Abdeey, saga Sulaiman Bn Himraan, daga Abayata Bn Rib-eeyyin yace; Wani mutum ya zo wajen Ibn Abbas (R. A) sai yace masa;
" Ka bani labari game da ANZAA-IL BADANI (mai babban ciki) Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A. S), domin mutane sunyi sabani a kansa. " Sai Ibn Abbas (R. A) yace;
" YAA KAI WANNAN MUTUMIN, HAQIQA KAYI TAMBAYA KAN WANDA BABU WANI KAMARSA KAN DORON QASA BAYAN ANNABI (S. A. W. W). KUMA HAQIQA SHINE 'DAN'UWAN MANZON ALLAH (S. A. W. W) , 'DAN AMMINSA, WASIYYINSA KUMA KHALIFANSA CIKIN AL'UMMARSA, SANNAN KUMA YA TSABTATU DAGA SHIRKA KUMA WANDA YA CIKA DA ILIMI. HAQIQA NA JI MANZON ALLAH (S. A. W. W) YANA CEWA;
" DUK WANDA KE SON TSIRA GOBE (Qiyama), TO, YAYI RIQO DA ZARIYAR WANNAN !" Yana nufin Aliyu (A. S).
YAA ALLAH 🙏🏿🙏🏿🙏🏿🙏🏿KA SHAIDA MUNYI RIQO DA WANNAN BAWA NAKA WASIYYIN ANNABINKA (S. A W. W) !
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
24th February, 2021/ 13th Rajab, 1442.