WANENE IMAM ALI (A.S)??? (1)



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED 


BAQURAISHE JININ HASHIMAWA BIYU


A nasaba ta Manzon Allah (S. A. W. W) Baquraishe ne kuma Bahashime wanda cikin qabilun larabawa babu madaukakiyar qabila kamarta. Duk wanda bai fito cikin Banu Hashim ba ba a sanya shi cikin madaukakiyar Qabilar laraba.


Imam Ali (A. S) cikakken Bahashime ne wanda ya fito cikin Hashima biyu, wato Uwa da Uba. Bari mu kawo nasabarsa (A. S) don fito dashi qarara cikin masoya da maqiyinsa. 


        NASABARSA (A. S)


MAHAIFINSA :- Shine Abu 'Dalib (Abdul-Manaf) Bn Abdul-Mudallib Bn Hashim Bn Abdul-Manaf Bn Qusaiyi.............


MAHAIFIYARSA :- Ita ce Fadimatu Bnt Asad Bn Hashim Bn Abdul-Manaf Bn Qusaiyi..........


Hashim shine kakansa na biyu ta bangaren mahaifinsa, sannan kuma kakansa na biyu ta bangaren mahaifiyarsa. Saboda hakane ake kiransa jinin Hashima biyu. Wannan kuwa wata martaba ce wacce Allah (T) yayi masa bisa ganin damarSa ba tare da neman shawarar wani  ko ra'ayinsa ba.


Manzon Allah (S. A. W. W) ma yayi fahari da wannan nasaba tasa ta Bahashime yadda yake cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" HAQIQA ALLAH (S. W. T) YA ZABI ISMA'IL DAGA CIKIN 'YA'YAN IBRAHIM, KUMA YA ZABI KINANATA DAGA 'YA'YAN ISMA'IL, KUMA YA ZABI QURAISHAWA DAGA CIKIN KINANATA, KUMA YA ZABI BANU HASHIM DAGA CIKIN QURAISHAWA. NI KUMA YA ZABE NI DAGA BANU HASHIM, SABODA HAKA NI ZABABBEN TSATSO NE MAFI GIRMAN ZABABBUN TSATSON LARABAWA  ."


To, shi ma Imam Ali (A. S) ya fito ne daga cikin wannan tsatso mafifici na Hashimawa. 


Ya zo cikin Usulul-Kafiy cewa;


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 الكافي‏: وُلِدَ ع بَعْدَ عَامِ الْفِيلِ بِثَلَاثِينَ سَنَةً و أُمُّهُ فَاطِمَةُ بِنْتُ أَسَدِ بْنِ هَاشِمِ بْنِ عَبْدِ مَنَافٍ وَ هُوَ أَوَّلُ هَاشِمِيٍّ وَلَدَهُ هَاشِمٌ مَرَّتَيْنِ‏[19].


" An haife shi (A. S) ne bayan shekarar Giwa da shekara talatin (30), kuma Mahaifiyarsa ita ce Fadimatu Bnt Asad Bn Hashim Bn Abdul-Manaaf, shine (A. S) Bahashime na farko wanda aka haifa cikin Hashimawa biyu ."


A wata riwaya kuma mai matuqar dadi tana cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


الكافي الْحُسَيْنُ بْنُ مُحَمَّدٍ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ يَحْيَى الْفَارِسِيِّ عَنْ أَبِي حَنِيفَةَ مُحَمَّدِ بْنِ يَحْيَى عَنِ الْوَلِيدِ بْنِ أَبَانٍ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مُسْكَانَ عَنْ أَبِيهِ قَالَ قَالَ أَبُو عَبْدِ اللَّهِ ع‏ إِنَّ فَاطِمَةَ بِنْتَ أَسَدٍ جَاءَتْ إِلَى أَبِي طَالِبٍ لِتُبَشِّرَهُ بِمَوْلِدِ النَّبِيِّ ص فَقَالَ أَبُو طَالِبٍ اصْبِرِي سَبْتاً آتِيكِ أُبَشِّرُكِ بِمِثْلِهِ‏[20] إِلَّا النُّبُوَّةَ وَ قَالَ السَّبْتُ ثَلَاثُونَ سَنَةً وَ كَانَ بَيْنَ رَسُولِ اللَّهِ ص وَ أَمِيرِ الْمُؤْمِنِينَ ع ثَلَاثُونَ سَنَةً[21].


أصول الكافي 1: 452.


Cikin Khafiy, daga Hussaini Bn Muhammad, daga Muhammad Bn Yahya al-Farisiy, daga Abu Hanifata Muhammad Bn Yahya, daga Walid Bn Abban, daga Muhammad Bn Abdullahi Bn Muskana, daga babansa yace;  Abu Abdullah (A. S) yace; 


" LALLE FADIMATU BNT ASAD TA ZO WAJEN ABU 'DALIB (A. S) DOMIN TAYI MASA BUSHARAR HAIHUWAR ANNABI (S. A. W .W), SAI ABU 'DALIB YACE;  " KIYI HAQURI NA 'DAN WANI LOKACI, ZAN ZO MIKI NAYI MIKI BUSHARA DA MISALINSA, SAI DAI BABU ANNABTA. YACE, " 'DAN LOKACIN SHEKARU TALATIN (30) NE. "


Ya kasance tsakanin Manzon Allah (S. A. W. W) da shugaban muminai (A. S) shekaru talatin (30) "


MARABA DA ZUWANKA YAA JININ HASHIMAWA  🌸☘️🌸🍀🌸🌿🌸🌺🌸🌹🌸🌴🌸


ZA MU CIGABA INSHA ALLAH. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


    (08137925034)


23rd February, 2021/  12th Rajab, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post