MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UUPDATED @
BAIWAR DAKE YAWO DA ANNABI CIKIN BIRNIN MADINAH
Ba wai bisa jin dadi muke kawo irin wadannan maganganu ba sai dai kawai don mu nunawa mutane irin rashin mutuncin da wasu malaman Sunnah ke yiwa Annabi (S. A. W. W), kuma suna inganta maganar tare da ganin laifin masu qaryata wadannan miyagun malamai.
Wajibi ne ba wai zabi ko ganin dama ba a kanmu mu fito don yaqar wadannan miyagun hadisai masu cin zarafin Annabi (S. A. W. W) don a nuna falalar wasu.
Ya zo cikin Musnad-Ahmad kamar haka;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
11721- حَدَّثَنَا هُشَيْمٌ ، أخبرَنَا حُمَيْدٌ ، عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ ، قَالَ : " إِنْ كَانَتْ الْأَمَةُ مِنْ أَهْلِ الْمَدِينَةِ ، لَتَأْخُذُ بِيَدِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ، فَتَنْطَلِقُ بِهِ فِي حَاجَتِهَا " .
Hushaim ya bamu labari, Humaid ya bamu labari daga Anas Bn Malik yace;
" LALLE WATA BAIWA (kuyanga) DAGA MUTANEN MADINAH TA KASANCE TANA KAMA HANNUN MANZON ALLAH (S. A. W. W) TA TAFI DASHI DON BIYAN BUQATARTA ."
Wannan baiwar dai bamu san wacce ba don basu ambaci sunanta ba, sannan kuma bamu san wacce irin buqata tata ce wacce sai ta ja shi (S. A. W. W) sannan buqatar tata ta biya ba.
Sannan kuma bamu san wanne irin darasi suke qoqarin koyar damu cikin wannan hadisi ba, domin mun san duk wani abinda aka kawo akwai darasin da ake son fito da shi ko koyar dashi.
Sannan kuma wani abin mamaki shine sai ga shi daga babin Anas din yana fada cikin hadisi na gaba kamar haka;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
۞۞۞۞۞۞
11722- حَدَّثَنَا هُشَيْمٌ ، أخبرَنَا عَبْدُ الْعَزِيزِ بْنُ صُهَيْبٍ ، وَإِسْمَاعِيلُ ، حَدَّثَنَا عَبْدُ الْعَزِيزِ بْنُ صُهَيْبٍ ، عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ ، قَالَ : قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : " مَنْ كَذَبَ عَلَيَّ مُتَعَمِّدًا ، فَلْيَتَبَوَّأْ مَقْعَدَهُ مِنَ النَّارِ " .
Hushaim ya bamu labari, Abdul-Azeez Bn Suhaib da Isma'il sun bamu labari daga Anas Bn Malik, yace;
Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" DUK WANDA YAYI MIN QARYA DA GANGAN, TO, YA TANADI MAZAUNINSA DAGA HUTA ."
(MUSNAD-AHMAD)
Haba malam Anas, ashe ka san da wannan magana ta Annabi (S. A. W. W) amma kake fadar irin wannan magana a kansa?
Idan kuwa masu riwaito hadisan ne suka yi maka qarya wai ka ce musu akwai matar da ke riqe hannun Annabi (S.A.W W) suna yawo a garin Madinah, to, Allah ya isar maka a kansu.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
26th February, 2021/ 15th Rajab, 1442.