Tambaya da Amsa daga bakin Sayyid Zakzaky (H) kashi na hudu: Tambaya kan wanda yayi mafarkin ana azabtar dashi da wuta


 TAMBAYA DA AMSOSHI DAGA BAKIN SHEIKH ZAKZAKY (H)


         KASHINA (4)


MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE


TAMBAYA: Akramakallahu na yi mafarki ana azabtar da ni da wuta. Na yi ta addu'a amma ba a daina ba har na farka. Ko me wannan yake nufi? Kuma wacce shawara Malam zai ba ni a kan haka?


SHAIKH ZAKZAKY: To, lallai ba ni da ilimi dangane da fassarar mafarki. Sai dai shi mafarki yana iya zama albishir ko garagadi. Wannan yana iya zama gargadi a gare ka. Saboda haka sai ka guji abubuwan da kake aikatawa wanda Allah ba ya so. Kuma ka roki Allah ya yafe maka. Wallahu a'alam.


TAMBAYA: Assalamu alaikum, nine dana ya yi laifi, na tashi hukunta shi, sai ya ji ciwo a sanadiyyar wannan hukuncin da na yi masa. Shin akwai diyyar da zan biya ne ko kuwa?


SHAIKH ZAKZAKY: E, lallai za ka biya diyya daidai gwargwadon jin ciwon da ka yi masa. Kuma sai a kai wa adilai su yi hukuncin, ba kai za ka yi hukuncin ba. Sai ka fid da daga cikin dukiyarka, ba dukiyarsa ba (shi yaron), sai ka biya yaron.


TAMBAYA: Allah gafarta Malam akwai diyyar da ake biya idan an buge dabba da abin hawa, ta mutu, ko ba ta mutu ba?


SHAIKH ZAKZAKY: Ma'abota hakki na wannan dabba din, akuya ce ko kare, to lallai in ganganci ne ba kuskure ba, to zai zama za ka biya. Alal misali, idan ya karye ne, aka nemi za ka biya wani abu domin a dora shi, ko a kai shi asibiti ko abin da ya yi kama da haka nan, to za ka dauki wannan dawainiyar. Amma wannan sai in ya zamana da ganganci ne ko da kuskure, ba bisa hadari ba. Alal misali kana ta tafiya, ba kai ka shige ma karen ba, ko dabba din ba, dabbar ta fado, to wannan zai zama babu komai.


TAMBAYA: Assalamu alaikum, mutum ne ya yi alwala, kafin ya yi sallah sai wani wanda ba musulmi ba ya mika masa hannu suka gaisa. Yaya matasayin alwalarsa?


SHAIKH ZAKZAKY: To, alwala tana nan sai dai idan ya tsargu dangane da rashin tsarkin shi wanda ya ba shi hannun, to sai ya wanke hannun.


Kusau raremu zuwa Kashi na (5) yanan tafe 


Tare da Mai kawo muku duk sati sau uku3 da musalin qarfe 8:00 pm 


Faruq sani kudan

08/02/2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post