MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE
TAMBAYA: Assalamu alaikum, mutum ne ya je yin sallama da iyayensa zai je taron harka islamiyya, to sai iyayen nasa suka ji tsoron azzalumai za su iya auka wa a wajen. Saboda haka sai suka hana shi. Shin ya tafi kawai ko kuwa dai ya tsaya?
SHAIKH ZAKZAKY: To, iyaye na da hakki na biyayya a kan abin da bai sabawa na Allah ba. Har wala yau kuma kana da hakki na yin harkar addini, ko da iyayenka ba su yarda ba in shi ne mafita a gare ka. Wannan ya danganta da yadda kai ka ga wannan zuwa din kenan. Tana iya yiwuwa ya zama maslaha ka bi shawarar iyayenka din, tana iya kuma zama (kamar mu ba abin wata fassarar kamar wani yaki ne wanda ya zama lazim a yi). Amma dai ya danganta da matsayin abin da za ka je din ne. Misali in ya zama mai nema ilimi ne, kuma a nan ne kawai za ka samu wannan ilimin, to yana iya zama ka ga cewa, to lallai ko da hadari dai, in ma ka fada hannun azzalumai sun yi maka wani abu, to kana da ladan wannan.
TAMBAYA: Allah gafarta Malam nine nake bin bashi har lokacin fid da Khumusi ya yi, sai na fitar da khumusin wadanda nake tsammanin za su biya ni. Sai daya daga cikinsu bai biya ni ba, amma wadanda ban yi tsammanin za su biya ni ba, sai daya daga cikinsu ya biya ni. Kuma a daidai lokaci guda. Sai na kaddara cewa ai shi kenan. Sai bayan tsawon lokaci na yi tambaya, sai aka ce sai dai na koma can inda na kai Khumusin in yi bayani. Allah gafarta Malam mene ne hukuncin?
SHAIKH ZAKZAKY: To dama tun farko ba za ka biya Khumusin abin da bai zo hannunka ba, sai abin da ya riga ya zo hannunka. Tun farko wato bashi za ka fitar da shi daga wanda kake bi daga cikin lissafin. Amma tunda kai ka yi amfani da fatawar kanka ka fidda ma na bashi, to sai mu dauka ya riga dai ya tafi, amma dai bai hau kanka ba da ma. Sannan kuma idan bashin da ya zo hannu din ya yi daidai da wanda bai zo hannu ba, to shi wanda ka fitar, wanda ba ka tsammani din ya tsaya a matsyinsa. In kuma da bambanci kai sai ka cika. In ko da ragowa, to lallai ba za ka je ka ce a ba ka ragowarka ba. Sai dai ka yi fatan Allah ya ba ka lada.
TAMBAYA: Ina so Malam ya yi mani bayanin yadda ake ciyar da miskini idan mutum ya sami matsalar da ta hana shi yin azumi.
SHAIKH ZAKZAKY: To, hanyoyi ne guda uku; tufatarwa, idan namiji ne riga da wando, idan mace ce doguwar riga da murfin kai. Sai kuma ciyarwa, wanda yake nufin mutum ya ba da abinci dafaffe, wanda mutum zai ci ya koshi har da abin sha. Ko kuma ya ba da mudu guda na Annabi. Amma shi ana son wannan in zai ba da mudu ne ya nunka biyu, sannan kuma ya ba da abin miya. Amma wala'alla tufatarwar shi ya fi alheri ga mafi yawan miskinai, wadanda suka rasa tufafi. Na biyu kuma sai ya zama ba da kayan abinci, musamman ga ma'abocin iyali, wanda shi ma an yarda kana iya lissafin ma har da iyalansa. Misali in yana da mace daya da 'ya'ya biyu, za ka iya ba shi kason mutum hudu, amma in ka tabbatar da cewa zai ciyar da iyalin ne ba zai je ya sayar ne ya yi wani abin da kudin ba.
Kusau raremu zuwa Kashi na (6) yanan tafe
Tare da mai kawo muku duk sati sau uku3
Faruq sani kudan ✍️
11/2/2021