Shi Imam Ali (A.S) son sa sai wanda Allah yasa yana da rabo duniya da lahira !


 

Anas isah Ismail

Annabi Muhammad Manzon Allah (S) yace: “Son imam Ali bin Abidalib wanzajjen abu ne a cikin zukatan Muminai, Ba wanda zai so shi face Mumini, kuma ba wanda zai ki shi face Munafuki, asararre, matalauci.


A duba Mustadrak din Hakim, 3/127.


Musnadin Ahmad, 1/86.


 Sahihu Muslim, 2/271. 


Sahihu Turmuzi, 2/301.


 Sahihu Nasa’I, 2/271.


 Tafsirin Raziy, 19/13.


ABIN NUFI DAGA ANNABI MUHAMMAD (S).


Annabi Muhammad (S) yana fada mana cewa duk wanda kaga yana son Imam Ali (AS) so da ma’anar so na hakika, babu shakka wanzajjen al’amari ne da Allah (T) ya wanzar masa da shi.


Ba bisa hadari ake samun mutum ya amsa cewa yana son Imam Ali (AS) ba.


-Kuma bai zama masoyi ba sam! Duk wanda ya wayi gari yana bege yana nuna soyayyarsa da kaunarsa ga Imam Ali (AS) a lokaci guda kuma yana bayyana soyayyarsa da kaunarsa da ma biyayyarsa ga wadanda suka zalunci Imam Ali (AS); 


wadanda suka masa gasabin hakkinsa na kilafa, da wadanda suka tasa shi da zagi akan munbari, da wadanda suka fito muraratan a bayyane suka zare masa takobi suka yake shi, dama masu goyon bayan wadanda suka zalunce shi din.


Lallai tabbas tare da soyayyar Imam Ali (AS) akwai sallamawa da biyayya mudlika a gare shi.


Na’am, mai sauki ne ka samu wani yace maka yana son Ali (AS), amma kuma ka bincike shi da kyau, wallahi in har yana son wadanda suka yaki Ali (AS), yakin boye ko na fili, to tabbas shi makiyin Ali ne! koda fa kaji yana ma Imam Ali Waka, ko yana yabonsa, ko ma ya saka ma yaronsa sunan Ali din.


To kuma tabbataccen al’amari shine, babu wani Mumini face shi

masoyin Imam Ali (AS) ne. Masoyi da ma’anar Masoyi na nufin Mabiyi. Mun gode ma Allah (T) da ya azurtamu da soyayya da biyayya ga Imam Ali (AS), Allah ya cika mana soyayyarmu da biyayyarmu gare shi (AS). 


Allah ya sakawa Jagoranmu Malaminmu, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) wanda ta dalilinsa ne muka san umurnin

Annabi (S) da duk wani albishir da ya yi mana akan iyalan gidansa.

 

Allah domin isar sayyeda Zahara kagaggauta bayyannamana sheikh Muhammad turi Allah domin hawayen sayyeda Zahara.



Allah domin saran takobin imam ALI Allah kakara lafia da nisan kwana ga sheikh yakub yahya katsina Allah



Allahummah salli ala Muhammad wa Ali Muhammad.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post