@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
IDAN KANA DA WADANNAN KA HUTACAR DA SHAIDAN
Alqawari ne wanda Shaidan (L. A) ya daukawa Allah yayin da ya nemi a jinkirta masa a rayuwa in har an jinkirta masa sai ya halakar da bayinSa 'ya'yan Adam (A. S) matuqar ya sami iko a kansu.
Allah ya amsa masa buqatar tasa ta neman jinkiri, saboda haka ya dana tarkonsa ko ta ina don ganin ya kama wadanda za su tafi wuta tare. Wannan shine aikin da yake yi tare da rundunarsa ba dare ba rawa !
To, amma duk da wannan aiki da ya daukarwa kansa yakan sauqaqa shi ko kuma nace mutane suka sauqaqa masa aiki ta hanyar yin aikin nasa da kansu. Saboda haka idan yaga haka sai yayi murna don an samar masa sauqi.
Ya zo cikin riwaya daga Abu Abdullahi (A. S) cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
عَنْ سَعْدٍ عَنِ الْبَرْقِيِّ عَنْ أَبِيهِ عَنْ صَفْوَانَ بْنِ يَحْيَى عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ الْحَجَّاجِ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ:
Daga Sa'ad daga Barqeeyi daga babansa daga Safwan Bn Yahya, daga Abdurrahman Bn Hajjaaj, daga Abu Abdullahi (A. S) yace;
قَالَ إِبْلِيسُ لَعَنَهُ اللَّهُ لِجُنُودِهِ إِذَا اسْتَمْكَنْتُ مِنِ ابْنِ آدَمَ فِي ثَلَاثٍ لَمْ أُبَالِ مَا عَمِلَ فَإِنَّهُ غَيْرُ مَقْبُولٍ مِنْهُ إِذَا اسْتَكْثَرَ عَمَلَهُ وَ نَسِيَ ذَنْبَهُ وَ دَخَلَهُ الْعُجْبُ[29
" IBLIS (L. A) YA CEWA RUNDUNARSA, " IDAN ABUBUWA UKU SUKA ZAUNA (kasance) TARE DA 'DAN ADAM, TO, BAN DAMU DA ABINDA ZAI AIKATA BA, DOMIN SHI BA YA KARBA DAGA GARE SHI.
(1)- IDAN YA YAWAITA AIKINSA .
(2)- KUMA YA MANTA ZUNUBINSA.
(3)- KUMA JI-JI-DA-KAI YA SHIGE SHI ."
الخصال ج 1 ص 55.
SHARHI
Abu na farko shine, duk mutumin da ya yawaita aiki in dai na duniya ne, to, za a sami naqasu cikin aikata abinda zai sami kusanci ga Allah. Idan kuma aikin ibada ce ya tsawaita, to, sai sare (wasu wata rana zai watsar da shi). Shi yasa Annabi (S. A. W. W) ya hane mu game da yin irin wannan aiki, kuma yace aikin da za ka yi shi mai dorewa shi yafi alkhairi komai qanqantarsa.
Shi kuwa wanda ya manta da zunuban da yake aikatawa ba zai taba zuwa ga Allah ba, kuma duk wanda ba ya tuba (IRIN BUHARI) ba zai shiga Aljannah ba. Ko Annabi (S. A. W. W) da ba ya aikata zunubi ma yana tuba da neman gafarar Ubangijinsa.
Sannan kuma duk wanda ji-ji-da-kai (UJUBU) ya shige shi ba zai taba risnawa gaskiya ba ballantana ya bi ta, kuma ba zai taba yin wani aiki domin Allah ba. Idan kuwa mutum ya kasance haka babu abinda zai yi wanda Allah zai karba.
Saboda haka Iblis (L. A) ba zai taba bata lokacinsa a kansa ba, domin ya riga ya samu, sai dai kawai jiran lokacin shiga Allah.
YAA ALLAH KA TSERATAR DAMU DAGA AIKATA ABINDA ZA MU HUTACAR DA SHAIDAN (L. A) . 🙏🏿🙏🏿🙏🏿
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
2nd February, 2021/ 20th Jimada-Saaniy, 1442.