Rabon gado (Inheritance) a Muslumci. Rubutu na ɗaya zuwa biyar..!!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

'YAN'UWA BA SA GADO TARE DA WANI DAGA CIKIN HUDUN NAN

Allah (T) ya riga ya gama mana komai cikin al'amarin rabon gado, cikin Qur'ani ya kawo mana yadda kason kowa zai kasance .

Yayi mana su daki-daki ta yadda wani ba ya shiga wani, sannan kuma duk wanda yake da kaso cikin gado ba za a iya kawar dashi ba sai dai ya tashi daga wani matsayi zuwa wani matsayin. 

Akwai wasu jinsin mutane wadanda matuqar akwai wani daga cikinsu rayayye, to, wani daga cikin 'yan'uwa ba zai yi tarayya dasu ba , sai dai idan babu wani daga cikinsu sai 'yan'uwa su sami shiga .

Bari dai mu kawo nassin da ke nuni kan haka, ku biyo mu cikin nutsuwa da karatu na fahinta. 

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

 تفسير العياشي عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ مُسْلِمٍ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع قَالَ:

Ya zo cikin Tafsir na Ayaashiy daga Muhammad Bn Muslim, daga Abu Ja'afar (A. S) yace; 

 إِذَا تَرَكَ الرَّجُلُ أُمَّهُ وَ أَبَاهُ وَ ابْنَتَهُ أَوِ ابْنَهُ فَإِذَا هُوَ تَرَكَ وَاحِداً مِنْ هَؤُلَاءِ الْأَرْبَعَةِ فَلَيْسَ هُوَ مِنَ الَّذِي عَنَى اللَّهُ فِي قَوْلِهِ- 

" Idan mutum ya bar mahaifiyarsa, da mahaifinsa, da 'yarsa ko dansa , to, idan ya bar wani (1) daga cikin wadannan hudu (4), to, ba sa daga cikin wadanda Allah ya ambato cikin fadinSa (S. W. A); 


" قُلِ اللَّهُ يُفْتِيكُمْ فِي الْكَلالَةِ "

" KACE ALLAH NA YI MUKU FATAWA CIKIN (al'amarin) KALALA ."


 لَيْسَ يَرِثُ مَعَ الْأُمِّ وَ لَا مَعَ الْأَبِ وَ لَا مَعَ الِابْنِ وَ لَا مَعَ الِابْنَةِ إِلَّا زَوْجٌ أَوْ زَوْجَةٌ فَإِنَّ الزَّوْجَ لَا يَنْقُصُ مِنَ النِّصْفِ شَيْئاً إِذَا لَمْ يَكُنْ مَعَهُ وَلَدٌ وَ لَا يَنْقُصُ الزَّوْجَةُ مِنَ الرُّبُعِ شَيْئاً إِذَا لَمْ يَكُنْ مَعَهَا وَلَدٌ[22

" To, (su wadannan da aka ambata cikin ayar) ba za suyi gado tare da Uwa ba, ko kuma tare da Uba ba, hakama (ba za suyi) tare da (son) ko 'ya ba. Sai dai za suyi gado tare da Miji ko Mata, domin shi Miji ba a tauye masa wani abu daga rabi 1/2 in dai babu da (son/daughter) tare da shi, sannan kuma ba a tauyewa Mata wani abu daga daga 1/4 in dai babu da (son/daughter) tare da ita ."


) نفس المصدر ج 1 ص 286.


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏101، ص: 347

Abinda ake nufi anan shine, wani daga cikin Uwa ko Uba ko 'Da ko 'Ya ba za suyi gado tare da 'yan'uwan mamaci wadanda aka ambace su cikin aya ta 11 da ta 170 cikin Suratul-Nisa'i ba, amma za suyi gado tare da Mijin Matar da ta rasu ko Matar Mijin da ya rasu, domin su babu mai tsare su daga cin gadon junansu.

Bari mu kawo misalai ko da uku ne don qara fito da al'amarin. 

(1)- Mata ce ta rasu ta bar 'Ya1 da Miji da Uwa da Uba ta dan'uwa shaqiqi tare da kudi #650,000.

  YADDA KASON ZAI KASANCE 

Anan 'ya tana da rabin dukiya, Uwa da Uba kuma kowannensu na da 1/6 tunda matar ta bar 'ya, Miji kuma na da 1/4, shi kuwa dan'uwa ba shi da komai tunda matar ba Kalala bace. 

  'Ya Miji Uwa Uba 
    1 1 1 1
   ---- ---- ---- -----
     2 4 6 6
     6 + 3 + 6 + 6=13
 ------------------------------------
                  12

Yanzu anan idan mun kasa dukiyar gida 12 wani ba zai sami kasonsu ba, saboda haka sai a raba ta kashi 13 kamar yadda adadin kason nasu ya bayar .

             KASON 'YA

  6 #650,000
--- * ---------------= #300,000
 13 1


               KASON MIJI 

 3 #650,000
--- * ----------------=#150,000
 13 1


         KASON UWA

  2 #650,000
 --- * --------------=#100,000
  13 1


         KASON UBA 

 2 #650,000
 --- * -------------=#100,000
  13 1


  KASON 'DAN'UWA 
                   👇🏼
     Ba shi da komai 


(2)- Miji ne ya rasu ya bar Mata 1, da Uwa da 'ya'ya mata 2 da kuma dan'uwa tare da kudi #3,000,000.

YADDA KASON ZAI KASANCE 

To, tunda Mijin yana da 'ya'ya matarsa za ta sami 1/8, Uwa kuma 1/6 , su kuma 'ya'yan tunda mata ne suna da 2/3.

 Mata Uwa 'yaya2 dan'
    1 1 2 👇🏼
   --- ---- --- 👇🏼
    8 6 3 👇🏼
    3 + 4 + 16 = 23 👇🏼
-----------------------------------
                  24

To, anan za a kasa dukiyar kashi 24 ne, sai kowa ya dau adadin kasonsa. 

          KASON MATA 

 3 #3,000,000
--- *----------------- =#375,000
 24 1


  KASON UWA 

 4 #3,000,000
--- *------------------=#500,000
 24 1


    KASON 'YA'YA

 16 #3,000,000
----* --------------=#2,000,000
  24 1


         'DAN'UWA 
                👇🏼
   Ba shi da komai 

Anan idan muka tara kason masu kaso gaba daya zai zama #2,875,000, za a sami sauran #125,000 daga cikin dukiyar. 

To, shi wannan saura za a mayar da shi ne zuwa ga 'ya'yan, suci kaso biyu kenan (FARDAN wa RADDAN) . Sai su raba shi tsakaninsu daidai-wa-daida. 

(3)- Mata ce ta rasu ta bar Miji da 'yan'uwanta shaqiqai mace da namiji, da kuma kudi #500,000.

To, anan tunda matar ba ta haihu ba ko kuma muce bata bar 'ya'ya ba, Mijinta yana da rabin abinda ta bari, su kuma 'yan'uwantaka sai su debe sauran abinda ya rage su raba namiji ya dau kaso biyu na 'yar mace. 

Ga shi kamar haka; 

   Miji 'Yan'uwa 
      1 👇🏼
    ------ Saura 
       2
       1
   ------------------------
              2


        KASON MIJI

  1 #500,000
----- * --------------= #250,000
   2 1

Abinda ya rage shine #250,000, sai su raba shi kashi uku, namiji ya dau kaso biyu tamatar kuma ta dau kaso daya. 

  Namiji Mace 
      2 1
    ------ ----------
       3 3
       2 + 1 =3
   ------------------------
                3

  KASON NAMIJI 

   2 #250,000
 ------ *--------------=#166,666
    3 1

     KASON MACE 

    1 #250,000
 ----- * --------------=#83,333
    3 1

Kunga anan 'yan'uwa sun sami kaso amma basu ragewa Miji wani abu daga rabin abinda matarsa ta bari ba. 


'YAN'UWA NA IYA CANZAWA UWA MATSAYI AMMA BA SU DA GADO

Tabbas 'yan'uwa na da tasiri ga mamaci domin su kan iya canza Uwa daga wani matsayi zuwa matsayi, sai dai kuma ba su wani rabo matuqar mamaci ya bar; 

- Uba, ko

- Uwa, ko

- 'Da ko kuma 

- 'Ya, domin su 'yan'uwa hukuncin 'ya'ya ne a kansu a rashin mahaifa ko 'ya'ya ga dan'uwansu mamaci.

Ya zo cikin Tafsiril-Qummy dangane da ayar nan da ke cewa, 

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

 تفسير القمي‏ يُوصِيكُمُ اللَّهُ فِي أَوْلادِكُمْ لِلذَّكَرِ مِثْلُ حَظِّ الْأُنْثَيَيْنِ‏:

" ALLAH NA YI MUKU WASIYYA CIKIN (al'amarin) 'YA'YANKU, NAMIJI DA MISALIN KASO BIYU NA MACE ."

 قَالَ إِذَا مَاتَ الرَّجُلُ وَ تَرَكَ بَنِينَ وَ بَنَاتٍ- فَلِلذَّكَرِ مِثْلُ حَظِّ الْأُنْثَيَيْنِ‏- فَإِنْ كُنَّ نِساءً فَوْقَ اثْنَتَيْنِ فَلَهُنَّ ثُلُثا ما تَرَكَ‏ يَعْنِي إِذَا مَاتَ الرَّجُلُ وَ تَرَكَ أَبَوَيْنِ وَ ابْنَتَيْنِ فَلِلْأَبَوَيْنِ السُّدُسَانِ وَ لِلِابْنَتَيْنِ الثُّلُثَانِ وَ إِنْ كَانَتِ الِابْنَةُ وَاحِدَةً فَلَهَا النِّصْفُ وَ لِأَبَوَيْهِ لِكُلِ وَاحِدٍ مِنْهُمَا السُّدُسُ وَ بَقِيَ سَهْمٌ يُقْسَمُ عَلَى خَمْسَةِ أَسْهُمٍ فَمَا أَصَابَ ثَلَاثَةَ أَسْهُمٍ فَلِلِابْنَةِ وَ مَا أَصَابَ اثْنَتَيْنِ فَلِلْأَبَوَيْنِ:

Yace, " Idan mutum ya rasu rabar 'ya'ya maza da 'ya'ya mata, to, namiji na da kaso biyu na 'ya mace, idan kuma 'ya'ya mata sun fi biyu, to, suna da kaso biyu bisa uku 2/3 na abinda aka bari.

Abin nufi shine, idan mutum ya rasu yabar mahaifa biyu Uwa da Uba, to, kowanne daga cikin mahaifa yana da 1/6 , su kuma 'ya'ya mata suna da biyu bisa uku 2/3, idan kuma 'ya 1 ce tana da rabi 1/2, su kuma iyaye kowa nada 1/6. Abinda yayi saura kuma sai a raba shi kashi 5, abinda aka samu daga ciki kashi uku na 'ya'ya ne, kaso biyu kuma na iyaye ne, kenan kowa zai sami asalin kasonsa sannan ya sami saura (Fardan wa Ta'addan). 

                MISALI 

- Mutum ya rasu ya bar Uwa da Uba da kuma 'ya 1 tare da kudi #400,000. 


 Uba Uwa 'Ya
   1 1 1
 ----- ----- ------
    6 6 2
    1 + 1 + 3 =5
----------------------------
               6

Anan za raba dukiyar kashi 6, sai kuma a bawa kowa adadin kasonsa daga cikin shidan nan. Ga shi kamar haka; 

            KASON UBA 


  1 #400,000
 ---- * --------------- = #66,666
   6 1


      KASON UWA

  1 #400,000
 --- * --------------- =#66,666
   6 1


           KASON 'YA

  3 #400,000
 ---- * ------------- =#200,000
  6 1

Idan muka tara kason mutane ukun nan za mu sami #333,332 daga cikin #400,000 da aka bari, wato za a sami ragowar #66,666 cikin dukiyar. Sai a raba wannan sauran kaso biyar, a bawa 'ya kaso uku, iyayen kuma a ba su kaso biyu, kowa dai-dai 1-1 kenan .

     GA SHI KAMAR HAKA 

Uwa da Uba 'Ya 
         2 3
       ----- ------
         5 5
         2 + 3= 5
      -------------------------
                  5


     KASON UWA DA UBA 

   2 #66,666
 ---- * ------------= #26,666.4
   5 1

Sai su raba shi daidai, kowa zai sami qarin 13,333.2 kenan akan kasonsa na farko.

QARIN KASON 'YA 

  3 #66,666
 --- * ------------= #39,999.6
   5 1


Idan muka tara za muga ya kama #66,665, wato #1 ta saura wacce ba za ta rabu ba. 

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

Imam ya qara da cewa, 

 فَإِنْ كَانَ لِلْمَيِّتِ إِخْوَةٌ وَ أَخَوَاتٌ مِنْ قِبَلِ الْأَبِ وَ الْأُمِّ أَوْ مِنْ قِبَلِ الْأَبِ وَحْدَهُ فَلِأُمِّهِ السُّدُسُ وَ لِلْأَبِ خَمْسَةُ أَسْدَاسٍ فَإِنَّ الْإِخْوَةَ وَ الْأَخَوَاتِ مِنْ قِبَلِ الْأَبِ هُمْ فِي عِيَالِ الْأَبِ وَ تَلْزَمُهُ مَئُونَتُهُمْ فَهُمْ يَحْجُبُونَ الْأُمَّ عَنِ الثُّلُثِ وَ لَا يَرِثُونَ‏[3]

Idan kuma ya kasance mamacin yana da 'yan'uwa maza da mata ta bangaren Uwa da Uwa (shaqiqai) ko kuma ta bangaren Uba ne kadai (Li-Abai), to, Uwa na da kashi 1 ne daga cikin shida 1/6, Uba kuma na da kashi biyar daga cikin shida 5/6. Domin su 'yan'uwa maza da mata ta bangaren Uba na daga cikin iyalinsa (Uba) , dukkan dawainiyarsu tana kansa ne (Uban), suna tsare Uwa daga samun 1/3, amma kuma su ('yan'uwan) ba su da gado (duk da cewa samuwarsu ya canzawa Uwa kason ta). 

تفسير عليّ بن إبراهيم ج 1 ص 132- 133.

                 MISALI

Mutum ne ya rasu ya bar Uwa da Uba da kuma 'yan'uwa shaqiqai, tare da kudi #120,000.

Allah (T) na cewa; 

.....وَلِأَبَوَيۡهِ لِكُلِّ وَٰحِدٖ مِّنۡهُمَا ٱلسُّدُسُ مِمَّا تَرَكَ إِن كَانَ لَهُۥ وَلَدٞۚ فَإِن لَّمۡ يَكُن لَّهُۥ وَلَدٞ وَوَرِثَهُۥٓ أَبَوَاهُ فَلِأُمِّهِ ٱلثُّلُثُۚ فَإِن كَانَ لَهُۥٓ إِخۡوَةٞ فَلِأُمِّهِ ٱلسُّدُسُۚ

" KOWANNE 'DAYA DAGA CIKIN MAHAIFANSA YANA DA 1/6 NA DAGA ABINDA YA BARI IN YA KASANCE YANA DA 'DA, IDAN KUMA BA SHI DA 'DA IYAYENSA NE KADAI SUKA GAJE SHI, TO, UWARSA TANA DA 1/3, IDAN KUMA YANA DA 'YAN'UWA, TO, MAHAIFIYARSA TANA DA 1/6."


To, anan tunda mamacin bai haihu ba amma kuma yana da 'yan'uwa, Uwa tana da kaso daya 1 ne cikin shida (6), Uba kuma yana da kaso biyar (5) daga cikin shida, amma 'yan'uwa ba su da komai duk da cewa sun tayar da Uwa daga samun 1/3 zuwa 1/6.

   YADDA KASON ZAI KASANCE 

 Uba Uwa 'Yan'uwa 
   5 1 👇🏼
 ----- ------ 👇🏼
    6 6 👇🏼
    5 + 1 =6
 -----------------
           6

  KASON UBA 


  5 #120,000
 ------ * ------------= #100,000
   6 1


          KASON UWA 

  1 #120,000
 ---- * ---------------= #20,000
   6 .


GURIN DA UWA KE FIN UBA SAMUN KASO MAI YAWA

Kamar yadda aka sani cewa dukkan magada sukan tashi daga wani matsayi zuwa wani matsayi bisa wasu dalilai, to, Uba ma kan tashi daga wani matsayi zuwa wani. 

Wani lokaci yana samun kaso daidai da Uwa, wani lokaci kuma yana finta, wani lokaci kuma ita Uwa tana finsa. Ya danganta ne kawai da irin magadan da aka bari. 

               MISALI 

Mata ce ta rasu ta bar Uwa da Uba da kuma dukiya #5,000,000.

Anan sai mu koma cikin Qur'ani muji abinda Allah ya fada game da wannan mas'alar. Allah (T) na cewa, 

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

"......فَإِن لَّمۡ يَكُن لَّهُۥ وَلَدٞ وَوَرِثَهُۥٓ أَبَوَاهُ فَلِأُمِّهِ ٱلثُّلُثُۚ ."

" IDAN KUMA BA SHI DA 'DA, IYAYENSA NE SUKA GAJE SHI, TO, UWARSA TANA DA 'DAYA BISA UKU 1/3 ."

Saboda haka kason Uwa anan shine 1/3, shi kuma Uba sai ya debi abinda ya saura komai yawansa kuma komai qanqantarsa. 

To, amma kuma ance matar tana da Miji, saboda haka sai mu qara komawa cikin Qur'ani muji abinda yace game da gadon miji ga matarsa. 

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

۞وَلَكُمۡ نِصۡفُ مَا تَرَكَ أَزۡوَٰجُكُمۡ إِن لَّمۡ يَكُن لَّهُنَّ وَلَدٞۚ فَإِن كَانَ لَهُنَّ وَلَدٞ فَلَكُمُ ٱلرُّبُعُ مِمَّا تَرَكۡنَۚ ...."


" KUMA KU (maza (KUNA DA RABIN ABINDA MATANKU SUKA BARI IN DAI BA SU DA 'DA, IDAN KUMA AKWAI 'DA GARE SU, TO, KUNA DA 'DAYA BISA HUDU 1/4 NA DAGA ABINDA SUKA BARI ...."

Saboda haka anan miji yana da rabin dukiyar matar tasa ce tunda bata haihu ba. 

GA YADDA RABON ZAI KASANCE 


  Uwa Miji Uba
     1 1 👇🏼
   ----- ------- 👇🏼
     3 2 👇🏼
     2 + 3=5 👇🏼
  --------------------
            6

Saboda haka dukiyar gida shida (6) za a kasata, sai a bawa kowa Uwa da Miji gwargwadon kasonsu tunda su an ambaci nasu, abinda ya rage kuma shine na Uba. 


      KASON UWA 

  
  2 #5,000,000
 --- * -------------=#1,666,666
  6 1


        KASON MIJI 

  3 #5,000,000
 --- * --------------=#2,500,000
  6 1


Idan aka cire kason Uwa #1,666,666 da kason Miji #2,500,000, abinda zai saura daga kudin shine #833,334.

To, shi wannan ragowar abinda ya rage shine kason Uba. 

           KASON UBA 
                      👇🏼
                      👇🏼
                      👇🏼
                #833,334

Kunga anan Uwa ta ninka Uba wajen samun kaso. 


BARNAR DA AKE YI BISA RASHIN ILIMI 

Ko da shike manya ne daga magabata suka tafka wannan barnar, amma dai ya kamata na baya suyi aiki da ilimi da hankali wajen gane gaskiya da kuma yin aiki da ita. 

A baya mun ambata cewa matuqar akwai Uba ko Uwa ko da (son) ko 'ya wani daga cikin halittun duniya ba zai yi gado tare dasu ba sai dai in shi Miji ne ko Mata, amma har yanzu a Sunnah basu gano wannan barnar ba. 

Bari mu kawo wani misali don nuna muku wannan barnar a ilimance. 

- Mutum ne ya rasu ya bar 'ya da Uwa da 'yar'uwa shaqiqiya da Mata da kuma dukiya #240,000.

A shari'ar muslimci 'yar'uwa ba ta da gado anan tunda cikin magadan akwai 'Ya kuma akwai Uwa. Amma a Sunnah suka ce za a bata 1/6 daya bisa shida ta cike gurbin kason 'ya'ya mata 2/3, abin nufi wai a hada da kason 'ya sai kasonsu ya fito. 

 KUNGA YADDA ZA A TARA 

  1 1
 --- ---
  2 6
  3 + 1 =4 2
----------- --- = ---
      6 6 3

Nufinsu haka za ayi ya zama 'ya da 'ya'uwa sun sami cikakken kason 'ya'ya mata. 

Subhanal-Lah, wannan hukunci ya sabawa ilimi da hankali domin an gina shi ne bisa hauka da rashin ilimi. 

Bari mu kawo muku implications da ke cikin wannan hukunci nasu . Amma kafin nan mu kalli wannan riwaya dake qasa; 

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

فس، تفسير القمي أَبِي عَنِ ابْنِ أَبِي عُمَيْرٍ عَنِ ابْنِ أُذَيْنَةَ عَنْ بُكَيْرٍ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع قَالَ: إِذَا مَاتَ الرَّجُلُ وَ لَهُ أُخْتٌ تَأْخُذُ نِصْفَ الْمِيرَاثِ بِالْآيَةِ كَمَا تَأْخُذُ الِابْنَةُ لَوْ كَانَتْ وَ النِّصْفُ الْبَاقِي يُرَدُّ عَلَيْهَا بِالرَّحِمِ إِذَا لَمْ يَكُنْ لِلْمَيِّتِ وَارِثٌ أَقْرَبَ مِنْهَا فَإِنْ كَانَ مَوْضِعَ الْأُخْتِ أَخٌ أَخَذَ الْمِيرَاثَ كُلَّهُ بِالْآيَةِ لِقَوْلِ اللَّهِ- وَ هُوَ يَرِثُها إِنْ لَمْ يَكُنْ لَها وَلَدٌ فَإِنْ كانت [كَانَتَا] أُخْتَيْنِ أَخَذَتَا الثُّلُثَيْنِ بِالْآيَةِ وَ الثُّلُثَ الْبَاقِيَ بِالرَّحِمِ- وَ إِنْ كانُوا إِخْوَةً رِجالًا وَ نِساءً فَلِلذَّكَرِ مِثْلُ حَظِّ الْأُنْثَيَيْنِ‏ وَ ذَلِكَ كُلُّهُ إِذَا لَمْ يَكُنْ لِلْمَيِّتِ وَلَدٌ أَوْ أَبَوَانِ أَوْ زَوْجَةٌ[2].

تفسير عليّ بن إبراهيم ج 1 ص 160.


Daga Ibn Abiy Umair , daga Ibn Uzainata , daga Bukhair daga Abu Abdullahi (A. S) yace, 

" Idan mutum ya mutu yabar 'yar'uwa za ta dauki rabin gadon bisa aya kamar yadda 'ya za ta dauka in ta kasance, kuma rabin a mayar mata bisa zumunci idan mamacin ya kasance ba shi da (wasu) magada wadanda suka fita kusantaka. 

Idan kuma a bigiren 'yar'uwar namiji ne, to, zai ci gadon ne baki daya bisa aya (nassi) bisa fadin Allah (T); 

" SHI MA ZAI GAJE TA IDAN YA KASANCE BABU 'DA GARE TA. "

Idan kuma sun kasan 'yan'uwa mata biyu ne za su dau 2/3 bisa aya (nassi) da kuma sauran bisa zumunci. Idan kuma 'yan'uwan sun kasance maza da mata ne, to, namiji na da kaso biyu na mace. Hakan kuwa na faruwa ne idan ya kasance mamacin bai bar da (children) ko iyaye ko Mata ba. "

       A LURA DA KYAU 

(1)- Babu aya ko hadisi wanda ke nuna cewa 'yar'uwa shaqiqiya na samun 1/6 in taci gado.

(2)- Idan aka ce 'yar'uwa ta ci gado, to, ko dai ta sami 1/2 in ita kadai ce, ko kuma suyi tarayya da 'yan'uwanta mata cikin 2/3, ko kuma ta sami kaso daya (1) cikin uku in suna tare da dan'uwanta namiji. 

(3)- Idan kuwa ba cikin kason da muka kawo cikin misalai biyu na saman nan ba, to, ita ma zaluntarta aka yi. 

(4)- 1/6 kason 'yar'uwa (Li-Ummiya) ce in ta kadaita, ita kuwa shaqiqiya ce. To, wacce hujja ce za a kafa ta ilimi wacce za a ba ta 1/6 ?

      SHARI'AR GASKIYA

Magada na haqiqa cikin wannan misali da muka kawo shine; 

 'Ya Uwa Mata 'Yar'uwa 
  1 1 1 👇🏼
 --- --- ---- 👇🏼
  2 6 8 👇🏼
 12 + 4 + 3=19 👇🏼
---------------------------
              24

Kenan za a kasa dukiyar ne gida 24 , sai a bawa kowa gwargwadon kasonsa, kuma za a sami sauran kaso 5 a qasa.

             KASON 'YA 

  12 #240,000
 ---- * -------------= #120,000
   24 1


        KASON UWA 

 4 #240,000
--- * --------------= #40,000
 24 1


        KASON MATA 

 3 #240,000
---- * ------------- = #30,000
 24 1

       KASON 'YAR'UWA
                    👇🏼
                    👇🏼
                    👇🏼
          Ba ta da komai 


Anan idan muka tara kason kowa za mu sami, 

'Ya. #120,000
Uwa. # 40,000
Mata. # 30,000
            + -----------------
                #190,000
               ------------------

To, saura kaso 5 ne a qasa wanda yake daidai da #50,000 daga cikin #240,000 da mamaci ya bari. 

Shi wannan saura za a mayarwa 'ya ce, ta ci 1/2 bisa aya, sannan ta ci saura bisa kusancinta da mamaci (Ubanta), ta sami kaso (FARDAN wa RADDAN) kenan.

ALLAH YA QARA MANA ILIMI NA FAHINTAR GASKIYA. 🙏🏿🙏🏿🙏🏿🙏🏿🙏🏿


KO KUN SAN WA AKE KIRA KALALA ?

Amsar da ta fito daga bakin Abubakar Bn Quhafata ita ce, 

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 الإرشاد سُئِلَ أَبُو بَكْرٍ عَنِ الْكَلَالَةِ فَقَالَ
An tambayi Abubakar game da Kamala, sai yace; 

 أَقُولُ فِيهَا بِرَأْيِي فَإِنْ أَصَبْتُ فَمِنَ اللَّهِ وَ إِنْ أَخْطَأْتُ فَمِنْ نَفْسِي وَ مِنَ الشَّيْطَانِ

" ZANYI MAGANA A KANTA NE BISA RA'AYINA (fahintata), IDAN NAYI DAIDAI TO, DAGA ALLAH NE, IDAN KUMA NA KUSKURE TO, DAGA GARE NI NE KUMA DAGA SHAIDAN. "

 فَبَلَغَ ذَلِكَ أَمِيرَ الْمُؤْمِنِينَ ع فَقَالَ مَا أَغْنَاهُ عَنِ الرَّأْيِ فِي هَذَا الْمَكَانِ أَ مَا عَلِمَ أَنَّ الْكَلَالَةَ هُمُ الْإِخْوَةُ وَ الْأَخَوَاتُ مِنْ قِبَلِ الْأَبِ وَ الْأُمِّ وَ مِنْ قِبَلِ الْأَبِ عَلَى الِانْفِرَادِ وَ مِنْ قِبَلِ الْأُمِّ أَيْضاً عَلَى حِدَتِهَا قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَ‏


Sai labari ya jewa Amirul-muminina Ali (A. S), sai yace, 

" Ra'ayi ba zai taba wadatar da shi kan wannan guri ba, bai san cewa Kamala sune 'yan'uwa maza da 'yan'uwa mata ta bangaren Uwa da Uba ba, da kuma bangaren Uba bisa kadaici, da kuma bangaren Uwa bisa kadaituwarta. Allah mai girma da daukaka yace, 

" يَسْتَفْتُونَكَ قُلِ اللَّهُ يُفْتِيكُمْ فِي الْكَلالَةِ إِنِ امْرُؤٌ هَلَكَ لَيْسَ لَهُ وَلَدٌ وَ لَهُ أُخْتٌ فَلَها نِصْفُ ما تَرَكَ‏ ."

" SUNA YI MAKA FATAWA, KACE " LALLE ALLAH NA YI MUKU FATAWA CIKIN KALALA, IDAN MUTUM YA HALAKA BA SHI DA 'DA KUMA YANA DA 'YAR'UWA, TO, TANA DA RABIN ABINDA YA BARI. "

Kuma yace madaukaki yana mai cewa ;

" IDAN MUTUM YA KASANCE AN GAJE SHI (a matsayin) KALALA, KO KUMA MACE, KUMA YANA DA 'DAN'UWA KO 'YAR'UWA (li-Ummai) , TO, KIWANNE 'DAYA DAGA CIKINSU YANA DA 'DAYA BISA SHIDA (1/6), IDAN KUMA SUN FI HAKA TO, SAI SUYI TARAYYA (SHARING) CIKIN 'DAYA BISA UKU (1/3) ."

 وَ قَالَ عَزَّ قَائِلًا وَ إِنْ كانَ رَجُلٌ يُورَثُ كَلالَةً أَوِ امْرَأَةٌ وَ لَهُ أَخٌ أَوْ أُخْتٌ فَلِكُلِّ واحِدٍ مِنْهُمَا السُّدُسُ فَإِنْ كانُوا أَكْثَرَ مِنْ ذلِكَ فَهُمْ شُرَكاءُ فِي الثُّلُثِ‏[13

إرشاد المفيد ص 107 طبع النجف.


Daga Sa'eed, daga Ibn Yazeed, daga Ibn Abiy, daga sashen Sahabbansa, daga Abu Abdullah (A. S) yace; 

" KALALA SHINE WANDA BA SHI DA UBA KO 'DA (ba shi da wani daga cikin mahaifa ko 'ya'ya) ."

مع، معاني الأخبار أَبِي عَنْ سَعْدٍ عَنِ ابْنِ يَزِيدَ عَنِ ابْنِ أَبِي عُمَيْرٍ عَنْ بَعْضِ أَصْحَابِهِ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: الْكَلَالَةُ مَا لَمْ يَكُنْ وَالِدٌ وَ لَا وَلَدٌ[1].

معاني الأخبار ص 272.

Saboda haka matuqar mutum ya rasu ya bar wani daga cikin mahaifa ko wani daga cikin 'ya'ya, to, shi ba Kalala bane, kenan ba hukuncin Kalala ne a kansa ba. 

Duk muna kawo irin wadannan bayanai ne dalla-dallah don mu fitar da wadanda suka fada cikin halaka cikin sakamakon raba gado ba yadda Allah yace ba. 

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.

      (08137925034)

20th February, 2021/ 8th Rajab, 1442.

5 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Slm mlm Allah yasaka da alkairi tan bayata anan itace yarbaiwa tanada gado

    ReplyDelete
  2. Dan uwan mijina ubansu daya yarasu yabar yaya mata 2 da mata 3 wayanda suke ciki daya. Sunraba gadon basubawa mijina ba, kuma shikadaine namiji su dika matane. Shin malam shi da kanwarsa basu da gado tunda uba daya sukafito?
    Kuma dam mata kadai ka iya cinye gado?

    ReplyDelete
  3. Allah ya bada lada tambayata itace idan mutum ya rasu yabar ya'ya' 3 maza da uba sai matarsh ya kason kowa zai kasance nagode

    ReplyDelete
Previous Post Next Post