Mutane huɗu (4) ne suka tserewa kowa cikin al'ummun da suka gabata !!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


WANDA YA TSEREWA KOWA CIKIN AL'UMMAR MANZON ALLAH SHINE IMAM ALI (A. S)


Cikin kowacce al'umma data gabata ba a rasa mutanen farko masu rigare cikin ayyukan aikhairi ko na sharri, kuma sune suke zama abin misali ga na baya .


Ambaton sunansu kan iya zuwa cikin Qur'ani ko cikin hadisai don mu sansu kuma mu dau darasi daga gare su. Idan masu tsere cikin aikin alkhairi ne muyi koyi da su, idan kuwa masu aikin sharri ne mu nisance su.


Abinda muke son kawowa anan shine wadanda suka tserewa kowa cikin muslimci da kuma ayyukan muslimci don mu bibiyi tarihinsu mu dau darusa daga rayuwarsu.


Ya zo cikin MAJMA'UL-BAYAAN daga Imam Baqeer (A. S) kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


وَ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع قَالَ: السَّابِقُونَ

 أَرْبَعَةٌ ابْنُ آدَمَ الْمَقْتُولُ وَ السَّابِقُ فِي أُمَّةِ مُوسَى وَ هُوَ مُؤْمِنُ آلِ فِرْعَوْنَ وَ السَّابِقُ فِي أُمَّةِ عِيسَى وَ هُوَ حَبِيبٌ النَّجَّارُ وَ السَّابِقُ فِي أُمَّةِ مُحَمَّدٍ ص وَ هُوَ عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبٍ ع‏[18].


. ثُلَّةٌ مِنَ الْأَوَّلِينَ‏ أي هم ثلة أي جماعة كثيرة العدد من الأمم الماضية 


(1) مجمع البيان ج 9 ص 215.


Daga Abu Ja'afar (A. S) yace; 


" MASU RIGAYE/TSERE (cikin alkhairi) SU HUDU (4) NE:-


(1)- 'DAN ANNABI ADAM WANDA AKA KASHE (Habila), 


(2)- WANDA YA RIGAYA CIKIN AL'UMMAR MUSA (A. S) SHINE MUMININ IYALAN FIR'AUNA, 


(3)- WANDA YA TSEREWA KOWA CIKIN AL'UMMAR ISAH (A. S) SHINE HABIBUN-NAJJAR, 


(4)- WANDA YA TSEREWA KOWA CIKIN AL'UMMAR MUHAMMAD (S. A. W. W) SHINE ALIYU BN ABIY 'DALIB (A. S) ."


Idan muka dauki misali dana kusa damu wato Imam Ali (A. S) za muga shine wanda ya tserewa kowa cikin al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W), domin ;


- Ya riga kowa gaskata Manzon Allah (S. A. W. W), 


- Ya fi kowa biyayya gare shi (S. A. W. W), 


- Ya fi kowa ilimi, 


- Ya fi kowa jaruntaka, 


- Ya fi kowa tausayi, 


- Ya fi kowa tawakkali, 


- Ya fi kowa tunani da hangen nesa, 


- Ya fi kowa fahintar maganar Manzon Allah (S. A. W. W) da kuma kiyaye ta, 


- Ya fi kowa iya hukunci cikin kowacce mas'ala,


- Ya fi kowa kyauta a halin buqata, 


- Ya fi kowa yaqini kan komai nasa cikin al'amarin muslimci, 


- Ya fi kowa sadaukar da rayuwarsa domin Allah da kare rayuwar Manzon Allah (S. A. W. W). 


           D. S


Idan kuwa hakane dole ma kowa yace Imam Ali (A. S) ya tserewa kowa cikin al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W), saboda haka shi yafi kowa abin koyi gare mu bayan Manzon Allah (S. A. W. W). 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


         (08137925034)


6th February, 2021/ 24th Jimada-Saaniy, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post