Rubutawa
- Bin Yaqoub Katsina.
8,Feb2021.
Tabbas munji dadi da aka ce gwamnatin Kano ta shirya Mukabala tsakanin Shaikh Abduljabbar da sauran Malaman da suke kalubalantarsa. Hakan na da kyau, sai dai bana jin zai haifar da da mai ido.
Eh!!, ma'ana ta yiwu akwai wani makircin da suka shirya a kasa wanda suke so suyi amfani da damar su cimmasa. Ba abin mamaki bane hakan domin gwamnati indai ba ta Allah bace, kuma ba tana hukunci ne da littafin Allah ba? (بغير ماأنزل الله) to lallai babu ranar da zata dai-daita da malamai na kwarai masu kira zuwa ga sahihin addinin Musulunci irin wanda Shaikh Abduljabbar yake yi.
Munga tarihohi da kissoshi kala-kala wanda hakan ta faru, amma sai gwamnati ta sa zalinci, ko ayi yarjejeniya karshe ta warware saboda tana ganin ita ce kan kowwa su taka wanda suke so ba abinda za a yi saboda mai mulki shi ne mai karfi (الملك لمن قهر).
Babban misalina a nan shi ne Shaikh Zakzaky (H), gaban idon kowwa ne gwamnatin nan ta 'yan maja suka bada damar a fita da shi india tare da mai dakinsa dan duba lafiyarsu. Amma karshe ya abin ya kaya ashe gwamnatin Najeriya ta gewaye ta kulla wani babban sharrin da karshe su Sayyid (H) sai dai dawowa suka yi kuma aikin da ba a yi ba kenan har yau.
In kaga gwamnati irinta Najeriya ta aikata abu to sai ta tabbatar ba ta zata ba iyayen gidanta sa'udiyawa da amerikawa kunya ba a cikinsa. Sannan su miyagun Malaman da ke zuga gwamnatin ban san wane hujjoji ne zasu iya kawowa ba da zasu shafe na Sarkin gida domin shi ba a litattafan shi'a ya kawo ba a'a a littafan Sunnah ne. In kuwa suna sane suka aikata hakan to lallai sunyi wauta kuma kashinsu ya bushe. Sannan abu daya cikin biyunnan zai faru na (1) imma su Malaman gwamnati su kwama da Sarkin gida (mukabala) Su ji kunya, shi kuma yayi nasara su kara fito da shi ya kara tunbatsa inda ba a sanshi ba kuma a gane irin duhun da dattin da yake son wankewa a addinin Musulunci.
Na (2) ko kuma gwamnati ta shigo da makirci, suyi zalinci, karshe su kuma al’umma su kara fahimtar Sarikin gida da koyarwarsa ya kara kwasar mabiya. Sai dai duk juyi Shi Shaikh Abduljabar Shi ne mai nasara tabbas. Amma 1 cikin 2 nan sai ya faru.
Tags:
Taskar ilimi