Duk da cewa ni dan kwankwasiyya ne, kuma nayi bakin ciki sosai da Gwamna Ganduje ya yiwa Sarki Korar kare daga Kano. Toh amma yanzu dole in fadi gaskiya.
MANYA-MANYAN ABUBUWA GUDA UKU DA SUKA FARU TSAKANIN MALAM ABDULJABBAR DA TSHOHON SARKI.
Lokacin yana sarki, abu guda biyu sun faru kamar haka:
1. UBA BAI FI UBA BA.
A farkon shekarar da aka nada Sunusi Sarki, ranar wata Juma'a da za'a dauki azumin watan Ramadan, a lokacin giyar Sarauta tana kwasar sarki, a hudubarsa ta juma'a, Sarki qarara yace: duk mutanen da basa yin azumi da umarnin ganin watan Sarki, toh ta6atattu ne, kuma hanyar wuta suke bi.
Malam Abduljabbar ya mayarwa da Sarki Martani a ilimance, kuma ya nuna masa cewa: Malam Nasiru Kabara da yake sa6awa ganin watan azumi a wasu lokuta qalilan, ai da hujjah a bayyane yake sa6awa, bada jahilci ba, kuma duniya ta shaida da haka.
Mal. Abduljabbar ya nunawa duniya, idan Sarki a matsayinsa na babba kuma uban Kanawa, zai saki wannan magana haka, toh fa uba bai fi uba ba. Kuma sarki mai zai ce akan wanda aka kawo shi Nigeria, sanadiyyar zuwansa TAUHIDI ya lalace, mabiyansa suke cewa shi Allah ne, wani zubin ma suce yafi Allah.
ABUN LURA
Wanda sanin kowane, Mai martaba Tsohon Sarki, yana daga cikin al-majiran SHEHU, hasali ma kakansa wanda ya gaji sunansa, shine ya kawo SHEHU Najeriya.
Toh tin daga nan aka fara takun saqa tsakanin Malamin da Sarki, tin bai shekara daya a kan kujerar Saurauta ba.
2. DAMA CHAN SUNUSI NE JAGORAN MALAMAN MAJA TIN KAFIN GANDUJE YA KORE SHI.
Sarki shine shugaban Malaman majah tun kafin Gwamna Ganduje ya kore shi daga jahar Kano, domin kuwa shine wanda ya jagoranci Malaman Majah gaba daya, suka yiwa Abduljabbar sharri da qazafi a masallacin Shehu Tijjani (R.A) da yake kofar mata. A inda Mal. Abduljabbar yace: idan sarki yana gani dashi zasu zauna muqabalah, toh ya futo da kansa ya hutar da Malaman majah, amma ya daina la6ewa yana tarasu, yana kunno masa wuta da qarya da sharri.
Kuma Malamin yace insha Allahu Sunusi ba zai kai wasu adadin kwanaki akan kujerar Sarauta ba, kuma kwanakin basu cika ba, sai da Ganduje yasa aka tsige shi.
3. TSOHON SARKI YACE ABU DALIB DAN WUTA NE.
A watan Azumin daya gabata ne, Sarki ya dakko littafin SALAFIYYA, inda ya kafirta ABU DALIB, wanda shine ya raini Annabi S.A.W tun daga shekara 6 da haihuwa har zuwa shekaru 10 bayan Annabta.
Don haka malam Abduljabbar yayi fatata da Sarki har yace: don ana yiwa sarki kara, yake ganin kamar shi malami ne? kuma littafin da yake karantawa na WAHABIYYA, sarkin yana da buqatar ayi masa wassali kafin ya karanta, domin ko jan baqi bai iya ba.
Idan Sarki yaga zai qara biyo sahun Abokansa, wanda shine dama tin asali shugaban Majah gaba daya, toh wannan abu shi yafi komai dadi da farin ciki.
Tinda naga wani Sarkin waka Maroqi (wanda duk mai sana'ar roqo zai tashi a lahira babu naman fuska) yayi cin mutunci, yana kukan munafurci, nasan mai bashi tuwo yake karewa a fakaice, tinda shi yaronsa ne, kuma yasan sa6anin daya faru tsakanin Sarki da Mal. Abduljabbar. Kuma suna ganin addu'ar da yayi cema ta tsige sarkin, Allah ya amsa. Don haka yake kuka yana kare mai bashi TUWO.
ALLAH YASA MU DACE.