Me Yasa Gwamnati Take Son Kawo Ƙarshen Malaman Addini ? – Sheikh Adamu Tsoho Jos



Yanzu lokaci ne da zamu fito mu ce bamu yarda da Zaluncin azzalumi ba, yanzu gashi sun taba Sheikh Abduljabbar kafin shi, wannan gwamnati ta kama Almajiran Sheikh Dahiru Usman Bauchi. To mu sani wannan Gwamnati ba kyale mu za su yi ayi addini yadda ya kamata ba. Dole ne musulmai ya zama mun yi inkarin wannan zaluncin.  


Kada kuyi tunanin zalunci yana tabbata, in ba haka ba da har yanzu fir'auna yana nan, da su Yazidu ma suna nan wanda suka kashe zuriyar manzon Allah (Saww). Amma kasantuwar basa nan yana tabbatar da cewa Zaluncin azzalumai ba zai taba tabbata ba. Don haka fatan mu shine musulmai ya zama mun fito mun yi inkarin wannan abin da yake gudana na zalunci. 


Domin Manzon Allah (Saww) ya ce, Idan kuna ga azzalumi yana zalunci , to ku hana shi aikata wannan zalunci da hannun ku ko harshen ku da kuma Zuciya. Idan muka yi haka wannan zai sa addinin mu ya dawo yadda yake sannan mu kasance cikin izza. 


  -Idishia Jos


Daga cikin jawabin Sheikh Adamu Tsoho Jos wanda yayi jiya da dare 6-Feb-2021 a garin Unguwar Nungu Yankin Jos. 


#FreeZakzaky

@Media Forum Jos.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post