@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Shi wa'azi ko tunatarwa yana amfani ne kadai ga masu tsoron Allah da neman gaskiya don suyi aiki da ita. Shi yasa Allah (T) ke cewa ku tunatar don ita tunatarwa tana amfanar da muminai.
Anan za mu iya ganewa cewa ashe dai ba kowa ne ke karbar wa'azi ba, duk zuciyar data qeqashe ba ta karbar gaskiya balle yin aiki da ita. Wannan kuwa ba akan wani bangare ko mutum ya taqaita ba, a'a yana kan dukkan musulmi da wanda ma ba musulmi ba in har zuciyarsa a bushe take.
Idan kaga an nunawa mutum gaskiya kuma ya bita, to, ka kira wannan mutumin mai imani da tsoron Allah. Amma shi fajiri ko yaga gaskiya ba zai bita ba, domin kalmar azaba ta riga ta tabbata a kansa.
Irin wadannan mutane za su sami tuhuma daga bakin Mala'iku masu tsoron gidan wuta a yayin da suka je don shigarta, kuma za su bayar da amsa ne gwargwadon sanin halin da za su koma ko shiga yayin da suka hadu da Ubangijinsu ranar da iqirarinsu ba zai amfanar dasu ba sai dai tabbatar dasu cikin mummuniyar makoma.
Dangane dasu Allah (T) na cewa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
وَسِيقَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِلَىٰ جَهَنَّمَ زُمَرًاۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءُوهَا فُتِحَتۡ أَبۡوَٰبُهَا وَقَالَ لَهُمۡ خَزَنَتُهَآ أَلَمۡ يَأۡتِكُمۡ رُسُلٞ مِّنكُمۡ يَتۡلُونَ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِ رَبِّكُمۡ وَيُنذِرُونَكُمۡ لِقَآءَ يَوۡمِكُمۡ هَٰذَاۚ قَالُواْ بَلَىٰ وَلَٰكِنۡ حَقَّتۡ كَلِمَةُ ٱلۡعَذَابِ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ ١٧
" ZA A KORA WADANDA SUKA KAFIRTA ZUWA GA JAHANNAMA SUNA JAMA'A-JAMA'A, HAR SAI SUNJE MATA AKA BUDE MUSU QOFARTA SAI MASU TSARONTA (MALA'IKU) SUCE MUSU; " ASHE MANZO (dan saqo) BAI ZO MUKU DAGA CIKINKU YANA KARANTA MUKU AYOYIN UBANGIJINKU BA , KUMA YANA GARGADINKU GAME DA HADUWARKU DA WANNAN RANA ? SUKA CE, " HAKANE, SAI DAI KALMAR AZABA CE TA TABBATA AKAN KAFIRAI ."
(SURATUL-ZUMAR:71)
Tabbas hakane, shi yasa masu karin magana ke cewa, " WANDA YAYI NISA BA YA JIN KIRA ."
To, wannan dalili yasa duk kiran da ake yiwa Buhari ba ya amsawa, kuma ba zai amsa ba har abada, duk abinda kaga ya auku na adalci akan wadanda ake zalunta 'yan Shi'ah ba hakan ya faru bane bisa son Buhari ba, a'a, sai dai kawai ganin damar Allah wanda yake da iko akan dukkan wani mai iko.
Shi kam kalmar azaba ta riga ta tabbata a kansa, sai dai kawai jiran lokacin da mai hukunci na gaskiya (Allah) zai yi hukuncinsa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda daga.
(08137925034)
4th February, 2021/ 22nd Jimada-Saaniy, 1442.