@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
HUKUNTA KIRISTAR BA AKAN MUSULMI YAKE BA
Shari'ar muslimci ta fayyace mana yadda ake hukunta mutumin da ya aikata zina cikin muslimci , yaro yake ko babba? Me aure ne ko marar aure?
Sai dai duk da hukuncin da aka sharadanta bai hana wasu daga musulmi aikata zina a junansu ba. Wasu ma abin yayi girma ta yadda suke samin lalatattu irinsu cikin masu addinin kiristanci. To, shin, idan musulmi yayi zina da kirista wanne hukunci ne ya hau kansu ?
Shin, dukkansu ne za a hukunta ko kuma a'a ? Idan kuma dukkansu ne wa ke da alhakin yin wannan hukunci ?
AMSA DAGA IMAM ALI (A. S)
Yazo cikin (Kitabul-Gharaati) daga Harith, daga babansa yace; Ya zo cikin hadisi cewa Imam Ali (A. S) ya aika Muhammad Bn Abubakar zuwa Misra a matsayin shugaba, sai (Muhammad) ya aiko da zuwa ga Aliyu (A. S) yana tambayarsa game da mutum musulmi wanda yayi zina da Banasariya (Kirista).
Sai Imam Ali (A. S) ya aika masa cewa ya zartar da haddi a kansu akan musulmin da yayi zina da Banasariya. Kuma ya bar Banasariyar zuwa ga ('yan'uwanta) Nasara suyi hukunci a kanta da abinda suka so (na hukuncinsu) ."
كِتَابُ الْغَارَاتِ، عَنِ الْحَارِثِ عَنْ أَبِيهِ قَالَ فِي حَدِيثٍ بَعَثَ عَلِيٌّ ع مُحَمَّدَ بْنَ أَبِي بَكْرٍ أَمِيراً عَلَى مِصْرَ فَكَتَبَ إِلَى عَلِيٍّ ع يَسْأَلُهُ عَنْ رَجُلٍ مُسْلِمٍ فَجَرَ بِامْرَأَةٍ نَصْرَانِيَّةٍ فَكَتَبَ إِلَيْهِ عَلِيٌّ أَنْ أَقِمِ الْحَدَّ فِيهِمْ عَلَى الْمُسْلِمِ الَّذِي فَجَرَ بِالنَّصْرَانِيَّةِ وَ ادْفَعِ النَّصْرَانِيَّةَ إِلَى النَّصَارَى يَقْضُونَ فِيهَا مَا شَاءُوا[4].
(1) كتاب الغارات مخطوط، و ما بين العلامتين كان محله بياضا في الأصل ألحقناه من كتاب الوسائل ج 18 ص 415.
Wannan na nuna mana ne cewa a cikin qasar da ake shari'ar muslimci amma ba dukkan qasar ce musulmi ba, to, idan ya kasance wanda ba musulmi ba ya aikata wani laifi ana hukunta shi ne da irin shari'ar addinin da mutum ke ciki, domin su ma suna da doka wacce ke hukunta masu laifi.
Irin haka ta faru zamanin Annabi (S. A. W. W) yadda wani abu ya faru tsakanin musulmi da wanda ba musulmi har wanda ba musulmin ba ke cewa aje wajen Annabi (S. A. W. W) yayi musu hukunci, shi kuma musulmin ke cewa aje wajen Bayahude.
Wannan dalili yasa Allah ya daukar da ayar nan da ke cewa;
" SHIN, BA KAGA WANDA KE RIYAWA CEWA YAYI IMANI DA ALLAH DA MANZONSA AMMA YANA NUFIN KAIWA QARA ZUWA GA 'DAGUTU ALHALI AN UMARCE SU CEWA SU KAFIRCE MASA.....?
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
30th January, 2021/ 17th Jimada-Saaniy, 1442.