Da Sannu A Hankali Mutane Ne Gane Maƙiya Ahlul-bait (As)
Wani bidiyo da jarumar Hausa Film mai suna A'isha Izzar So ta wallafa a shafin ta jiya take taya daukacin Al'ummar musulmi murnar ranar haihuwa Aliyu Ibn Abu Talib (As) ya jawo mata zagi da bayyana ta a matsayin ƴar Shi'a a Wajen wahabiyawa (Izala).
Inda maƙiya Ali (As) suka dinga kushe, tsinuwa da bayyana cewa zasu daina Following dinta a shafin ta. Kaman sun manta cewa Manzon Allah (s) yace "Ya Ali! Babu mai sonka sai mumini, babu mai ƙinka sai munafiki".
Annabi (s) yake cewa "Ali yana tare da gaskiya, gaskiya tana tare da Ali". Amma basuyi la'akari da hakan ba su fara kirar ta da ƴar Shi'a. Wannan yana nuna maka lallai ƴan Shi'a suna tare da gaskiya tunda suna tare da Ali (As), sun dauka duk duniya babu wani wanda ya kai Ali (As) bayan Annabi (s).
Duk wani wanda ya ƴaƙi Ali a lokacin rayuwar Manzon Allah ko kuma bayan wafatinsa to lallai ƴan Shi'a basa tare dashi ko shi waye. Akwai masu ruɗar mutane da cewa su suna tare da kowane bangare (Wanda su yaƙi Ali (As) da kuma shi Ali din) duk suna tare dasu, kuma kowanne ɓangaren yana da gaskiya (Ali da wanda su yaƙe shi), kuma wallahi karya ne ba yanda za ayi ace an samu saɓani ace kuma kowanne bangare yana da gaskiya dole sai an samu wanda baya kan dai-dai. Ko dai kana tare da Ali ko kuma kana tare da wanda su yaƙe shi Faƙat.
- Ibrahim Almustapha Saminaka
- 27/February/2021