2021-02-07
A Yau Lahadi Jagoran Juyin Musulunci Zai Gana Da Wasu Kwamandojin Sojan Sama Na Iran
A Yau Lahadi Jagoran Juyin Musulunci Zai Gana Da Wasu Kwamandojin Sojan Sama Na Iran.
A ci gaba da bukukuwan zagayowar ranakun cin nasarar Juyin Musulunci A Iran, Ayatullah Sayyid Imam Ali Khamnei zai gana da tsirarun kwamandojin sojan sama saboda yanayin cutar corona da ake ciki.
A kowace rana irin wannan dai kwamandojin sojan saman Iran suna jaddada mubaya’a ga jagoran juyin musulunci na Iran, a matsayin tunawa da abinda ya faru a ranakun cin nasarar juyin musulunci.
A ranar 19 ga watan Febrairu na 1979 ne dai manyan kwamandojin sojan sama na Iran su ka yi wa Imam Khumain mubaya’a.
Source: HAUSA TV