Ma'asuma Nigeria news update,
Muƙaddara cewa kudin da suke rabawa satoshi sukayi,
to ina hukuncin mutumin da yake cin kuɗin sata kuma bisa sanin cewa kuɗin sata ne???
Idan ko muka ƙaddara cewa kuɗin su ne na halal ɗinsu muka karɓa da zummar zamu zaɓesu to ina hukuncin mayaudari me Saɓa alkawari?
Idan yazama sun siyi ƙuri'ar mune sun biyamu to anya munada haƙƙi akansu kuwa?
Domin ba zaɓar su mukayi ba, siyanmu sukayi suka biya.
Kana ganin Wanda ake siya da kudi zai iya zaɓar cancanta?
Naji labarin wasu mutanen ma ganye suke ɗorawa akansu alamar cewa su kayan siyarwa ne!!
Wasu kuma suna riƙe da kwali an rubuta "for sale"
Ashe ba mu muke daga dutse domin ya faɗo ya danne mu ba?
Kanawan Dabo Da mutanan baucin yakubu da sakkwatawan shehu ga shekaru hudu agabanmu,
Shahid Ishaq Muh'd Suleman