Cikakken mahaukaci shine wanda ya fifita duniyarsa a kan lahirarsa !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


'DAUKAR ABU DAGA KAN JUJI BAI NUNA CEWA SHI YAFI KOWA HAUKA BA 


Yana daga cikin manyan alamomi na gane mutum ya sami tabin hankali a gan shi yana tafiya yana dariya ko kuma aga yana daukar ledodi daga kan juji, ko kuma rashin yin wanki da tafiya cikin gari babu takalmi a qafarsa.


To, shi wannan mutum za a iya kiransa wanda ya fada cikin jarrabawa, kuma zai iya samin rahmar Allah ranar sakamako , domin shi Allah ya dauke alqalami daga kansa har sai ya dawo daidai kamar wadanda hukunci ya hau kansu. 


Ya zo cikin riwaya kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


- وَ رُوِيَ‏ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ ص مَرَّ بِمَجْنُونٍ فَقَالَ مَا لَهُ فَقِيلَ إِنَّهُ مَجْنُونٌ فَقَالَ بَلْ هُوَ مُصَابٌ إِنَّمَا الْمَجْنُونُ مَنْ آثَرَ الدُّنْيَا عَلَى الْآخِرَةِ[57].


(1) أي اختار الدنيا و فضله على الآخرة.


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏1، ص: 132


An riwaito cewa Manzon Allah (S. A. W. W) ya wuce wani mai tabuwar kai sai yace, " MENENE GARE SHI ? " Sai aka ce ai mahaukaci ne. 


Sai (S. A. W. W) yace, " A'A, WANDA DAI YA HADU DA MUSIBA (jarrabawa), ABIN SANI MAHAUKACI SHINE WANDA YA FIFITA DUNIYA AKAN LAHIRA ."


Kunga kuwa ai wanda ya fifita duniya akan lahira shine cikakken mahaukaci, domin duniya tana qarewa ita lahira kuwa wanzajjiya ce, kuma duk wanda ya fifita gidan duniya akan na lahira ba shi da rabon gidan lahira.


Wannan na nuna mana ne kamar misalin wanda ya rungumi abinda yasan zai cutar da shi kuma marar amfani gare shi maimakon ya rungumi abinda zai amfanar da shi.


Yanzu kuwa za mu iya cewa ashe dai mafi yawan mutane mahaukata ne, domin 75% daga cikinsu sun fi fifita duniya akan lahira. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


        (08137925034)


8th February, 2021/ 27th Jimada-Saaniy, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post