Hotuna: Bangaren kiwon lafiyan harkar Musulunci (Isma Medical Initiatives) na yankin Kano sun yiwa yara Kaciya



Da safiyar yau Lahadi 07/02/2021 yan ISMA masu kula da harkar lafiya na da'irar Kano karkashin kulawar wakilin yan'uwa Musulmi almajiran Sayyid Zakzaky (h) na da'irar Kano da kewaye Sheikh Dr. Sunusi Abdulkadir suka gabatar da kaciya ga yara kanana, kamar yanda suka saba duk shekara.


Kaciyar wacce Dr. Muhammad Kabiru Kabara ya jagoranta an gabatar da ita ne a unguwar Kurna yan ganda cikin Makarantar Ansarul Mahdi Kano.


Wakilin Yan'uwa Musulmi na Kano Sheikh Dr. Sunusi Abdulkadir na daga cikin wayanda suka sheda yanda aikin kaciyar ya gudana, kuma anyi aikin lafiya, an kuma gama lafiya kamar yanda kuke gani cikin hotuna👇

Daga Baban Sayyid


       07/02/2021

Hotuna Lamiru










Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post