@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
WANDA YAYI FARIN CIKI DA ABINDA YA SAMI 'YAN SHI'AH ZAIYI FARIN CIKIN ABINDA YA SAMI ANNABAWA (A. S)
Cikin abubuwan da ke samun bawa mai kyau ko mummuna kan iya zama qaddara gare shi, amma wani lokaci shi yake jawowa kansa. Shi yasa ma wani guri Allah ke cewa duk abinda kaga ya sami mutum na musiba sakamakon aikinsa ne.
Wadannan abubuwa ne biyu masu bambancin ma'ana, domin kowanne na da muhalinsa. Wasu daga cikin Annabawa (A. S) kashe su akayi ta hanyar yankan Rago (🐑 ) , wanda hakan na daga cikin qaddara ba bisa jawowa kansu ba.
Duk wani abu da ke samun mutum a hanyar Allah sunansa qaddara, wani lokaci ma ba a hanyar addini bane amma kan iya zama qaddara. Za mu iya bada misali da hatsarin mota ko gobawa a wani lokaci.
Sai dai kuma wannan wani ilimi ne wanda ba kowa ke iya gane ba sai masu ilimi na haqiqa da masu tsarkin zuciya. Za mu iya bada misali game da abinda ya faru a waqi'ar Karbala cikin furucin Yazeed (L. A) da Imam Zainul-Abideen (A. S).
Ya zo cikin riwaya daga Imam Sadeeq (A. S) yake cewa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
كَمَا رُوِيَ عَنِ الصَّادِقِ ع أَنَّهُ لَمَّا دَخَلَ عَلِيُّ بْنُ الْحُسَيْنِ ع عَلَى يَزِيدَ نَظَرَ إِلَيْهِ ثُمَّ قَالَ:
Yayin da Aliyu Bn Husain (A. S) ya shiga wajen Yazeed (L. A), sai ya kalle shi sa'annan yace :
يَا عَلِيُ," ما أَصابَكُمْ مِنْ مُصِيبَةٍ فَبِما كَسَبَتْ أَيْدِيكُمْ ."
" Yaa Aliyu ! " ABINDA YA SAME KU NA DAGA MUSIBA (a Karbala) SAKAMAKON ABINDA HANNAYENKU SUKA AIKATA NE ."
فَقَالَ ع: كَلَّا مَا هَذِهِ فِينَا إِنَّمَا نَزَلَ فِينَا,
Sai (A. S) yace, " A'aha, wannan ba a kanmu take ba, abinda ya sauka a kanmu shine :
" ما أَصابَ مِنْ مُصِيبَةٍ فِي الْأَرْضِ وَ لا فِي أَنْفُسِكُمْ إِلَّا فِي كِتابٍ مِنْ قَبْلِ أَنْ نَبْرَأَها إِنَّ ذلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرٌ لِكَيْلا تَأْسَوْا عَلى ما فاتَكُمْ وَ لا تَفْرَحُوا بِما آتاكُمْ ."
" BABU WANI ABINDA KE FARUWA NA DAGA MUSIBA A CIKIN QASA KO AKAN KAWUNANKU FACE YANA NAN (tun farko rubuce) CIKIN LITTAFI TUN GABANNIN MU AUKAR DA ITA, SHI KUWA WANNAN MAI SAUQI NE A WAJEN ALLAH. (Allah kan yi hakanne gare ku) DON KADA KUYI BAQIN CIKI GAME DA ABINDA YA KUBUCE MUKU (na haqqoqinku da 'yancinku), KUMA KADA KUYI FARIN CIKI DA ABINDA YAZO MUKU. "
فَنَحْنُ الَّذِينَ لَا نَأْسَى عَلَى مَا فَاتَنَا وَ لَا نَفْرَحُ بِمَا أُوتِينَا.
" To, mune wadannan da ba za muyi baqin ciki da abinda ya kubuce mana (na haqqoqinmu) ba, kuma ba za muyi farin ciki da abinda yazo mana ba. "
(3) الشورى: 30.
(4) الكافي ج 2 ص 269.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج70، ص: 316
Kaga anan Yazeed (L. A) bai san ma'anar wannan ayar da ya kawo ba, kuma irin wannan gurbatacce karatu ne mafi yawan wannan al'umma ke da shi, suna fassara aya ba a muhallinta ba .
Wannan gurbacewar karatu ne yasa za ka ji suna bada fatawa wacce hankali ma ba ya kamawa ballantana ilimi.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
2nd February 2021/ 19th Jimada-Saaniy, 1442.