An kama barawon da ya addabi kajin mutane a Abuja


 

Kotu a gundumar Bwari dake babban birnin tarayya Abuja ta yanke wa wani matashi mai suna Adam Abdulrahaman hukuncin zama a kurkuku na tsawon kwanaki 30.


Kotun ta yi haka ne bayan ta kama Abdulrahaman da laifin satan kaji guda biyu.


Abdulrahaman ya amsa laifin sa kuma ya roki kotu ta yi masa sassauci.


Alkalin kotun Hassan Aliyu ya bada belin Abdulrahaman akan Naira 5,000.


Aliyu ya ce hukuncin da ya yanke zai zama gargadi ga barayin kajin mutane a Abuja.


Lauyan da ya shigar da karar Tunde Arowolo ya ce Mohammed Salihu dake zama a Action Layout, Bwari, ne ya kai karar satar kaji da ake masa yana neman a taya shi kamo wanda ya ke dauke masa kaji.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post