@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
A duk lokacin da wani al'amari ya taso kuma yake yaduwa sa sauri cikin al'umma kamar wutar daji za ka ji shine babban abinda ake magana a kansa don ankarar da mutane game da sharrinsa ko Illar dake cikinsa.
A daidai lokacin da gwamnatin jihar Kano da zartar da wani hukunci mai zafi kan Sheikh Abdul-Jabbar sakamakon karatuttukan da yake yi sai al'amarin ya ratsa ko ina cikin kafafen sada zumunta da jaridu da kuma sauran kafafen radio da television.
Su kuwa malamai masu bambancin ra'ayi dana wannan Shehin malami suka cigaba da tallata abinda yake yi ko yayi a matsayin wata fitina wacce idan ta barke ba a san iya inda za ta tsaya ba.
BAN YANKE HUKUNCI KAN ABINDA SHEHIN MALAMIN KE YI BA
Tun faruwar wannan al'amari wasu ke tambayata kan cewa wai menene haqiqanin abinda wannan malami yayi ne har aka yanke masa wannan hukunci ? Sakamakon rashin jin abinda ya fada da kunnena ban iya bada wata amsa game da abinda na fahinta a kai ba.
Wani ya kirani a waya yake fada min cewa lalle ya saurari sashen abinda malamin ya fada amma wai munin abin yayi yawa domin ya taba shaksiyyar Manzon Allah (S. A. W. W). Kuma wai ance masa abinda bai jin bama shi yafi muni daga wanda ya saurara.
Ni kuma saboda rashin jin abinda ya fada da kunnena ya hana nayi wani furuci ga wani ko kuma nayi rubutu kan wannan al'amari.
YAU NA YANKE HUKUNCI
Duk da cewa ni ba malami bane kuma ba masani ko marubuci wanda za a iya tsayawa a karanta har ya zamana ya amfanar da wasu ba, amma sakamakon hankalin da Allah ya bamu kuma yace muyi amfani da shi wajen tantance gaskiya da qarya yasa na yanke hukunci har nayi wannan rubutu.
Na fito wajen aiki a yau larabawa 10-2-2021 na tarar ana turawa wani jawabin da Sheikh yayi wanda aka tattara su cikin (cassette ) guda don gamsar da masu sauraro munin abinda malamin yayi har ake ganin hukuncin da aka yanke a kansa yayi daidai.
Ba tare da nace komai ba sai wani dan Izala yake ce min in ce dai mu ('yan Shi'ah) ba ma tare da abinda wannan malami yayi? Sai nace masa ai ni ban ji abinda ya fada ba ballantana kace muna tare da shi ko ba ma tare. Sai yace min ai batanci yayi game da Manzon Allah (S. A. W. W) , domin shi da ya fara sauraron (cassette) din ma kasawa yayi, don ji yake kamar sama za ta hade da qasa !
Bayan an gama tura wannan (cassette) cikin wayar wani sai ya kunna mana don mu ji. A lokacin da muka fara jin muqaddimar da mai gabatarwar yayi sai hankalina ya tashi don ban san abinda zan ji daga bakin Sheik Abdul-Jabbar ba. Wannan dalili ya qara sa ni cikin nutsuwa don saurare da kunne basira.
Farkon abinda aka fara sawa cikin jawaban nasa naji ai ya kawo irin munin abubuwan da aka rubuta ne na cin zarafin Manzon Allah (S. A. W. W) wanda aka nasabta su da shi (A. A. W. W), shi kuma yake qoqarin ba shi kariya tare da nuna laifin masu wannan aiki.
Dana cigaba da saurare sai naga gaba daya babu wani furuci wanda za ace nasa ne dake nuna cin zarafin Annabi (S. A. W. W), sai dai ya riqa tsakuro irin abinda aka rubuta ne na cin zarafi, shi kuma yana nuna laifin masu kawo wannan magana na cin mutunci ga fiyayyen halitta (S. A. W. W), kuma suke nuna fifikon wasu a kansa (S. A. W. W).
Ni da wanda aka turawa kowa ya fahinci inda Shehin yasa gaba, har ma yake cewa gaskiya mutane ba sa fahintar magana, amma ai abinda malamin ke fada ya hakaito zance wasu ne ba wai zancensa bane.
Shi kuwa wannan dan Izala da muka bayyana masa manufar malamin har ma muna dawo da cassette din farko muka qara saurara sai yace ai gaskiya yanzu ya fahinci wannan magana, domin shi bai saurara ba tun da yaji abinda mai qaddamarwar ya fara.
Tun daga nan na raina hankalin masu jin magana daga bakin wani kan wani suyi saurin yanke hukunci kansa ba tare da sun ji daga bakinsa ba.
Shi yasa Allah (T) ya gargade mu cewa,
" IDAN FASIQI YAZO MUKU DA LABARI KUYI BINCIKE DON KADA KU AFKAWA MUTANE BISA JAHILCI SANNAN KU WAYI GARI KUMA MASU NADAMA KAN ABINDA KUKA AIKATA.
Abinda ake nufi da (FASIQI) anan shine duk mutumin da ba ma'asumi bane ya fadi magana kada ka riqa zartar da hukunci daga jin abinda ya fada.
ABINDA KUKA MANTA KO BA KU SANI BA
Salon da maqiya Allah ke bi don munana bayin Allah shine qirqirar qarya ko sharri su jinginawa bayin Allah don a nisantar da jama'a daga kiran da suke yi.
An kira Annabi (S. A. W. W) da cewa shi Boka ne, Mawaqi, Masihirci mai rarraba tsanin 'ya'ya da mahaifansu, amma wannan magana gaskiya ce ? Amsa ita ce a'a, amma hakan bai hana wasu gamsuwa da hujjar wadannan kafirai ba.
Kar ku manda da cewa, irin wannan salo akayi amfani da shi wajen munana 'yan Shi'ah wai suna zagin Sahabbai, kan haka aka riqa halasta jinanansu tare da lalata musu muhallansu da dukiyoyinsu.
Yanzu kuma sun gano cewa yin kamfen (campaign) da zagin Sahabbai don hana bayyanar da gaskiya ba zai yi tasiri ba, saboda haka gara suce ana zagin Annabi (S. A. W. W) don sun san soyayyarsa ta yi tasiri cikin zukatan al'umma, duk da cewa su masu wannan magana ba son Annabin ne cikin zukatansu ba.
Wanda ke yin musu ga wannan magana tawa dan Allah ya nemi cassette din ya saurara, in kuma yana da shi ya daure ya qara sauraro da kunnen basira insha Allahu zai fahinci cewa maganar da Shehin ya kawo ba tasa bace sai dai ya kawo abinda maqiya Annabi (S. A. W. W) ne suka kawo na cin zarafi, shi kuma yake kare Shi. Su dai wadannan mutane (malamai) suna qoqarin boye laifuffukan da Sahabban ne suka yi, shine suke juyar da hankalin mutane marar sa hankali da tunani.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
10th February, 2021/ 28th Jimada-Saaniy, 1442.