@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ZUNIFI YA FI SAURIN SHIGA JIKI FIYE DA YADDA WUQA KE SHIGA JIKIN MUTUM
Duk da cewa Allah yace mana in mun nisanci aikata manyan zunuban da ya hane mu aikata su zai kankare mana qananan laifuffukanmu, amma ba hakan nu nuna mana ne mu riqa aikata su ko kuma ganin qasqantarsu ba.
Imam Ali (A. S) na cewa, " ZUNUBI MAFI HADARI SHINE WANDA MAI AIKATA SHI YA 'DAUKE SHI QANQANI ."
Idan mutum ya kasance yana yawan aikata qananan zunubai ba tare da nisantarsu ba, to, da sannu wadannan zunubai za su iya taruwa su girma yadda mai aikata su ba zai iya daukarsu ba, domin Allah (T) ya nuna mana cewa babu wani abu wanda bawa zai aikata na zunubi ko khairi komai qanqantarsa face yana cikin littafi bayyananne. Kaga kuwa ai ko kudi ne da kadan yake taruwa har wataran aga ya zama mai yawa.
Ya zo cikin Usulul-Kafiy kamar haka;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
عَنِ ابْنِ فَضَّالٍ عَنِ ابْنِ بُكَيْرٍ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: إِنَّ الرَّجُلَ يُذْنِبُ الذَّنْبَ فَيُحْرَمُ صَلَاةَ اللَّيْلِ وَ إِنَّ الْعَمَلَ السَّيِّئَ أَسْرَعُ فِي صَاحِبِهِ مِنَ السِّكِّينِ فِي اللَّحْمِ[95].
(1) الكافي ج 2 ص 272.
Daga Ibn Gaddhaali, daga Ibn Bukairin, daga Abu Abdullah (A. S) yace:
" LALLE MUTUM YAKAN AIKATA ZUNUBI WANDA KAN IYA HANA SHI (yin) SALLAR DARE, KUMA LALLE SHI AIKIN ZUNUBI YA FI SAURIN (shiga) JIKIN MAI AIKATA SHI FIYE DA YADDA WUQA (ke saurin shiga) CIKIN NAMA ."
Daga cikin wannan hadisi za mu iya fahintar cewa ashe aikata zunubi na hana mai aikata shi yin sallar dare, kuma shi zunubi kan saurin tasirantuwa ga mai aikata shi.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
5th February, 2021/ 23th Jimada-Saaniy, 1442.